💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 78By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Dis page is ur Amina Yar'adua i really appreciate with all ur comment keep it up. I heart you Mamanah*
Ya kashe wayar tabi wayar da kallo sai ta mike, hijab ta saka har kasa sannan ta fice daga dakin, a compound ta same shi ta karasa tana fadin
"Ina yini Yaa Ahmad?""Lafiya lou, ya gida ina My son?"
"Yana can wajen su Ummi ina jin."Sukai shiru sai kuma ya dago ya dan kalle ta yace
"A baya naso na maye gurbin aboki na amman Allah bai nufa ba, Allah ya karasa kin tabbata a matar Haidar din ba abinda zance sai fatan alheri."Kan ta a kasa tace
"Nagode Yaa Ahmad."
Yayi mata murmushi
"Babu wata godiya mata zaki bani kawai."Itama tayi murmushin tace
"Wacece nai alkawarin ni kuma Insha Allahu."
Yai murmushi yace
"Shi nazo na fada miki amman ina neman wata afarma."Kai ta gyada yace
"Ina so ki dauken tamkar Alkasim wanda in kina bukatar taimako ko wani abu direct zaki fada min ni kuma zan ji dadi fiye da yadda zaki zato, kuma ina son ana bani Haidar yana zuwa gidana hutu.""Insha Allahu Yaa Ahmad, Haidar kuma d'an ka ne."
"Haka ne sai batu na biyu."Kai ta gyada yace
" 'Kawar ki nake so Maryam, a jiya na fara jin wani abu game da ita, ta kwanta min itama tana da sanyin hali kamar naki, ina fatan zaki tayani mika kokon barata, a gida an damen da batun aure ina ta dojewa dan ina sa ran dawowar ki to yanzu kin dawo a matsayin Matar aure kin ga dole nima na nemi mata ko?""Haka ne Yaya duk da mun jima ba tare ba amman har yanzu Rukkaya na nan a yadda na san ta, tana da sanyin hali da hakuri, tabbas kun dace da juna ba tin yau ba nake maka sha'awar ta, ashe dai da rabon, Allah nagode maka, Yaa Alkasim ya auri Aisha kai kuma Rukayya, nice dai na rasa Yaa Haidar, ko da yake nima ban rasa shi ba tinda ga wani Yaa Haidar din."
Tai magana hawaye na taruwa a idon ta sai yaji tausayin ta kai ya dauke yace
"Zan tafi yaushe zaku koma?""Jibi!"
"Ok zan zo muyi sallama gobe, ki turon number Rukuyyan."
Kai ta gyada ta juya kenan Yaa Haidar ya karaso kusan cin karo sukai ta dago da sauri, idon ta dake cike da hawaye ta dago suna kallon juna, gefen sa tabi tayi cikin gida ya karasa wajen Yaa Ahmad suka gaisa yace
"Ai ban san da aure a tsakanin ku ba sai jiya, ina maka fatan alheri da fatan Allah ya kawo zuria ta gari, muna godiya da dawainiyya Allah saka da gidan aljanna.""Amin Amin Ahmad."
Ya saki hannun sa yabi bayan Maryam dan duk hankalin sa na kan ta, yana shiga falo ba kowa dakin ta ya nufa direct, yana shiga ya same ta kwance akan gado ko hijab din ta bata cire ba, karasawa yayi ya zauna a gefen gadon yana dago ta gaba daya, a zabure ta dago ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya, a jikin sa ya matse ta yana fadin
"Menene?"Kai ta hau girgizawa yace
"Fada min sirrin zuciyar ki."
Kin magana tayi, yasa hannun sa ya dago kanta, ta runtsa idon ta yace
"Ni dai na gaji wallahi dan Allah fada min abinda na jima ina gani a cikin idon ki."Da sauri ta bude idon ta tana son taji me ya jima da gani a cikin su, ganin Maryam na son raina masa hankali yasa ya sake ta tare da fuskantar ta, hannun ta dukka biyun ya kamo ya rike ya dago fuskar ta ya saita da tashi yace
"Ki tsaya a haka."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...