Page 13 Flash back

440 20 1
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 13

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

~Flash Back~
'''July 2017
Kano State'''

'''*MANS GIRLS COLLAGE* shine sunan dake rubuce a saman wani katon gini wanda aka kwata shi rubutun kan sa abun kalla ne, banda ginin  da yake katon gaske wanda ginin mai kyau ne, da tsari dan ba dan an rubuta makaranta ba da ba zakace makaranta bane dan kyau da tsarin ginin, wanda yake da bene har wajen hawa uku. Wanda makarantar tai fice a cikin garin Kano da kewaye duk wani d'an wane wato masu kudi, yan siyasa, da masu mulki, da wanda ke ji da kansa nan ba wai dan tsadar makarantar ba a'ah sai dan yadda makaranta take da manyan kuma kwararrun malamai. Dan malaman duk kan su kwararrun ne kuma suma dan suna samun salary mai kyau shiyasa suke kara zama a wajen duk da wasu suna aikin gwamnati kuma suke kara zuwa suna aiki a wajen.

Da ka shiga babban gate din babban harabar (compound) wanda yake dauke da wajen adana motoci (parking space) an saka masa rumfa an kwawata harabar wajen (compound) da shuke shuke,  wanda har wani round about akai a tsakiyar makarantar an rubuta sunan makarantar da manyan baki kuma an kwatashi. Duk ka makarantar an malaleta da kwalta wajen yayi kyau, kato ne sosai dan in anzo ziyara  (visiting) din dalibai duk anan ake ajiye motoci (parking) duk yawan mutane wato iyayen yaran da zasu zo wannan harabar (compound) din na dauke su kamar yadda yau yake ma cike da manyan motaci masu kyau,  tsada duk ka dai saboda yau dalibai makaranta ake yaye su (graduation) wanda duk iyaye suka zo daukar yaran su.

Ba motar da ta karewa kowa in zai fita duk da wajen ba kowa sai d'ai d'ai kun drivers sauran ma kuwa duk suna cikin mota iyayen kuma suna can cikin makarantar. Wanda bayan wannan harabar (compound) din akwai wani a ciki wanda anan bangaren malamai yake da ajujiwa (classes) din daliban makarantar shima wannan compound din an kwata shi sosai dan har filin (wasanni) sport, Assembly hall,  meeting hall,  da Special hall wanda anan ake duk manyan taro na yaye dalibai ko speech and price giving day da holidays da sauran abubuwan duk anan suke,  wanda iya nan wajen da dalibai suke iya fitowa daga nan sai can cikin makaranta wanda a can ne hotel yake da sauran abubuwan entertainment na makaranta.

To yau special hall ne ya dauka dan yau SS 3 student sukai graduation wanda tin 9:30am suka shiga exam suka fito 12:30pm suna fitowa dukkan dalibai cikin makaranta suka koma suka wanka sukai sallah sannan suka shirya cikin kayan su na graduation. Duk kan su yan mata ne wanda suke daga kan shekara 16,  17,  18 and 19 kuma duk wacce zaka kalla zaka gane yar hutu ce domin in kana *MGC (MANS GIRLS COLLEGE)* tamkar kana gida ne yadda ake kula da kai da komai na rayuwa dan kowa yana da system a hannun sa haka suna da wayoyi amman duk inda takwas na dare yayi an amshe wayoyin su haka nan karfe tara duk dalibai dole su tafi su samu entertainment sunyi kallo na awa daya zuwa awa daya da rabi da sun tashi kowa zai wanka da alwala sannan a kwanta kan sha daya dole kowa yai bacci kuma duk bayan awa daya zuwa daya da rabi Nanin dakin zatana mikewa tana duba lafiyar kowa wanda karfe biyar duk suke tashi suyi wanka suyi alwala sannan su shirya suyi sallah. Kan 6:00am sun gama komai har azkar wanda daga nan dining hall suke tafiya a can kowa zai zabi abinda yake bukata wanda kafin 7:00am an kawowa kowa nasa yai break daga nan su tafi assembly hall minti talatin suke yi ake tafiya aji wanda a ragowar minti talatin din zasuyi kintsa kan a fara class activities at 8:00am wanda karfe 10:30am ake fita tara, shima kowa abinda yake so zai zaba ya amsa, 11:00am ake dawowa 1:30pm ake tashi wanda ana tashi ake sallah daga nan abasu minti talatin dan suje suyi wanka suci abinci sannan su fito isilamiyya. 3:45pm kuma ake sallah sannan su koma sai 5:30pm ake tashi wanda anan kowa ake bashi wayar sa inda abinda zai yi yayi har ai magariba da isha'i a amsa. Haka rayuwar su take daga Litinin zuwa Laraba wanda Alhamis da Juma'a basa isilamiyya suna shiga catering class ne a koya musu girki kala kala wanda Asabar da Lahadi kuma tahfiz suke zuwa tin 7am har 5pm. Hatta uniform wanke musu ake kowa da sunan sa a jiki za a ajiyewa kowa nasa. Kuma basa taba saka kayan gida kullum kayan makaranta suke sakawa (personal wear they always put uniform) wanda suke da na normal school,  na Isilamiyya,  na catering,  na tahfiz,  sport,  entertainment,  da kayan bacci (sleeping dress) duk iri daya sai dai kowa da sunan sa ko kuma yan room kaza su zama on one colour like red,  blue,  yellow,  pink etc

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now