💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 35By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Wata ajiyar zuciya Matar ta sauke duk da bata gama yadda da yarinyar ba amman jin cikin ta yana da uba yasa ta dan ji dadi. Kallon ta tayi tace
"Na fada miki bana son karya ki fada min gaskiya.""Wallahi Allah gaskiya na fada miki ban san kowa da komai ba wadan nan mutane biyun su kadai na sani. Wallahi da gaske nake ba karya nai miki ba. Dan Allah ki taimaken ki kai ni gidan marayu na karasa rayuwa acan ba wanda na sani anan. Am just suffering here ba inda na sani please help me"
Ledar magani ta janyo ta miko mata ta bata idon ta ne ya kawo ruwa. Ummi ta dan bata fuska tace
"Bazaki sa nayi asarar kudi a banza ba daga jiya zuwa yau an rubuta magani na sama da dubu goma sannan ace ba zaki sha ba in baki sha ba tayaya zaki samu lafiya. In baki amsa kin sha ba bazan taimakeki ba zan tafi na barki kinji ko?"Amsa tayi ta bata ruwa ta watsa maganin ta sha kirji ta dafe tana son ta mike dan amai take ji. Da sauri Ummi ta kamo ta, ta fara shafa bayan ta a hankali a hankali. Ahankali taji ya fada mata amman da yake ita makiyar maganice har da kukan ta. tace
"Tashi kije ki kwanta."
Mikewa tayi ta hau gado tana kwanciyya ta lumshe ido take bacci ya dauke ta.Wayar Ammi ce ta fara ringing ta dauka tace
"Ya akai My Son!"
"Ummi banji daga gareki ba.""Name fa?"
"Na tasowar taku!""Oh Aliyu... In mun taso zan sanar maka wallahi yarinyar nan ce she is suffering tana bukatar kulawa daga likitoci sosai da sosai."
"Ummi where is her relative!""Aliyu yarinyar ce sosai bama wannan ba abubuwan dake damun ta suna da yawa na daya bata magana a yadda na lura kamar tayi losing memory tana rayuwa ne ita kadai gata yarinya tana cikin hatsari ban san ya zanyi ba."
"Ummi ki bata duk kulawar da ya dace but please Ummi your Son is missing you wallahi ko abinci bana iya ci you know abincin ki nake iyaci kawai"
"Ina na Innar ka!""Kai ki bar innan nan ai kinsan halin ta dan bakya nan rowa take min in tai abu ta boye bata sammin"
"Kai kuma bakin kwadayi ko?""Ummi kinsan Inna ai tasan all what i likes eating to da gayya in ina dakin ta take girkawa kamshi yana busoni taki sammin."
"Ai gwara tai maka haka kaga kayi aure a huta ko?""Kai Ummi wane aure ana zaune kalau. Ai ni na gama aure Ummi."
"My son shekaru na tafiya fa shekarar Maryam nawa da rasuwa amman ace bazaka kara aure ba. Shekara sama da takwas fa, auren shine cikar ka na babban mutum gaka har babban mutum amman baka cika ba dan auren shi zai sa ka zama babban mutum.""Ummi ya jikin yarinyar da kuke tare?"
Kallon Maryam dake bacci tayi tace
"Da sauki.""Allah sauwake."
"Amin""Please Ummi duk yadda za ai gobe ki dawo."
"Insha Allahu my Son."Sukai sallama. Abbah ne ya shigo tai masa bayanin komai. Shiru yayi yace
"Ya kike ganin za ayi!"
"Alfarma zan nema a wajen ka!""Ina jin ki!"
"Zan tafi da Maryam na cigaba da kula da ita har ta sauka lafiya tayi recovery in ta tino komai sai mu maida ta ga ahalin ta.""Aisha kenan. Kina son taimako. Allah baki ikon kulawa da ita kinsan ba zan hanaki ba kuma yarinyar na bukatar taimako. Allah baki ladan taimakon."
"Amin!"Washe gari da safe.
Da kan ta, ta taimakawa Maryam tai wanka ta fito ta shafa mata mai sannan ta bawa wata rigar tata ta saka. Tea ta hada mata ta miko mata. Fuska ta bata. Ammi tace
"Ki daure ki sha kinji ko zaki dawo dashi wani zai samu ya zauna. Ko akwai abinda kike so?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...