Page 42

297 17 4
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 42

By
*MARYAM S INDABAWA*
Hakuri da Juriyya Online ✍
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Stair ya nufa yana tasbihi har ya karasa kofar dakin Mami. Knocking yayi ta bashi izinin shiga sannan ya shiga. Tana zaune a gefen gadon ta ya karasa ya zauna akan center carpet din dakin sannan ya zame hular kansa. Hannun ta ta daura akan sa tai masa addu'a sannan ta dago tana kallon sa.
"Ina kwana Mami?"

"Lafiya lou! Ya kake ya aiki?"
"Alhamdulillah!"

"Ya Ummin naka da me jiki?"
"Da sauki!"

"Masha Allah!"
Kai yai kasa dashi sannan yace
"Mami ni zan tafi!"

"To Allah tsare yai albarka ya kare a kula a kiyaye aiki da neman halak duk inda haram take ka guje ta dan abinda zata kara maka,  sharri ne tare da ita halak kuwa duk kan kantar ta zaka same ta da albarka a cikin ta. Allah tsare!"
"Amin Mami nagode! Sai na dawo!"
Sannan ya mike Mami ma ta mike tare suka fito suka samu Mamah a falo ya nufi kofa ita kuma Mami tayi sashen Abbi.

Daga nan parking lot ɗinsu mai ɗan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau. Ya nufa,  Wasu tsala-tsalan motocine da a ƙalla sun kai su takwas sai sheƙi sukeyi. Wajen wacce zai shiga ya nufa blue black ce sai sheki take ya nufi ta ya sa hannu zai bude Farouk dake cike ya bude kallon sa ya tsaya.

Ya fito yana murmushi yace
"Na jira ka fito mu tafi ne!"
Ya bashi hanya ya shiga ya rufe masa kofa. Glass yai kasa dashi wanda yake tint yace
"Me kake so?"

Kai ya shafa yace
"Ba komai Hamma!"
"Kai dai!"

"Please Hamma motar ka dayar nan nake so tinda naga ka daina hawan ta!"
"Wacce a ciki?"

"Red colour din!"
"Ok key din yana clinic in naje zan dauko maka yayi maka?"
"Yes Hamma na godiya nake Allah saka da alheri ya kara budi!"

"Amin! Ka kiyaye kaji abinda Abbi dai ya fada Allah tsare!"
"Amin Hamma Allah tsare hanya!"

Ya daga kai yana fadin
"Amin!"
Sannan ya tada motar Farouk sai da yaga ya fita sannan ya nufi motar sa ya shiga yabi bayan sa.

Cikin nutsuwa yake driving yana yi yana tsabihi da addu'ar tsari a haka har ya karasa babban asibitin da yake aiki. A cikin rumfar adana motor da aka rubuta Dr Aliyu Suleiman a samanta anan yai parking sai da ya dauki minti sama da goma sanna ya bude murfin motar, a hankali ya zuro ƙafafunshi ya fito. Wani massenger sa ne ya karaso da sauri car key din ya bashi ya bude ya dauko system din sa da wayoyin sa. Cikin nutsuwa ya fara taku yana ratsowa cikin farfajiyar Hospital ɗin.

A nutse yake tafiya massenger sa na take masa baya har suka shiga cikin asibitin gaba ɗaya Nurses ɗin dake ƙoƙarin fitowa sunyi maza suka koma baya, tare da rusunawa suka haɗa baki wurin cewa.
"Barka da hantsi Dr A.S"
Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, tafiya mai tsayi yayi ya shiga  cikin wani ɗan corridor dake gefen daman sa  wanda shi zai sadashi da office din sa.

Yana zuwa bakin office din ya tsaya da sauri messenger dake biye dashi rike da jakar system din sa ya karaso ya bude masa. Da Sallama hadi da bismillah ya saka kafar sa ta dama cikin office din. Ajiyan zuciya yaja a hankali saboda ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta, Office din ya hadu iya haduwa kai ba ka ce a cikin asibiti kake ba dan tsaruwa da kyau da tsabtar sa.

Yana shiga Office dinshi, ya nufi kan katon table din dake gaban sa wanda ya ke katon gaske zama yayi messenger ya ajiye masa bag da wayoyin sa. Budewa yayi ya dauko ta ya kunna ya fara aikin daya kawoshi. Bayan minti na ya dago ya kalli agogon hannun sa har goma da rabi, messenger dake tsaye yace
"Hassan Abubakar shine first call him!"
Ya juya ya fita ba a jima ba patient din ya shigo cikin mutunci da girmamawa suka gaisa sannan ya duba shi ya sallame shi.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now