💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 61By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Maryam ta hade rai, Hauwa tai dariya, Maryam tace
"Kai ke wallahi baki san Yaya bane ko ke bai miki haka ba?"
Ta fada tana mai da tambayar kan Najwa."Ya min amman ba kamar naki ba."
"To ai ni dan muna tare ne.""Uhmm cewa fa yayi kar ta tsaya kula samari ta riki karatu dan Allah kalli wannan budurwa mai kyau wai ita za a cewa kar ta kula samari."
Dariya suka sheke da ita Basma tace
"Uhmm kalli fa yadda Affan ya rikice daga ganin ta."Dariya Hauwa tayi tace
"Tabb, lallai Yaya Aliyu"
Maryam dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba, Hauwa tace
"Toh wallahi son ki yake...."Maryam ta zaro ido ta koma baya da sauri tace
"Don Allah ki daina cewa haka plsease, wallahi Yaya na ne fa, ke ai Najwa kinsan Yaya fa"Najwa tayi wani murmushi tace
"Tinda ba ciki daya kuka fito ba ai an gama Maryam, ki daina tinda manyan yan soyayya suka gane to da wata a kasa fa. Ni daman na fara zargin sa dan yadda da kika zo hutun nan ya adabe mu da zarya har sai da kika koma sai muyi sati nawa bamu gansa ba amman kina nan kullum yana nan kuma bai son ya barki ki je ko ina ke kulawar Yayan tai yawa. Yadda Yaya yake miki ma ai bai mana ba, ke dai ce ban san lokacin da zaki yi wayo har ki fahimci inda ya dosa, wai Yaya ne. A'a ba Yaya ba..."lokaci daya hankalin Maryam ya tashi wai Yaya son ta yake, ji tayi ta kasa nutsuwa sai kara tabbatar wa suke Hauwa na kara zuga Najwa, Maryam tace
"Wallahi ku daina cewa haka ba kyau, ni ai Yaya yafi karfi na wallahi ba ruwan sa."Dariya kawai Hauwa take don Maryam tayi mugun bata dariya, haushi suka bata ta mike ta bar dakin, dakin Sitti taje ta zauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, Sitti ce ta shigo ta zauna a gefen ta tace
"A'ah Yaushe kika dawo.""Yanzu."
Ta fada tana kwanciyya akan gado, Sitti tace
"Meyake damun ki?""Ba komai Sitti bacci nake ji."
"To kinci abinci ne?"
Kai ta girgiza tace
"Na koshi."Bandaki ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci a jikin ta ta kwanta akan gadon Sitti.
*
Washe gari yini da safe duk yan mata na dakin Najwa, Maryam kuwa na dakin Sitti kwance Najwa tayi tayi ta fito taki dan tin jiya bata kara komawa wajen su ba Basma ce zaune suna hira jefi jefi, wayar Maryam ce tai kara ta dauka ta kai kunnen ta tace
"Asslamau alaikum."
"Wa'alaikum salam.""Ya kk ya gida?"
"Alhamdulillah.""Jiya kuma sai kika gudu."
"Kai nane yake ciwo.""Ayyah ya kike ji yanzu?"
"Ya daina."
"To sannu ya anjima fa? Nazo na kai ki?"Kai ta gyada tace
"To in mun shirya zan maka magana."
"Shikenan sai anjima."Sukai sallama, ta kashe wayar, Basma tace
"Wai da Muhammad za ayi ne? Affan na damu na fa.""Ke kyale wani Affan dan Allah."
"Uhmm shikenan."
Ta koma ta kwanta.Biyar har an fara kwashe yan tafiya wajen yinin bikin sauran yan matan suna waje suna jiran motoci, yau Maryam bata bi Najwa ba dan tin jiya ma bataje wajen ta ba da zasu tafi makeup tazo su tafi amman taki tace ba inda zata.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasía*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...