Page 68

348 17 3
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 68

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Yesterday 10:00pm*
At Auwal House.
Abinda ya faru jiya bayan dawowar su daga dinner, wanda lokacin goman dare, yana shigowa gidan aka fada masa Dady na neman sa wannan yasa ya nufi bangaren mahafin nasa, zaune yaga Dad dinsa Ammin sa na safa da marwa wanda hakan ya nuna akwai wani abu da ya faru, da kallo suka bishi har ya shiga ya zauna.

Kansa a 'kansa yace
"Dad lafiya?"
Kan Dad yai magana Ammi ta hau fada
"Kana da hankali kuwa?"

Dagowa yayi ta koma ta zauna tace
"Ashe baka da hankali ace kana neman yarinyar da ba a sam asalin ta ba karuwa...."
Har tsakar kansa yaji wannan mummunar kalmar cikin damuwa ya dago ya kalli Ammi yace
"Ammi ba karuwa bace sam...."

"Rufe min baki, Khalifa in har ni na haife ka to ka sani ba kai ba waccan yarinyar ace har dan shege ne da ita amman kake son ta a haka? Shin asirce ka tayi, amman ka bani kunya to wallahi kaji na rantse ba zaka auro mana karuwa a cikin zuri'ar mu ba."
Rarrafawa yayi wajen Ammi yana fadin
"Ammi ba haka bane ku tsaya nai muku bayani."

Ido Ammi ta zaro tace
"Ashe kama sani har so kake ka kare ta."
Ganin Ammi ba zata saurare shi ba ya karasa wajen Dad hawaye na zubo masa yace
"Dad dan Allah ka saurare ni wallahi ba haka bane, Maryam yarinya ce mai ladabi da biyayya ga hankali da nutsuwa..."

Hannu Dad ya daga masa yace
"Khalifa ka makaro ba zan saurare ka ba sam, meyasa tin tini baka fada mana ba, duk matan garin nan ka rasa wacce kake so sa wacce ba asan asalin ta ba, a gaskiya ba zan iya wannan abun ba kayi hakuri amman tabbas bakai ba auren wannan yarinyar."
A razane Muhammad ya dago yana girgiza kai, Dad ya mike yai daki kallon Ammi yayi ya rarrafa wejen ta ta mike tana fadin
"In ka sake kai min wannan magana akan wannan yarinyar tabbas ranka zai baci."

Tana fada ta mike ta bar wajen, kai ya hade da gwiwa yafi minti uku sannan ya mike ya nufi dakin Dad a zaune ya same shi ya shiga yace
"Dad dan Allah kayi hakuri wallahi ina son Maryam ita ce rayuwa ta in kuka hanani auren Maryam wallahi mutuwa zanyi....."

"Sai dai ka mutu Khalifa ba zan taba yadda d'ana ya auri wacce bata da asali ba dan azo ana mana yarfe kasan ni dan siyasa ba abinda bakai tsamani bama zakaji dan haka ba zan yadda ba kayi hakuri kawai."
"Dad amman ka duba a yanzu naje musu da zancen nan abun ba zai musu dadi ba sam..."

Kallon sa Dad yayi yace
"Maganin su da basu sanar mana ba."
"Wallahi Dad sun fada min kuma sunce na fada muku..."

"Me ya hana ka fada manan?"
Shiru yayi, Dad yace
"Maganin marar neman shawara da fadar gaskiya da tin can ka fada haka ba zai faru ba zamu taka maka burki wallahi Khalifa ban yadda ka auri wannan yarinyar ba dan haka tashi ba bani waje"
Ya fada yana nuna masa kofa, yadda yai maganar cikin bacin rai yasa Muhammad tashi ya fita da sauri, yana fita ya shiga mota ya bar gidan, gidan su Maryam ya isa wanda ya kira Abba ya sanar masa anan akai wannan abun.

*
Yadda yaga rana haka yaga dare, sam ko bacci bayaji haka da safe ko yunwa bai ji ba bare yaci abinci yana dawowa daga masallaci ya nufi sashen Dad, wanda shi har ya shige anan falo ya zauna yana jiran fitowar sa, har karfe goma sannan Ammi ta shigo tana ganin sa ta dauke kai ta nufi sashen Dad da sauri ya sha gaban ta dago tana kallon sa idon sa cike da hawaye yace
"Ammi ke uwa tace dan Allah kada ku hukunta ni ta wannan hanyar wallahi ina son Maryam Ammi dan Allah...."

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now