Page 38

349 17 3
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 38

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

*
Abba na gidan tsakiya Ummi da Maryam na gidan baya, Maryam kwance akan cinyar Ummi tana ta bacci dan yanzu ba abinda take yawan yi sai bacci. Har suka Iso Kano bacci take. Suna shiga Kano, ta mike ta matsa jikin Ummi tana karkare wa kamar me tsoron wani abu. Ummi tace
"Menene Maryam?"

Jikin Ummi ta fada ta rufe fuskar ta tana girigiza kai,
"Alhaji akwai abinda zakuyi kan mu karasa airport?"
Ado Driver ya tambaya.

"Aah! Mu zarce airport kawai. Madam ko kina so wani abu!"
"A'ah Maryam ko kina son wani abu ne?"

Kai tai sauri ta girgiza kan ta a boye a jikin Ummi.
"Mu tafi airport din lokaci ma ya kusa."
Direct Aminu Kano Airport suka tafi suna zuwa suka shiga suka dan huta, Aliyu ta kira ta shaida masa yanzu zasu taho yai musu addu'a sannan yace
"Ummi ina asibiti da kyar na samu na dauko ku."

"Kada ka damu kaji."
"To Ummi zan aiko Baba Halliru sai ya dauko ku tinda naga Baba Ado ne ya kai ku nan ko?"

"Eh sun taho suma nasan nan da magariba zasu karaso."
"Allah kawo su lafiya."

"Amin!"
"Ya me jikin?"

Kallon Maryam tayi wacce ke jikin ta a dukunkune tinda suka shigo Kano take a haka wanda ta ki ta saki Ummi sam kamar wanda ke ganin wani abu.
"Gata nan!"
Ta fada tana shafa kan ta."
"Ai mata sannu!"

"Zataji!"
Sukai sallama sannan ta shafa kan Maryam tace
"My Son na miki sannu!"
Kai ta gyada kawai. Karfe uku jirgin su ya fara haramar tashi.

Abuja
Karfe biyar saura suka fito daga cikin airport din cikin wasu jerin gwanon motoci wajen guda biyar biyu a gaban tasu biyu a bayan tasu an saki jiniya a haka suka ratsa babban titi suka nufi gida kai tsaye. Bakin wani katon hadadden gida sukai horn security ya bude katon gate din ciki suka shiga a jere.

Babban compound ne sosai dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar gidan kasan naira ta zauna, makeken tsakar gidan na dauke da sassa har uku manya masu fenti iri daya, ko wanne sassa kuma akwai tazara mai tsayi tsakaninsa da wani sassan, sashin farko da na biyu, wanda na farko shi zaka ci karo da bayan shigowar ka gate din zamanin dake babban gidan ba dai girma ba wanda girman sa daya da tsaruwa a komai da na kusa dashi. Manyan gida ne masu girman gaske sai parking space gari guda dake gefe.,  a cikin ko wanne. Banda na main compound da yake dauke da securities room da boy quaters. Gidan ya tsaru iya tsaruwa da kyau ko ina neat sai kamshi yake ga ni'ima saboda shuke shuken da suke dashi.

Suna parking suka fito Ummi rike da hannun Maryam da ta gama galabaita saboda gajiya da tayi ga ciwo ga yunwa duk ita kadai. Second part dake cikin gidan suka nufa,  hannu ta saka ta karkashin wata tukunyar shuka sannan ta dauki key. Abba ta bawa ya amsa yai bismillah ya zura key din ya bude. Kamshi ne ya dake su tare da sanyin AC. Shiga yayi da sallama Ummi tabi bayan sa rike da hannun Maryam.

Katon falo wanda yake dauke manya manyan kujeru wajen set uku maroon kala and milk,  labulayen ma maroon kala ne da adon milk sai milk center carpet da center table a tsakiyar dakin. Gefen kujerun kuma side stool ne yan kananu a tsakan kanin kujerun. Can gefe kuma dan step ne wanda ke dauke da dining table da dining carbinate an saka musu wani labule mai igiyoyi milk an maroon ka. Ta gefen dining  akwai kitchen, sai gefen dining da wata kofa, da matattakalar bene sannan akwai corridor dake dauke da three room two bedroom da resting room.

Suna shiga Maryam ta lumshe ido ta saki Hannun Ummi kasan tile ta kwanta tana mai lumshe ido. Ummi ta kalle ta sannan ta karasa ta kamata tace
"Ba a son kwanciyar kasa fa."
Akan three sitter dake gefe ta kwantar da ita Abba kuwa har yayi kan stair.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now