💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 71By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Kai ta girgiza kawai, Yaya Ummulkairi da Zainab dake bakin kofa suka shigo suka saka yar uwar tasu a tsakiya, Yaya Ummulkairi wacce take babba a cikin su tace
"In kika duba rayuwar ki ta baya tin daga haihuwa har ranar graduatin din ki me zaki ce ga Allah? Na tabbata godiya ce saboda a lokacin baki fuskanci ko wanne kalubale ba, rayuwa kike cikin gata da soyayya, komai naki sucess. To a haka bawa zai ci gaba da tafiya babu jarabawar rayuwa? A'a! In har Allah bai jarabtar ka ba ma to ka tuntubi imanin ka, amman ke kin tashi cikin gata sai ga wannan jarabar ta rasa miji a gareki wanda shine hope din ki, shine farin cikin, bayan nan ya dauke miki magana sannan ya jarabce ki da abubuwa masu yawa har kika bar gida kikaje wani wajen kikai rayuwa mai tsayi wanda suka rike ki da amana a karshe sai ya baki d'a duk da Allah ya dauke miki uban shi sai ya baki magajin sa, wanda gashi nan kikai masa takwara shin wannan ba wata ni'ima bace, bayan kin bar gida kinyi rayuwa mai kyau a wani waje wannan ba ni'ima bace a karshe rashin ahalin ki na asali duk da kin samu asalin su yasa ba a aure ki ba amman wadanan mutane masu karamci suka bawa dansu mafi soyuwa a gare su wannan ba ni'ima bace, wanda zai rufa miki asiri kinsan me, a yau da kika dawo wallahi ba kowa zai yadda da ina kika je ba wasu cewa zasuyi wayon karuwancu da makamantansu kika je amman ganin ki da miji zai cire wanna aransu dan haka abinda zance miki rayuwa juyi juyi ce yau fari gobe baki ki godewa Allah kuma ki amshi jarabarwar ki kinji.""Kullum a cikin gode masa nake Yaya Ummu, amman yau zuwa na gida ya tadan hankali ji nake tamkar yau na rasa Yaa Haidar abubuwa da dama nake tunawa na rayuwar mu Yaya Ummu, kunsan wanenen Yaa Haidar kuwa?"
Ta fada tana binsu da kallo, murmushi sukai dan sun sanshi farin sani tinda tin ba a haife ta ba sukai rayuwa."Ku tayani da addu'a kawai amman zuciya ta ji nake tamkar zata tarwatse da gaske dai na rasa Yaa Haidar, da gaske ba zan sake ganin sa ba ya tafi inda ba a dawowa."
Ta fada taba kife kanta a jikin Haidar dake ta kallon picture Abban sa yana jin son sa a cikin zuciyar sa, hawayen da yaji na Addan sa yasa ya juyo yace
"Adda kalli Abbi na murnushi yace ba kyau kuka ki daina shima yace ki daina."Yaa Alkasim ne ya shigo yace
"Tabbas Haidar kayi gaskiya abinda Abbin ka yafi tsana yaga Maryam tanayi kenan kuka, in har zai ga Maryam na kuka to tabbas hankalin sai yayi dubu ya tashi ba zai taba samun nutsuwa ba har sai yaga tana murmushi amman yau bayan idon sa ba zata masa wannan alfarmar ba wanda da yana nan yanzu tasan bashi da kwanciyyar hankali, ki godewa Allah Maryam da komai na rayuwar ki Haidar ya tafi ga wani ya dawo, kin tabbata *Matar Haidar* dan Allah ki kwantar da hankalin ki, ki daina kukan nan bana so sam bana son kukan ki."Kallon yan uwan nata take ganin yadda duk suka shiga damuwa dan sunganta tana kuka, murnushi ta kirkiro tana goge hawayen idon ta hadi da fadin
"Insha Allahu ba za ku sake ganin hawayena ba da damuwa ta ba na daina kuma ku daina damuwa kalle ku dukka akai na kun shiga damuwa in kai hakkin ku ina, ni ma na daina insha Allahu kuna tayani da addu'a ina fatan kuna saka Yaa Haidar a addu'ar ku?"Kai suka gyada tace
"Nagode Allah saka muka da gidan Aljanna Allah ya bar min ku."
Suka amsa da Amin. Yaa Alkasim ya kamo ta yace
"Taso muje muci abinci."
Ya dauki Haidar.A parlour ta tarar dasu Yaa Muhammad suna zaune suna jiran fitowar ta, Rumgume juna sukayi itada Anty Rabi'a cikin jindadi kafin daga bisani suka nufi Dining dukkansu, Ammi duk wani abu da tasan Maryam naso shi aka dafa.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...