💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 89-90
*Epilogue*By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*JAN HANKALI*
*BAN YADDA WANI KO WATA YA COPY KO YA JUYA MIN LABARI, KO YA KARANTA MIN A KO WANNE CHANNEL BA TARE DA IZINI NA BA. NAGODE*6 years later
Masha Allah rayuwace mai dad'i da zaman lafiya suke ciki gaba daya familyn kowa sai sam barka duk da wani lokacin akwai wasu kalubale da Allah kan jarabci bawa amman Alhamdulillah komai yana zuwan musu da sauki baya fin karfin su saboda sun rike Allah da bauta masa ba dare ba rana haka nan sun kyautatawa iyayen su da yan uwan su, a tsakanin su baka taba jin wani fada ko sabani kowa yana son dan uwan sa duk inda suka hadu zaka kamar su cinye junan su ya'yan na da zumunci da son junan su.Cikin wannan shekarun Aliyu ya kara zama babban mutum dan har asibitin sa ya bude wanda yake aiki tare da matar sa duk da ita bata fiya fita aiki ba bama da ta cigaba da karatu har ta zama babbar likitan mata wanda ake ji da ita ba a iya Abuja ba har a Nigeria baki daya dan ma ba aiki take sosai ba in kaga ta shiga asibiti to an samu masu bukatar taimakon ta sosai wanda dole sai ita sannan take shiga asibiti ta. Sosai suka samu cigaba daga asibitin nasu dan yadda suke da kwararun likitoci.
A cikin wadan nan shekarun Maryam ta sake haihuwar Baby girl sau biyu, ta farko aka saka mata suna Maryam din suke kiran ta da Islam sai ta biyun ta aka saka mata sunan Mami suke kiran ta da Sajida, Najwa ma ya'yan ta uku maza biyu mace daya sai Aisha ma ya'yan ta uku mata biyu namiji daya, Rukayya ya'yan ta biyu mace da namiji inda namijin yaci suna Yaa Haidar, Anty Nusaiba matar Yaya Abubakar ma ta sake haihuwar ya'ya biyu duk maza, Yaa Farouk da Jawahir ma ya'yan su biyu mace da namiji daya sunan Mama ya saka mata sai namijin yasa suna Abba Usman.
*
Zaune take a falon Ummi sanye cikin wata atamfa fara ce wacce akai mata ado da blue and orange kala dinkin doguwar riga ne wanda yaji stone tai kyau ta sha dauri ga sakar gold wuya da hannun ta, Maryam ta kara kyau ta ciko ba rama a jikin ta ta kara haske kana ganin ta kasan kwanciyyar hankali ta zauna mata, Ummi ce ke zaune a gefen ta tana kallon tana murmushi, yadda take magana kamar zatai kuka, tana fadin
"Dan Allah Ummi ki sa baki yaki ya barni naje sam kuma Ummi kusan shekara fa rabo na da Kano, in ba irin hakan ce ta faru fa bai fiya bari na naje ba."
Tai maganar cike da shagwaba wacce har yanzu taki ta barta.Haidar, da kannen sa Humaira, Islam, da Sajida, suka shigo a tare cikin shiga iri daya, dogayen riguna ne a jikin su, red and white kala wanda kansu an musu kitso jelar ta fito ta kasan hular dake kan su iri daya hatta takalmin su iri daya ne, in kaga Humaira da Islam sai ka zata yan biyu ne dan basu da nesa sosai, Sajida ce yar shekara uku, Haidar ma wando ne jeans da har riga a jikin sa, sai takamlmi baki yaran kyawawa dasu abin sha'awa dukkan su leda ce a hannun su. Sajida ce ta nufi wajen Maryam ta hau an cinyar ta tana fadi
"Momy kinga abinda Dady ya siyo mana."Janye ta tayi dan ita so take taji abinda Ummi zata fada dan tana son taje Kano ta hadu da yan uwan ta, wanda Matar Yaa Abdullah ce ta haihu take son zuwa sunan.
"Daughter ki bar damuwa zan masa magana shikenan?"Kai ta gyada tana sakin murmushi, Sajida ta makale mata daukar ta tayi tana fadin
"Menene Sajida?"
Ta rumgume yarinyar da take kama da ita sak, dan Haidar kama yake da Abbin sa haka Humaira da Islam kamar su daya da Abbin su, Sajidar ce tayo ta gaba daya kamar ita haka su Ammi ke fadi. Yaa Haidar ne ya shigo dakin da sallama cikin shiga ta alfarma sai tashin kamshi yake, amsawa suka ya zauna akan kujera yana fadin
"Ku fito mu tafi gida."
Sajida, Maryam ta ajiye tai sama dan hado kayan su, da kallo ya bita sannan ya kalli Ummi yace
"Ummi yar taki sai rigima take ji fa."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...