Page 84

490 24 4
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 84

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Kan su shiga gida har Haidar yai bacci suna zuwa ta kai shi d'aki ta canja masa kaya tare da masa addu'a, bandaki ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci, tana shirin kwanciyya ya shigo yana fadin
"Me nake gani haka?"

Ya iso ya dauke ta yana fadin
"Wai me yake damun ki ne?"
Ya fada yana ajiye ta akan gado, idon ta ne ya kawo ruwa, yace
"Ba zan taba kishi da Yaa Haidar ba Maryam, amman wallahi in na ganki a damuwar ni kadai nasan me nake ji dan Allah ki fada min da me kike tina shi ni kuma in maye gurbin hakan."

Murmushi ta saki tace
"Yaya na i love u the way u re, a kullum in zan tuna da Yaa Haidar sai na tina da kai dan sanadin ka na ke raye cikin jin dadi, in Yaa Haidar ya kula dani a baya yanzu kai ke kulawa dani, in Yaa Haidar ya soni a baya yanzu kai ke so na, in na kasance da Yaa Haidar a da yanzu da kai nake tare, ka mayewa Haidar gurbin sa, dan haka ka sani kai kadai ke zuciya ta da tunani na dole na tina Yaa Haidar Yaya amman ba haka zai sa nace bana son ka ba, ina son ka, kuma in na tuna shin addu'a nake masa, please Yaya kada kai fushi ko kaji haushin sa akan haka, yau Haidar karami ya tina min da Abbin sa, kuma na kara sauke mata wani nauyi dake kaina, kai min alfarmar ko ya'ya muka haifa zamu sa musu soyayyar Yaa Haidar, dan suna masa addu'a saboda abinda yake so kenan."

"Ya'yan mu na Yaa Haidar ne Maryam, kamar yadda Haidar yake nima 'dan na, dan haka na miki wannan alfarmar kuma nima zan kasance cikin masa addu'a Allah masa rahma ya kyautata namu zuwan."
"Amin My honey."
Ta fada tana shigewa jikin sa.

Rumgume ta yayi tsam a jikin sa kamar zai mai data cikin sa yace
"In nace nafi Yaa Haidar son ki zaki yadda?"
Kai ta dago tana kallon cikin idon sa, wanda ba abinda take gani sai tsantsar son ta, ido ta lumshe tace
"Ba Yaa Haidar Yaya dole kai ne me sona a yanzu fiye da kowa, ni na isa na karyata Yaya na bayan baka taba batan rai ba kullum kula kake bani kamar 'yar sa, abinda Innan Abbi na ta fada kenan nake ganin ta fada ne kawai cewar ina dacen masoya a lokacin ban san da gaske take ba sai a yanzu nake gaskatawa, hakika nagode Allah da ya jarrabcen ya kuma bani ikon cinye jarabawar har yai min canji da mafi alheri, Allah ya jikan Yaa Haidar, ya barni da kai har a aljanna Yaa Haidar, ina son ka ina kaunar ka kuma na yadda da duk soyayyar ka."

Idon ta cikin nasa take maganar nan wanda yaji son ta da kaunar ta na kara ninkuwa a cikin zuciyar sa, goshin sa ya hade da nata inda hancin su ke gugar juna, ya kara yin kasa da fuskar sa bakin su ya hade da na juna, wani irin kiss yake bata mai ma'anoni da manufa da yawa, a haka ya cigaba da romancing nata tare da faranta ran juna su kamar ba ita ba ta zage suna shan soyayyar su.

*
Washe gari da safe, sam sun manta da Haidar baccin su suka hau yi, wanda Haidar ya farka wajen takwas, da kan sa yai brush ya fito falo, ya kunna kayan kallo ya kai mbc 3 ya zauna yana kallon cartoon, da yaji yunwa ya shiga kitchen ya nufi store ya dauko fresh yoo da biskit ya dawo ya zauna yaci ya koshi daga haka ya cigaba da kallon sa, wanda bai san lokacin da bacci ya dauke shi ba, sai karfe goma suka farka, wanka sukai suka shirya sai da ta zata bude kofa ta tuno da Haidar karami da sauri ta fita ana fadin
"Honey mun manta da Haidar."

Ya fito da sauri yana fadin
"Kuma ya tashi?"
Suka fita a falo suka same shi yana bacci gefen sa robar fresh yoo da ledar biskit din da yaci, karasawa Yaa Haidar yayi ya dago Haidar yana rumgumewa Maryam ta nufi kitchen dan hada musu breakfast. Sai da ta gama suka zo ta je ta karai masa brush suka karya, a jikin su ya yini daga ya fada jikin wannan sai na wannan, da yamma Yaa Haidar ya dauke su suka je park, wanda daga can suka shige wani reaturant acan sukai dinner daga nan store sukaje sukai shopping sannan suka koma gida, haka the next day ma da yamma suka fita zaga gari sai dare suka dawo.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now