Page 26

299 18 0
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 26

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Yaa Muhammad ne yace
"Abbi aje asibiti dai a kara gwada ta."

Yaa Abdullah yace
"Akwai likitoci, a waje bari na kira wani."
Ya juya ya fita da sauri da daya daga cikin abokan Aliyu ne basu koma ba suka zo amsa jana'idar sa suka shigo Maryam ya dudduba sannan yace
"A kai ta asibiti dan tana cikin mayuwacin hali in ba a kula da ita ba zata iya karasawa."

Da sauri Yaa Muhammad ya dauke ta Ammi tabi bayan sa. A bakin bangaren Yaa Haidar su Aisha sukaga Yaa Muhammad ya fito da Maryam da sauri suka bi bayan sa Ammi ma ta fito mota daya suka shiga. Yaa Fadima na gaba Ammi da Aisha na baya rike da Maryam wacce take tamkar gawa.

Suna zuwa aka amshe ta aka wuce da ita emergency likitoci ne suka hadu dan ceto ranta wanda suka kwashe sama da awa takwas akan ta amman sam bata dawo haiyacin ta ba da taimakon oxygen dai sun samu tana numfashi amma daga nan ba abinda yake motsi a jikin ta.

Wanda asibiti zuwa wannan lokacin a cike yake dan wajen hudu na yamma lokacin har an sallaci Aliyu Haidar wanda ya samu hallartar mutane masu yawa aka kai shi gidan sa na gaskiya kowa sai addu'a yake masa dan Aliyu mutumin kirki ne bai taba fada da kowa ba kowa nasa ne dan haka kowa sai yabon sa yake.

Ammi, Yaya Fadima da Aisha sune suke asibitin tin safe basu koma gida ba. Yaya Zainab,  Yaya Ummulkursum, Yaya Rabi da Hauwa duk sun zo. Haka nan Innah da su Anty Asibi, Anty Hauwa da sauran suma kowa yazo yaga halin da Maryam take, kowa yazo da kuka yake tafiya. Innah ce ta kasa tafiya itama dan halin da taga Maryam ya tsorata ta gani take itama kamar mutuwa zatai.

Suna zaune sukaji sallamar Mamah, da sauri Ammi ta mike tana fadin
"Da kanki Hajiya ai wandan da suka zo ma sun wadatar!"
Zama Mamah tayi tana goge hawaye tace
" *Matar Haidar* ce fa,  dole na rike masa amanar ta ko da bashi da rai domin ba tin yau ba yake ban amanar ta dan da yana da rai da shine mutum na farko da zai kasance akan ta to bashi da rai dan haka ni zan kasance mata tamkar Haidar insha Allahu. Allah ya bata lafiya domin Ita kadai zan kalla na tina haidar ita mutane da yawa zasu kalla suyiwa Haidar addu'a dan za ace ga *Matar Haidar* wanda ranar daurin auren su ya rasu....."

Kasa karasawa tayi, saboda kuka. Innah ma kukan take tace
"Tabbas ko ba aure shakuwar Ali da Takwara abin duba ne dole ta shiga wani hali, Allah ya tashi kafadun ta shi kuma munyi rashi yaro mai hankali da nustuwa ga zumunci takanas kafa ya kafa yake zuwa ya gaishe ni,  Allah ya jikan sa yasa can tafi nan Allah gafarta masa."

"Amin Amin! Amin Ya hayyu ya qayyum!"
Haka duk yan dakin suka amsa. Bayan mintina Ammi ta kalli Mamah tace
"Hajiya amman da kin koma gida saboda yan zuwa gaisuwa ko?"

"Hajiya Aliyu ya riga ya tafi addu'a ce kawai abinda zamuyi masa,  Maryam ita ke bukatar mu yanzu dan Allah ku barni anjima na tafi ganin Maryam nasa naji tamkar Aliyu nake gani".
"Allahu Akbar! Lallai ku mutanen kwarai ne, Allah ya jikan Aliyu."
Innah ta fada. Suka amsa da Amin.

Sai dare da Abbi da Abbah suka zo sannan Mamah ta tafi aka tafi da Innah da Yaya Fadima dan Aisha sam taki tafiya itama sai kuka take iyayen ta dazu sun zo sunje gaisuwa suka biyo asibiti. sai bayan fitar su Abbi ya kalli Ammi yace
"Alkasim ma fa yana gida ana masa karin ruwa tinda muka kai Aliyu yake kuka ya suma yafi sau biyar ga zazzabi dake damun sa ga rashin bacci da abinci."

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah mungode maka Allah mungode maka Allah ka yafe mana ka jikan Aliyu ka tashi kafadun yaran nan!"
"Amin!"
Abbi da Aisha suka amsa. Daga haka ba abinda suke ce. Can sai ga Yaya Ummulkursum da Yaa Muhammad ya kawo ta dan ta kwana da Maryam amman Ammi tace suje kawai zata kwana. Aisha taki tafiya Ammi tace a barta.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now