💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 70By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Kuka ta fashe dashi ta fada jikin sa wanda suka kara jin wannan abun da ya tsarga musu har tafin kafar su, kuka take sosai wanda yake jin sa har cikin kasan zuciyar sa, hannun sa ya daura a bayan ta yana lallashin ta tare da fadin
"To ya isa kinga bakya jin dadi kuma ba ason damuwa a tare dake ko akan wani can zaki mana asarar kanki, kin fi son sa akan ahalin ki?"Kai ta hau girgizawa yace
"To ki daina kukan kinji."
Kai ta gyada ya hau lallashin ta har ta daina ya dago ta yana taba jikin ta da ya dau zafi yace
"Me yake miki ciwo yanzu?"Kanta ta nuna masa ya daura hannu akan zuwa wuyanta wanda tsigar jikin ta ta wani irin mike yace
"Zazzabi ma nake ji a jikin? Kin sha maganin ko allura zan miki?"Fuska ta shagwabe ta koma ta kwanta ya rakwafa yace
"Oh allurar kike son kenan ko?"
Da sauri ta dago wanda hakan yasa fuskar su ta hadu da juna hannayen sa yasa ya tallafonta yana dage mata gira a hankali yace
"Ayi allurar?"Kafada ta make sai kuma ta fashe da kuka yace
"A'ah da wasa nake ba za ai miki allura shikenan."
Kai ta gyada dai dai jin an kwankwaso, suka bada izinin shigowa Aisha ta shigo hannun ta rike da basket tace
"Sannu Patient."Ta kalli Aliyu tace
"Sannu Dr ya me jikin?"
"Da sauki."Basket ta ajiye tana ganin Maryam na matsawa daga kusa da Aliyu, kai ta dauke tace
"Abinci na kawo mata Dr gashi nan ka bata taci."
Wani kallo Maryam ta zabga mata tace
"Ni na koshi.""Kasan Allah tin tea bata kara shan komai ba, yanzu naje nai mata pepper soup din ko zataji dan dadin bakin ta."
"To sannu mungode."Ta juya tana wa Maryam gwalo ya dauki bowl ya zuba mata ya dauki spoon ya ajiye akan stool ya karasa ya daga ta ya jingina ta da filo ya fara bata da kansa sosai taci sannan ya barta da dabara ya bata magani ta sha lokacin likita yazo ya kara dubata, bayan ya gama Aliyu yace
"Ya jikin nata?""Da sauki sosai sai dai naji zazzabi yanzu."
"Abinda na gani kenan.""Zan bata maganin insha Allahu zai sauka."
"Please in ba damuwa a bamu sallama mu karasa a gida kaga yadda muke cika asibitin nan.""Eh ba wata matsala sai ka cigaba da duba ta a gida din amman dan Allah a kula da bata mata rai, sannan ki rage tunani kinji?"
Ya fada yana kallon Maryam.Kai ta gyada yace
"Allah kara sauki."
Ta amsa da amin ya juya ya fita. Daga nan suka hada kayan su suka tafi gida.*
Washe gari gaba dayan su ne zaune a falon Abbi, banda Mama da ko asibiti bataje duba Maryam ba da taji anga ahalin sai ma karyawata tayi dan bata so ba, ta so rayuwar ta ta lalace gaba daya.Abbin Maryam ne yace
"Ba abinda zamu ce muku sai godiya da yadda kuke rike mana Maryam da Abubakar Allah ya biya ku da gidan aljanna hakika ku mutanen kirki ne samun irin ku sai an tona ba abinda zamuyi muku sai addu'a Allah ya saka muku da mafificin alheri ya biya ku da gidan Aljanna.""Ah haba ai yiwa kai ne, dan yanzu daga Maryam har Abubakar ai duk namu ne duk mun zama zuri'a daya."
Abbin Haidar ne yai wannan maganar.Mami dake zaune jikokin ta a jikin ta ta rasa ina zata sa kan ta dan murna yau ita da ake cewa ba zata taba ganin jinin ta ba sai gata ga danta ga jikoki har guda shida na Abubakar biyar na Haidar d'aya, kai alhamdulillah, hakika a baya Allah ya jarabce ta amman amsa kaddarar ta yau Allah ya bata wannan tukwincin ba abinda zata ce sai Alhamdulillah, Haidar kuma Allah masa rahma.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasi*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...