Book 1 page 1

994 33 0
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 1

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

******* ****** ******
Zaune suke a falon su wanda yake a gyare sai tashin kamshi yake ga sanyin AC da ya karawa dakin ni'ima. TV na ta aiki, komai na dakin red kaa ne daga manya manyan kujerun har labulayen dakin da center carpet din dake tsakiyar dakin mai uban taushi, wata dattijuwar mata da ba zata wuce shekara arba'in da biyar zuwa da takwas ce zaune gaban ta system, sanye take da less mai kyau da tsada daga yadda take kallon system din zaka san aiki take a cikin ta. Sai gefenta wani dan yaro kyakyawa wanda a ido bai zai wuce shekara biyu ba, sanye yake da wasu riga da wando bakake wanda suka kara fito da hasken fatar sa, gashin kansa a kwance baki sidik sai sheki yake, wasa yake da mota, sai wata kyakyawar budurwa da bata wuce shekara sha tara ba sanye da maroon kalar hijab wanda yake har kasa, waya ce a hannun ta tana daddanawa gaba daya hankalin ta na kan wayar. Sallama akai dabwata muryar mai dadin da zaki, daga bakin kofa amsawa sukai a tare. Wanda yai sallama ne ya shigo cikin takun sa na kasaita sanye yake da suit ash kala wacce ta amshi shi sai bakin takalmi sau ciki baki, hannun sa rike da brief case din sa. Fari ne tas dogo ga saje, idanun sa manya wanda suke ko da yaushe a lunshe sai dogon hancin sa, da madaidaicin baki sa ai agaye da pink lips masha Allah kyakyawa ne sosai.

Yaron dake wasa da mota ne ya d'ago yana ganin sa ya mike yayo wajen sa a guje yana fadin
"Abbi Oyoyo!"

Brief case din ya ajiye akan kujera ya daga yaron sama ya rumgume shi, yana murmushi wanda kumatun sa suka lotsa kan yaron ya shafa yace
"My Son ya gidan?"
"Abbi i miss you (nayi kewar ka)"
Ya fada da harshen da zaka san magana bata gama zama a bakin sa ba.

Matar dake aiki a system ce ta d'an d'ago tana kallon sa,  ya karaso cikin falon ya zauna a kan carpet din dake tsakiyar dakin tare da d'aura kan sa a gefen kafar matar yace
"Ummi nah sannu da gida ya aiki?"
"Alhamdulillah Dr ya aikin?"
Ta tambaya cike da kulawa.

"Alhamdulillah!"
Ya fada yana shafa sumar kansa da take kamar ta indiyawa sai sheki da kamshi take. Budurwar dake zaune ce ta dago fuska ba yabo ba fallasa tace
"Sannu da zuwa Yaya."

"Yauwah!"
Kadai yace ya mike rike da yaron yai hanyar dining inda wata kofa take suka shige. Da kallo ta bisu ta d'an tabe baki mikewa tayi tace
"Ummi bari naje wajen Inna."

"To ki gaishe ta."
Ta fita tana tafiya a hankali kamar ba zata taka kasa ba, saboda wayar da take dannawa kamar daga sama taji an zare wayar hannun ta da sauri ta d'ago fuska ta marairaice tana kallon wanda ya amshe wayar, wani kyakyawan saurayi ne wanda ba zai wuce shekara talatin ba, dogo ne fari tas dashi wanda yake da faffadan kirji, yana da idanu da hanci da bakin sa dan madaidaici, murmushi yake wanda ya kara masa kyau, fuska ta kara shagwabewa kamar zatai kuka tace
"Yaa Faroukkk"

Wanda aka kira da Yaa Farouk ne ya zuba mata ido wannan yasa tai saurin yin kasa da kan ta tana son wucewa ta gefen sa. Ya d'an kamo gefen hijab din ta,  ta juyo yace
"Kina tafiya kina danne danne sai kin fadi kinji ciwo ki barewa mutane baki kina kuka ko?"

Ido ta zaro ta, tace
"Kai Yaa Faroukkk ni din?"
Ta fada tana nuna kan ta.
"Eh ke din fa ke wa ya kai ki ragwanta, ko Haidar ya fiki jarumta."

Baki ta dan turo tace
"Uhmm ai kuwa na fishi wancan dan mitsitsin yaron."
Yai murmushi yace
"Shi fa. Yanzu ina zuwa?"

Bangaren Inna ta nuno masa tana fadin
"Wajen Inna."
"Nima can zani. Wai me kike dadannawa a wayar ne ko chat kike da siriki nane?"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now