Page 63

288 12 1
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 63

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Ta mike ta kwashe kwanukan takai kitchen ta dawo ta wuce sama, har tayi shirin bacci Muhammad ya kira ta, dauka tayi tace
"Baka kwanta ba?"
"Yanzu zan kwanta nace bari na kira My happiness."

Murmushi ta dan saki, kira taji yana shigowa ta dauke taga Aliyu ne ido ta dan zaro tace
"Please bari na amsa wani call."

Ta kashe ta dauki ta Aliyu,
"Dawa kike waya?"
Ya tambaya,
"Uhmm uhmm da Jawahir ne."

"Me kuke fadi?"
"Yaya akan makarana wani aiki?"

"Wane aikin?"
Idon ta ne yai tsilli tsilli yace
"Uhmm ina jin ki."

Wani case ta lalubo ta fada masa yace
"Ganewa ne baki ba ko me?"
"Eh."

Bayani ya hau yi mata, tana ji sosai take ganewa, Muhammad ya kira yafi sau uku sai yaji call waiting sun dauki kusan awa daya sannan yace
"Ina fatan kin gane?"
Kai ta gyada yace
"To kije ki kwanta nasan dare yayi muku sai da safe."

"To Yaya nagode."
Ta kashe wayar, tana kashewa Muhammad na kiranta, dauka tayi yace
"Dawa kike waya?"

Shiru tayi tana mamakin wai meyasa suke mata haka ne kowa bai son tai waya da wani, gwara shi Muhammad ta sani kishi ne Aliyu kuma tausayi ne da kulawar da yake mata, dan tsaki ta saki tace
"Suna sani ina yin karya."

"Hello!"
Ya fada tace
"Uhmm ina jin ka."

"Nace dawa kike waya?"
"Yaya ne yana koya min wani karatu ne."

"Uhmm Yaya a wannan lokacin yake koya miki karatu."
"Eh!"

Kawai ta fada a dan fusace wannan yasa yace
"To shikenan sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."
Ta kashe wayar kawai. Kwanciyya tayi tana mai rufe idon ta kawai.

A cikin satin Abba ya kira Muhammad akan ya turo magabatan sa akan zancen auren su da Maryam, Muhammad ma da yake a shirye yake yana fadawa Dadyn sa, Dadyn sa yasa ya tambaya yaushe zasu zo suka saka rana, lokaci nayi suka shirya da Dadyn sa da yan uwansa biyu da aminin sa sukaje, sosai akai musu tarba sukace dan su yaga yarinya yana so in an basu dama zasu kawo kudin saka rana da komai na biki dan su haka suke yi, su Abbi suka yadda akan haka.

Bayan wata daya suka dawo da kudin saka rana da sadaki har da lefe suka saka wata uku masu zuwa wanda a lokacin su Maryam sun samu hutu suna komawa shekara daya zasuyi karatu sun gama gaba daya.

Bayan  tafiyar su Ummi da Mami suka shiga ganin uban kayan da aka kawo kamar wanda za a bude shago dasu, kaya ne masu kyau da tsada ko akwati nan har da ruwan gold aka hada aka yi su, Lokacin da Mama ta gani ba karamin tashin hankali ta shiga ba, dan Mama irin matan nan ne masu bakin ciki ba sa son abu ya samu wani sai su kadai, Inna kuwa sai saka albarka take har da kuka na murna Maryam zata samu gidan hutu mai sonta, gwala gwale kuwa an saka mata har guda uku, banda zobe da awarwaro duk a ciki, bangaren Ummi aka mai da kayan su Anty Asiya, Najwa duk sun zo sun ga kaya.

Maryam ce zaune a dakin ta tana neman layin Jawahir tana fara ringing ta dauka ta kai kunnen ta Jawahir tace
"Ke albishirin ki?"

"Goro ya akai?"
"An kai kayan auren Yaa Khalifa fa, nan da wata uku muna da biki."

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now