💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 87By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Daga baya mota suka koma sai da ya gama shanye jan baki ta sannan ya kyale ta, ta dago tana masa hararar wasa mai cike da so da kauna, daurin ta ta fara gyarawa ta kalli kan ta a mirrow, duka ta kai masa a kirji tana fadin
"Shine ka shanyen jan baki ko?""To ya za ayi Ranki ya dade?"
"Kaje ka siyo min yanzu."An gama ya fara kokarin tada motar da sauri ta zare mukullin tace
"Yadda zakaji dadin mai dani gida ko?"Yai dariya yace
"Sai na kawo karshen rigimar ko?"
"Yaya."Ta kira sunan sa, ya kalle ta dan yadda ta kira sa kadai zaka san abun da zata fada mai mahimmanci ne,
"Matar Yaya."Ta saki murmushi tace
"Ni dai in mun shiga kada kayi dariya kaji."
Dariya yayi yace
"To saboda me?"Baki ta turo tace
"Ni bana so."
"To toh an gama ranki ya dade uwar gida kuma amarya a gidan Aliyu Haidar."Ta bude jaka ta dauki mudubi ta shafa man lebe, kallon ta yake har ta gama ta gyara daurin ta sannan tace
"Ya nayi?"
Tai maganar tana dage masa gira, murmushi ya saki yace
"Yes kamar mu koma gida."Hannu ta sa zata bude kofa yai saurin saka lock yace
"Ranki ya dade ki tsaya ki daina abu da sauri fa yanzu kin san akwai little a cikin ki."
Ya fada yana shafa cikin nata cikin wani salo, hannun sa ta buge tana mai shagwabe fuska kamar zatai kuka tace
"Allah Honey ka bari.""Na bari."
Ya fita yana dariya ya zagayo ya bude mata kofa ya mika mata hannun sa ta kamo ta fito ya rufe a haka suka karasa hall din da yake cike da mutane hannun ta cikin nasa, kowa ya sha kwalliya ya kece raini bama da yake sun hada biki da masu siyasa.Suna shiga Yaa Muhammad ya hango su sai da gaban sa ya fadi dan tin ranar dinner su bai kara ganin Maryam ba sai yau, sai yaga ta kara kyau tai haske da sauri ya dauke ido yana istigifari dan yadda shaidan yasa zai fara yabon matar wani, hannun Maryam cikin na Yaa Haudar suka fara shiga nan su Yaa Hannah, Yaa Asiya da Yaa Bilkisu da Najwa da Basma wanda suka sha kwalliya cikin hadadden less suka karaso suka rufe su suna liki tin kan su karasa tsakiyar hall din nan aka hau musu kirari, Tasleem bakin ciki kamar ta hadiyi zuciya.
A haka sukaje suka gaishe da su Ummi da Mami, da Momy, da Mama sannan suka karasa wajen da aka ware musu ita dashi wanda an anjiye musu lemo da ruwa, tana zama ya kalle ta yana sakar mata murnushi, ta dan harare shi tace
"Murmushin me kake?""Shikenan ni kuma ba zan wa matata murmushi taji dadi ba."
"Hmm Yaya wannan daban kayi shi."Wani murmushin ya kara ta mike tace
"Kaga ni bari naje wajen amarya da ango."
"Yanzu fa kin zama Anty ki zauna zasu zo su kwashi gaisuwa."Ya fada yana dawo da ita ta zauna, ai kuwa ana kiran amarya da ango su fito wajen su Yaa Haidar suka fara zuwa mai vedio da camera suka hau biyo su har suka karaso aka hau musu picture nan su Najwa suka karaso duk akai dasu daga nan suka shiga fili suna musu liki sosai sukai musu liki, su Najwa, m Yaya Hannah ana ta rawa, Yaa Haidar ya janyo hannun Maryam dan yaga yadda Najwa ke jijjiga ta wai sai tai rawa shi kuwa bai son ana jijjiga ta dan baya son a wahalar masa da Babyn sa.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...