Page 40

336 21 0
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 40

By
*MARYAM S INDABAWA*

Hakuri da Juriyya Online ✍
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Wata Motoci kirar Rolls Royce, Motace mai tsananin sheƙi da azabar kyau motar sabuwace dal, sai she'ki da ɗaukar ido takeyi komai na motar farine 'kal sai glass d'inta daya kasance tint mai duhu. Wani kyakyawan matashine mai cikar haiba da kamala da kima, uwa uba kwarjininsa mai cika idon mutane, farine 'kal wanda da ka ganshi kasan tabbas bafulatani ne, kuma zaka gane ya haɗa jini da larabawa. Shigar kanannun kaya ne a jikin sa masu kyau da tsada. Bakin wando ne da orange kalar riga, sai bakin takalmi cover mai masifar tsada. Sai sheki yake haka nan hannun sa makale da bakin agogo mai kyau da tsada. Yana da doguwar fuska wacce take zagaye da saje mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, kana gashin girarsa ya kwanta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido.

Bayan sa jingine da kujera hannun sa daya akan sitiyarin motar dayan kuma counter ne a hannun sa yake ambaton Allah. Fararen idanun sa ya lumshe bayan ya iso bakin gate din gidan su tare da dannan horn din motar wanda daya daga cikin security yai sauri ya bude gate din.

A hankali ya bude idon sa ya sauke akan sa yace
"Welcome Doctor!"
Hannu ya daga masa yace
"Thanks!"

Sannan a hankali ya karasa tura hancin motar cikin katon compound din nasu wanda duk da dare ne wajen tamkar rana saboda hasken wajen ko allura ce ta fadi zaka gani a wajen. Idon sa ya juya ya kalli bangaren Ummi. Murmushi ya saki ganin bangaren Ummin da haske ba kamar kwanakin baya ba da bata nan. A hankali yai parking a wajen da ya saba parking sai da ya dauki minti wajen goma sannan ya bude kofar motar ya zuro kafafun sa kasa. A hankali ya fito ya zura wayoyin sa cikin aljihun wandon sa. A hankali yake taku cikin nutsuwa, tafiyar yake tamkar yana tausayawa ƙasar bakin sa dake zage da siraran lips yana motsi a hankali a hankali hannun sa na pressing counter din sa. A haka ya karasa bakin kofar Ummi,  knocking yayi, Abbah ya bashi izinin shiga. Ya shigo a hankali,  A hankali ya shigo cikin tafiyar sa a nutse, karasowa falon yayi a kasa ya zauna kan sa a kasa yace
"Barka da dare Abbah!"
"Yauwah Doctor Ya kake?"

"Alhamdulillah. Abbah kun dawo lafiya ya hanya da mai jiki?"
"Alhamdulillah!"

Ya dan kalli dakin yace
"Ina Ummi na?"
"Tana sama ita da Inna!"

Mikewa yayi ya nufi stair yana fadin
"Me Inna tazo yi da daren nan!"
"Tazo ganin marar lafiya."

"Tab tazo dai damun ta!"
Ya fada a hankali ya karasa hawa. Yana hawa ya fara jiyo muryar Inna na fadin
"Na shiga uku har yanzu aman yaki tsayawa!"

Dakin da yajiyo muryar ta ya karasa yai sallama a hankali ya bude dakin ya shiga. Inna ya gani tsaye a kofar bandakin tana ta magana. Karasawa yayi a hankali ya ra'ba ta gefen ta ya shiga ciki.

Ummi ya gani rike da Maryam. Amsar Maryam yayi a hannun Ummi ya cire mata hijab ya dafa bayan ta hade da tallabo  ta. Ido ta lumshe ta daura kan ta a kirjin sa tana sauke ajiyar zuciya.

Famfo ya kunna ya janyo ta ya dauraye mata baki sannan ta koma jikin sa ta kwanta tana ta numfarfashi.
"Sannu!"

Ummi ta fada. Hannun ta ya kamo suka fito kan gado ya ajiye ta yana kallon dakin.
"Menene wannan kuma?"
Ya fada idon sa aka plate din da Maryam ta gama shan faten
"Fate ne!"
Inna ta fada

"Menene fate? Zaki bata wannan abincin haba ai dole ya sata amai tsaki ne ma fa! Menene value nasa a jiki?"
Kallon sa Inna ta tsaya yi sama da kasa sai da ya gama tace
"Kai kasan menene value din? Kuma naga uwar ka shi taci da tana da cikin ka ma. Kullum shi take sawa nake mata dan shi take jin dadin sa abakin ta har kazo duniya shin me ya faru da ita zaka zo ka ishe ni da wani kaza da kaza!"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now