💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 44By
*MARYAM S INDABAWA*Hakuri da Juriyya Online ✍
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
A sama ya same ta a dakin Maryam, ta taimakawa Maryam ta shirya tana zaune tana lallabata ta sha ko tea ne amman taki sai lemon da ta sha kawai. Shigowa yayi ya durkusa a gaban su. Ummi ta mike tana fadin
"Ina zuwa bari na kira office naji dan yau da kyar zan fita ban san wa zan barwa Maryam ba.""Ba aikin da zakiyi ne?"
"Wallahi akwai wani case da aka kawon nake son na fara aiki akan sa amman ban san tayaya zan ba ina ganin ko na samo me kula da ita."Zama yayi sannan yace
"For today u can go and do your work since i will not go any where!"
"Kai amman nagode kuwa Son kaga na samu nayi abu da yawa yau."Ta juya ta fita. Ya juyo ya kalli Maryam da ta hade kan ta da gwiwoyin ta. Gyaran murya yayi yace
"Kinsan ba za dai ki zauna haka ba komai a cikin ki ba ko? Ko kina son ki rasa Babyn dake cikin ki?".Da sauri ta dago tana kallon sa hannun ta akan cikin ta. Sai ta hau girgiza kan hawaye na zubo mata. Yace
"Fada min me kike so?"
Kai ta girgiza ya dauki cake din gaban ta ya mika mata. Amsa tayi ta kai bakin ta kadan ta gutsura ta tauna ya kalle ta yace
"Kara mana!"Ta dago ta kalle shi, murmushi ya dan mata yace
"Kici kinji!"
Kara gutsura tayi dai dai lokacin da Ummi ta shigo cikin shirin ta na tafiya aiki. Ta kalle ta ta saki murmushi tace
"Tana ci kenan!""Eh tana dan ci."
Ya bata amsa, ta karasa wajen Maryam ta dafa ta tace,
"Daugther zan fita aiki but i will soon come back, ga Yayan ki nan he will take care of u if u need any thing else tell him. Allah baki lafiya!"Hannun ta ta kama tai mata godiya sannan ta mike ta kalli Aliyu tace
"Son am going take care!"
"Insha Allah!"Ya mike zai rakata tace
"No ka zauna wajen ta takarasa kaji!"
"Ok!"Ta juya ta fita yana mata addu'a sannan ya kalli Maryam yace
"To ki dan sha Tea din!"
Idon ta ne ya ciko da kwalla. Yace
"Try it!"Cup din ta dauka ta kai bakin ta dumim tea din yasa ta kafa kai sai da tasha rabi sannan ta ajiye, kirji ta dafe yace
"No kar kiyi kinji!"
Kai ta gyada amman yadda take jin tashin zuciyar bata san lokacin da ta mike da sauri tayi bandaki ba. Da sauri yabi bayan ta.Ummi na sauka ta samu Farouk zaune a falo. Kallon sa tayi tace
"Ah Farouk kai kadai zaune anan!"
Kai ya shafa yace
"Nazo wajen Hamma ne!"Sama ta kalla tace
"Yana sama ai! Kaje ka same shi!" "Toh fita zakiyi?""Eh zani aiki ne!"
"Adawo lafiya Allah tsare.""Amin!"
Ta juya ta fita shi kuma ya haye sama ya nufi dakin Ummi ya murda. Kakarin aman ta ya jiyo da sauri ya juya ya fita yana yamutsa fuska. Anan falon sama ya zauna yana pressing phone nasa.Ganin ya kwashe wajen minti goma bai fito ba yasa ya nufi dakin. Ganin su yayi sun fito a toilet din Maryam na gaba Aliyu na bayan ta. Kan gado ta kwanta taja bargo ta rufa ya karaso cikin kulawa da tausayi yace
"Sannu!"
Kai ta gyada ya dago yana kallon Farouk dake tsaye fuska a yamutse dan Farouk ba dai kyamkyami ba."Kaje daki na ka daukon wata leda akan kujera!"
Da sauri ya juya bai jima ba ya dawo ya mika masa leda ya juya ya fita. Ruwa ya dauka a ciki ya hada ya saka mata nan take bacci ya dauke ta. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kwashe kwanukan wajen ya fita dakinFarouk ya gani zaune ya kalle shi ya nufi stair da sauri Farouk ya karaso yana fadin
"Kawo big bro!"
Ya amsa ya sauka Aliyu yabi bayansa. Kitchen ya kai ya dawo ya sami Aliyu a kasa yace
"Hamma wai wacece wacan ne?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...