Page 88

528 25 7
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 88

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Washe gari daurin aure tare suka tafi ya ajiye ta a gida ya nufi wajen daurin auren, a gida ta samu su Najwa da Yaa Hanna dan duk kwana sukai, bata dade da zuwa ba Aisha da Rukayya suka karaso, Basma da taga Maryam ta rumgume ta, Maryam ta ture ta tace
"Ni ba ruwa na dake daki 'kaki zuwa ki kwanan mana"

"Kai Anty ance gidan ku ai bai zama."
Basma ta fada, Najwa, Maryam ta kalla ta harara tace
"Nagode shiyasa ai Rukayya ma taki tazo Allah ya saka min tinda abinda kuke min kenan."

"Ba wani nan Rukayya ai ke shaida ce da muka ce zamuje ba hana mu yayi ba."
Najwa ta fada tana mai da tambayar ga Rukkaya

"Abu kusan shekara dan iskanci."
Maryam ta fada, Aisha ta dafa ta tace
"Ke rabu dasu kada su zo din."

Kamar zatai kuka tace
"Amman ai ba dadi ko?"
Dariya Aisha tayi, dan Maryam in abun yazo akwai shagwaba ji akan dan wannan abun zatai kuka, Anty Hanna da ke jin su tace
"To ba sai suyi tayi ba, ai ni abinda nake so kenan, Yaya yana kular min dake."

Kallon Anty Hannah suke ta dan harare su tace
"Taso kinji kanwata in baki wani sirrin da zaki kara rikita Yaya."
Ta kamo hannunta suka mike, Najwa da Aisha suka ce
"Haba Anty muma muna so."

"Ba wanda zan fadawa tinda tsiya kuke mata."
Sukai sama abinsu acan ma lallashin ta tayi, tare da nuna mata yadda zata cigaba da kula da mijin ta, haka Yaa Asiya da Bilkisu suka shigo suka same ta suka zauna suna tattaunawa da hirar su. Can sai gasu Najwa nan da Aisha gaba dayan su.

Sai yamma da za ai Walima Tasleem ta zo gidan cikin wani material wanda akai masa wani banzan dinki, a kasa ta zauna wajen da aka saka kujeru tana kallon kowa d'ai d'ai, Maryam kuwa na sama Najwa ta tsare ta wai dole ai mata kwalliya inda ake mata amman duk ta gaji, sai da aka gama gaba dayan su sunyi anko cikin wata atamfa da sukai anko sosai sukai kyau kamar a debe su  gudu, Najwa, Anty Hanna, Asiya, Bilkisu, Aisha, Rukky, da ita, kasa suka sauko suka bar Maryam wajen Haidar dake mata rigima ta dauko masa lemo, suka nufi store ta dauko masa ta bashi ya amsa yana fadin
"Thank you Adda nah."
Yai mata kiss a kumatu yai sama wajen Ummi.

Ta mike tana murmushi tare da fara neman layin Aliyu dan basuyi waya ba tin dazu, yana cikin mutane yaga kiran dan sunje reception ya fito yace
"Ya dai Baby?"

"Ina ka shiga ina ta missing naka."
"In zo mu tafi gida?"

"Kai Yaya sai dare."
"Yanzu zamu karaso gidan ai."

"Ohk sai kunzo."
"Bye muahh."
Ta kashe wayar ta fita, tana fita ta karasa wajen su Najwa da suke zazzaune, Tasleem na gefen Najwa Maryam ta zauna a gefe Aisha, Aisha tace
"Uhmm an gama soyayyar?"

"Ina ai bazamu taba daina soyayya ba ni da Honey."
Hannu Najwa ta tafa tace
"Rashin kunya su Anty Hanna suka koya miki kenan ko?"

Baki ta murguda tace
"A gun mijin nawa ne ya zama rashin kunya."
Sukai dariya suna hira abinsu.

Jawahir ce ta kira ta bayan ta dauka tace
"Uhmm ni daman nasan yau ba zan ganki ba please dear kinsan bani da wata 'kawa bayan ke dan Allah kizo kinji."

"To yanzu ya zanyi Yaya bai dawo ba."
"Zan kira Baby sai ya fada masa please Dear."

"Ok kira shi nima zan kira shi yanzu sai mu taho dasu Najwa."
"Yauwah dear."
Ta kashe wayar, ta fara neman Yaa Aliyu, yana dauka ta sakar masa shagwaba yace
"Ya dai Baby."

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now