💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 53By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Aliyu kuwa yana can masallaci yana ta addu'a ya dukufa a wajen sai wajen tara saura sannan ya mike ya fito jiki a sanyeye zuciyar sa sai bugawa take kamar zata fito daga kirjin sa. Inda su Ummi suke ya dosa yana shan kwana ana bude dakin aikin daya daga cikin nurse din ce ta fito rike da baby a hannun ta da sauri ya fara takowa Ummi ta mikawa Ummi na amsa ya karaso ya zura hannu ya amshe yaron yana leka fuskar sa. Murmushi ya saki sai kuma yai sauri ya mikawa Ummi ya kalli Nurse din yace
"Ya Maman sa?""Tana ciki komai lafiya."
A take a wajen ya juya ya kalli gabas ya durkusa yai sujudul shukur ya dago yana fadin
"Alhamdulillah Alhamdulillah."Dakin ya shiga yaga sun fara turo gadon da Maryam take kai da sauri ya karasa wajen kan ta yana kallon ta idon ta a lumshe amman ta kwarmin idon ta zaka gane ta fad'a bin bayansu yayi.
Su Ummi kuwa suna waje sai murna suke Mami ta amshi Baby, Tana fadin
"Masha Allah tabarakallah!"Inna ta amsa tana fadin
"Masha Allah, Allah ya raya mana kai."
Farouk ya karaso yana fadin
"Nima a bani dan Allah.""Iya daukar yara kai?"
"Kai Inna."
Ta mika masa ya amsa yana leka fuskar Babyn yace
"Wow fine Baby me kyau Tarakallah."Ya mikawa Abbi da Abba suma suka amsa sukai masa addu'a yadda mutanen nan ke farin ciki zaka rantse d'an cikin su ne ko jikan su. A haka su Aliyu suka fito ana tura gadon da Maryam take kai. Bayan su suka bi har aka karasa da ita dakin da aka tanadar dan kula da ita suna shiga su Ummi suka karaso rike da Baby. Bakin Gadon Aliyu ya karasa ya amshi Babyn hannun Ummi yace
"Ummu Haidar Bude idon ki, kiga Haidar din ki."A hankali ta bude idon ta, ta sauke akan fuskar Baby dan Aliyu ya dago mata da fuskar Baby yadda zata gani tana daga kwance
"Yaa Haidar ya tafi Yaa Haidar ya dawo."
Ta fada, da sauri duk suka kalle ta suna son suji daga ina maganar ta fito babyn ta amsa ta kifa a saman fuskar ta tana sakin wani kuka mai ciwo tare da fadin
"Allah ya raya min kai Haidar, Allah ya maka albarka ya kare ka daga duk abin ki ya baka ilimi mai albarka, Allah yasa alummar musulmi suyi afahari da kai, Allah ya raya min kai Haidar kai kadai ne gata na, Abbin ka ya tafi ya barmu sai gashi Allah ya dawon da me kama dashi."
Ta karashe magana tana mai cigaba da kuka, wanda kukan kanaji daga kasan zuciyar ta yake fitowa.Dago Babyn Aliyu yai yana fadin
"Yau naga raguwar Ammi kuka zaki fara koyawa Babyn ke da zaki masa addu'a gaskiya ba zan yadda d'ana ya koyi ragwantaka ba jarumi ne kada ki manta mai asalin sunan jarumi ne."Hannu ta saka tana share hawayen idon ta, wani bacci ta fara ji yana fizgar ta bata fargaba ya dauke ta. Ummi tace
"Aliyu kuma bacci take?"Ya duba yace
"Eh allurar bata gama sakin ta ba."
Ya mikawa Ummi Babyn.Abba yace
"Ba wata matsala dai ko?"
"Babu Abba."Abbi ya kalli agogo tara da rabi yace
"To Alhamdulillah dare yayi sai mu tafi ko? Tinda komai ya tafi lafiya."
Mami ta mike tana fadin
"To Ummin Aliyu mu zamu tafi sai da safe amman Aliyu yazo ya amso miki abinci tin safe bakuci komai ba, itama mai jegon kada ta tashi cikin dare tana jin yunwa ko?""Haka ne Mami mungode. Dr kaje ka kai su gida sai ka dawo din ko?"
"To Ummi!"
Lokacin har Abbi da Abba sun fita Mami da Inna suka bi bayan su. Farouk ya mike ya karaso wajen Ummi tare da zaro wayar sa dake cikin aljihu yace
"Bari na dauki hoton Babyn mu."Ya dauke shi sannan yai masa kiss a goshi yace
"Ummi sai da safe ki kular mana da Babyn."
Ummi tai murmushi Aliyu ya fita yana daddana waya. Abba ne ya dauki Inna, Abbi kuma ya dauki Mami Aliyu da Farouk kowa ya dauki motar sa. A kusan tare suka karasa gidan. Abba ya raka Inna har bangaren ta sannan ya dawo sashen sa. Aliyu na shiga ya nufi dakin sa yai wanka ya canja kaya sannan ya fito. Dakin Maryam ya shiga hado musu kayan da zasu bukata sannan ya fito.Bangaren su ya nufa ya samu Mami a kitchen tana hada wa su Ummi abinci har ta gama dafa tea. A basket ta saka masa da kayan tea da su lemo da ruwa sannan ya dauka ya koma asibitin.
Lokacin da ya koma Ummi na rike da Baby ya shimfida babbar carpet din da ya shigo dashi sannan ya ajiye kayan da yazo dasu a inda ya dace. Ya bude flask ya zuba ma Ummi abinci yace
"Ummi taho kici abinci nasan yau baki ci komai.""Kai ma haka ai Dr."
"Ummi na dan ci dankali da safe.""Wannan dashi da babu duk daya ai. Taho muci kaji."
Ya taho ya zauna kusa da Ummi zai dauki plate ta miko masa spoon tace
"Muci tare."Tare suka ci suka sha ruwa sukai hamdala sannan yace
"Ummi bari naje office na danyi aiki.""Yaushe zaka tafi gida dare na yi?"
"Ummi anan zan kwana.""Anan kuma Dr ka tafi gida gobe da safe kazo kaji."
Yai shiru tace
"Jeka kaji dan albarka."Dawowa yai ciki ya amshi Babyn yai masa addu'a sannan ya sumbaci goshin sa ya mikawa Ummi yana fadin
"Sai da safe to me zan taho muku dashi gobe?""Zan duba in akwai abinda muke bukata zan fada maka kan ka fito."
"To Ummi."Ya kara matsawa kusa da gado ya leka Maryam dake ta baccin ta, sannan ya juyo ya kara leka baby da kyar ya iya cewa
"Ummi sai da safe."
Ya fita.*
Washe gari tin asuba da ya dawo daga masallaci ya shiga kitchen shi yai musu breakfast ya hadawa Maryam abinda yasan zata iya ci marar nauyi ya hada komai a basket. Karfe bakwai ya fice ya bar gidan bayan ya gaida Abba tare da gabatar masa da abincin sa.Yana zuwa ya samu Ummi har taiwa Baby wanka ta shirya shi cikin kayan sanyi sky blue sai kamshin turare yake. Amsar Babyn yayi ya zauna yana fadin
"Ina kwana Ummi na?""Lafiya lou ya gidan?"
"Alhamdulillah ya my son da Maman sa?""Gata nan tana ta bacci har yanzu bata tashi ba."
Gadon ya kalla ya dauke kai ya mai da kallon sa kan Babyn yana fadin
"Baby nah yayi kyau Ummi tai maka kwalliya kai kyau my baby."Ya sumbaci goshin sa tare da zaro waya ya dauki babyn hoto yana fadin
"Ummi yaron nan tubarkallah kato dashi gashi kyakyawa."
"Ya maman sa take?""Ya fita kyau fa."
"Kai dai kace kafi son yaron ka.""No ba haka bane Ummi yanzu dai ki yi break din ki tukkuna."
"A'ah bari na fara wanka dai."Ta debi kayan ta ta shiga bandaki yana zaune rike da baby har ta fito cikin shiri sannan ta karya. Karfe takwas sukaji ana knocking kofar dakin izinin shiga suka bayar sai ga Farouk ya shigo da sallama suka amsa ya karaso ya zauna gefen Aliyu yana fadin
"Ina kwana Hamma?""Ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah!"
Ya fada yana leka Babyn sannan ya dago yace
"Ummi ina kwana?""Lafiya lou ya gidan?"
"Alhamdulillah!"Ya kalli Aliyu yace
"Hamma ka ban Babyn mana nifa shi nazo na gani kan na tafi aiki."Mika masa yayi sannan ya mike yana fadin
"Bari naje Ummi ba abinda kuke bukata?"
"Babu Dr."
Ya juya ya fita. Bai jima da fita ba mai aikin su ta kawo abinci daga wajen Mami. Farouk sai da Ummi ta kore shi sannan ya tafi da kyar wajen tara.Karfe goma Maryam ta farka Ummi ta karasa tana fadin
"Sannu Maryam!"
"Yauwah Ummi nagode."Murnushin fuskar Ummi ne ya dado jin da gaske maganar Maryam ta dawo. Ummi tace
"Bari a kira Dr dan ya duba ki ko?"Kai ta gyada Ummi ta kira Aliyu ta sanar dashi, Dr da tai mata aiki ya kira ai kuwa nan da nan tazo ta duba ta komai normal bayanin abinda zataci tai mata da yadda za ai mata wanka dan kar ruwa ya taba inda aka manne dan ba dinki akai mata ba cealing (like) wajen akai.
*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin*
*Antty*
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...