💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 33By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
******
Kano
A lokacin da Abbi ya dawo daga masallaci ya shiga bangaren Ammi a dai-dai lokacin Ammi ta farka daga baccin da take tun jiya cikin hanzari Abbi ya karaso yana mata sannu tare da taimaka mata ta zauna, bin dakin Ammi tafarayi da kallo a hankali abunda yafaru yafara dawo mata sabo fil a kwakwalwanta nan take hawaye suka fara zubowa akan kuncinta kallon mijin nata tayi cikin rawar murya tace
"Shin da gaske ne abunda kunnuwana suka jiyemun ko kuma mummunan mafarki nayi..!"Abbi baice da ita komai ba, dan halin da yake ciki, mahaifin sa Malam ya aiko yaje a yau yau din nan wanda ya tabbata akwai matsala bai sam a yaya Malam zai dauki abun ba. Kallon ta Abbi yayi ya mike ya nufi cikin toilet itako ta bishi da kallo zuciyarta na bugawa saboda tsabar tsoro da fargaba bai dade ba ya fito yace
"Ki tashi ki kimtsa kiyi sallah lokaci na tafiya..!"A hankali tafara saukowa daga kan gadon ta nufo inda yake ta dafa bayansa cikin sanyin murya tace "Alhaji Ina tambayarka kamun shiru ina Maryam take, da gaske ba a ganta ba?"
Runtse idanu Abbi yayi cikin tsantsar bakin ciki da bacin rai ji yake kaman ya hadiye zuciya ya huta da kyar ya iya saita kansa ya juyo ya kwakulo murmushin dole ya daura akan fuskarsa saboda Dr yace a guji abunda zai bata mata rai ko ya tsorata ta nan kusa, dafata yayi cikin tsigar rarrashi yace
"Kije kiyi sallah lokaci na wucewa zan miki bayanin komai zuwa anjima..!"Ya karisa yana mai kama hannunta ya nufi bakin toilet da ita, haka ta rika binshi duk da tana cikin fargaba da tsoro amma kuma haka nan taja bakinta tayi shiru tabi umarninsa, yana ganin ta shige ya juya ya fita falo bai jima ba ya koma daki akan sallaya ya tarar da ita tana lazimi don haka sai ya koma sashen sa ya shiga bathroom shima ya watsa ruwa har ya fito ya fara shafa mai bayan ya gama ya kimtsa a cikin fararen kaya a dai-dai lokacin ne ya koma sashen Ammi ya same ta akan sallaya har lokacin tana ganin sa ta mike tana ninke sallaya hade da gaishesa fuskarsa dauke da murmushi ya juyo yana amsawa hade da tambayarta ya karfin jikin nata yanzun tace dashi Alhamdulillah da sauki sosai kafun ya sake cewa wani abu wayanshi dake kan gado tayi ringing.
Sai da gabanshi yafadi ganin numbern dake yawo akan screen na wayar cikin sanyin jiki Abbi ya daga wayar
"Malam yace a yau yake bukatar ganinka.."
Iyakacin abunda aka fada kenan wayar ta yanke wani yawu mai daci ya hadiye, zuciyarsa cike da fargaba da kuma tsoro dakyar ya saita kansa ya kama hanyar fita yana mai cewa
"Idan kin gama shiri ina jiranki a falo kuma kiyi sauri munkusa makara.....!"Baki a sake ta bishi da kallo kirjinta na cigaba da bugawa tunani take ina Maryam take? Sannan me Abbi yake nufi da kin gaya mata komai? To wai ma ina zasuje can kuma ganin babu inda tunani zai kaita yasa ta bude wardrobe a kasalance ta dauko kayanta ta saka babu wani kwalliya ta dauki mayafinta kawai ta rufa ta fito a falo kuwa ta tarar dashi.
Baice da ita komai ba ya nufi hanyar barin dakin ta bishi a baya suka nufi parking space inda Alkasim da Abdulah suke tsaye suke jiran fitowansu, da daddaya suka rika gaishe ta da tambayar ta ya jiki itama jiki a sanyaye ta rika amsawa tana mai karewa gidan kallo kamar ranar ta fara ganin sa, haka nan suka shiga suka tada motar maigadi na musu Addu'an dawowa lafiya.
Alkasim ne ke Jan motar a yayin da Abdullah ke zaune a gefensa su Abbi kuma suna zaune a baya, duk yadda Ammi taso tambayan Abbi abunda ke faruwa hakan ya faskara saboda bai bata fuskan hakan ba haka suka cigaba da tafiya shiru babu mai magana.
Dan su Yaa Muhammad da su Yaa Ummulkhairi sun rigasu barin garin tin safe saboda Ammi bata tashi ba shiyasa su Alkasim basu tafi ba, duk da Alkasim bai so ya tuka Abbi ba dan ba yadda zai yi amman yana jin ciwon abinda Abbi yayiwa Maryam yanzu ko tana wane hali duk damuwar sa ya take ya jikin ta.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...