💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 25By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Dafata Yaya Fadima tayi tace
"Dan Allah kibar kukan nan haka menene kuma ya faru?""Dan Allah kicewa Ammi akai ni wajen Yaa Haidar, in ba mai kaini ni zan tafi dan Allah ki rokar min ita."
"To naji! Ki bar kukan ko a haka zakije masa kina kuka ki dada tada masa hankali.""Wai tayaya kuke son na daina kukan nan nifa ban san yana fitowa ba nakasa rike shi dan Allah kije ki mata magana."
Mikewa tayi tace
"Toh!"Ta tafi dakin Ammi. Dawowar Ammi daga gidan Mamah kenan gidan da har ya fara cika da mutane ga na biki ga yan uwa, da makwabta. Mamah na zaune a gefen Aliyu sai addu'a take masa Abbah da Abbi da Alkasim da baya uhm bare Uhm uhm duk suna zaune. A cikin gida kuwa sai kuka ake. Zuwan Ammi ma dan Abbi yace tazo ta kira Maryam ne suyi sallama wannan yasa ta mike ta nufi gida shine suka hadu da Fadima.
Tana ganin ta tace
"Daman wajen ki zani!"
"Meyafaru ba dai taji ba?""Bata ji ba dan so take kisa a kai ta wajen Yaa Haidar."
"Ikon Allah! Tayaya zan sanar mata ne. Bari naje dai."
Ta nufi dakin Yaya Fadima na bin ta a baya.Tana shiga Maryam ta rarrafo wajen Ammi ta kama kafar ta tace
"Ammi dan Allah kada kice min A'ah!"
Kamo ta Ammi tayi tana boye hawayen idon ta tace
"Ba zance ba, taso muje!"Ta kamota ta mike ta lafe a jikin Ammi dan yadda take ganin bibbiyu. Ammi ta kama ta tace
"Menene?"
"Jiri Ammi, biyu biyu nake gani Ammi!""To rufe idon ki kinji!"
Rufe idon tai Ammi ta lattafe ta suka fita a dakin. Suna fita Fadima da Aisha suka fashe da kuka. Fadima ce ta mike tace
"Taso muje."
Suka bi bayan su.Har suka fita compound idon ta a rufe yake sai da suka kusa kofar gidan su Aliyu ta bude ido. Mutanen da ta gani ne ya bata tsoro tace
"Ammi me ya faru?""Ba komai."
"Waye zai kaini gun Yaa Haidar?""An sallamo shi fa yana gida "
"Ammi da gaske? Yaji sauki ko?"
Kai Ammi ta gyada tana kama ta suka shiga gidan yadda taga compound din a cike wasu na kuka wasu na jimami yasa gaban ta ya kara yankewa ya fadi. Tunanin ta ya gushe dan ta kasa gane mutanen menene suka zo musu haka. Sai kace jiya ranar bikin su da daurin auren su.Kama ta tayi suka nufi bangaren Aliyu, yan tsakar gidan kuwa sai nuna ta suke da hannu suna fadin
"Ga matar tasa. Allah sarki!""Ai fa jiya jiya aka daura aure yau ba miji wannan wane irin tashin hankali ne."
Haka suke ta magana kala kala dai.Suna shiga falon Aliyu gaban Maryam ya kara faduwa har sai da ta durkusa ta dafe kirjin ta. Ammi ta durkusa tace
"Menene?"
"Ammi kirjina, sai faduwa yake.""Kina fadin Innalillahi wainna illahir rajiun kinji?"
Kai ta gyada ta fara ambaton haka a zuciyar ta. Ammi ta dago ta suka shiga. Abbah da Abbi ta fara gani sai Yaa Alkasim da Mamah daga kan da zatai ta gano Mutum kwance rufe da farin abu da sauri ta juya ta kamo hannun Ammi tana nuna mata abun hannunta na rawa bakin ta ma rawa yake ta kasa furta komai, sai nuna abun da take jikin ta na karkarwa.Tin kafin Ammi tai magana ta sulale zata fadi kasa da sauri Ammi takamo ta tana fadin
"Innalillahi wainna illahir rajiun!"
Abbi ya mike da sauri yayo wajen su yana fadin
"Me ya faru?""Suma tayi ko?"
Ya dago ta ya karasa dakin da ita. Ammi ta dauko ruwa a firij ta shafa mata a fuska shiru bata farka ba, kara zuba mata tayi nan ma haka ruwan ta tuttula mata a kanta wannan yasa taja wata doguwar ajiyar zuciya wanda yasa kowa fadin
"Alhamdulillah!"Kusan minti biyar kenan da ta farfado amma ta kasa bude idonta. Tsoro take ta bude za ta sake ganin abinda ta gani, wannan shi ake kira mummunan gani.
"Shin waye ma a kwance a cikin likafani?
Tai tambayar a zuciya da sauri ta bude ido dan gwara ta gama sanin wanene ta tabbata dai ba Yaa Haidar bane. Ina Yaa Haidar ba zai mutu ya barta ba.Kasa-kasa take jin muryar su Mamah, Ammi suna fadin
"Tana numfashi."
Tofi taji ana mata a hankali ta bude idon ta. Abbi ta gani yana mata tofi. Idonta ta mayar kan gawar dake kwance sambal nuni tai musu da ita dan su fada mata waye a ciki amman duk suka gaza bata amsa.A hankali ta mike zaune ta dafe kai dake barazanar rabewa gida biyu, kallon gawar ta karayi sannan ta mike tsaye Ammi ta kamo ta cire hannun Ammi tayi ta tafi gaban gawar a dai dai kan sa ta durkusa jikinta na rawa ido na zubar da hawaye ta mika hannu ta dage Likafanin.....
Fuskar Yaa Haidar ce wacce yake tai mata murmushi ta bayyana, bata san lokacin da zauna akasa ba ta tsurawa gawar ido ba abinda yake motsi a jikin ta har numfashin ta daukewa yayi cak idon ta na kafe akan sa kawai. Ammi ce ta gane ta shiga shock wannan yasa ta karasa kusa da ita da sauri tana zuwa ta taba ta ai take ta bingire a jikin Ammi.
Yaa Muhammad ne ya miko ruwan dazu dan a shafa mata amman ko gezau, har juye mata akai amman sam bata farka ba kuma ko alamun rai babu a jikin ta. Ammi ce tace
"Itama fa ta mutu!"Da sauri Mamah ta karaso tana fadin
"Mun shiga uku, Yaa Allah kada ka jarabce mu da rasa yara biyu a lokaci daya Allah mun tuba in wani laifi mukai maka."Abbi ne ya karaso ya duba kai ya girgiza yace
"Ai kuwa kamar itama ta rasu!"
Kuka Ammi da Mamah suka saka. Ammi ta rumgume gawar Maryam tana jijjigawa..........~Please ku karata kasan nan~
*_Ban taba zato ba, ban zata haka ba*__Jiya naji dadi sosai dan ba a taba yin comment kamar jiya ba, daga facebook har whatsapp naga abinda akai ta tattaunawa shine MATAR HAIDAR abun ya bani nishadi duk da akwai taba zuciya, ba yau na fara rubutu ba, ba yau kuma in nayi wasu suke cewa sun daina karantawa ba dan ban musu yadda suke so ba, duk abinda kuka gani a littafin nan na rubuta shi sama da watanni bawai ko sama da haka kafin na rubutawa kuwa labarin yana kaina sama da shekara biyu sai a yanzu dai Allah yayi lokacin sa, ba dan nishadi kawai nake rubutu ba ina rubutu dan fadakarwa da zaburarwa so, ni akwai abinda nake son na isar am not after all this love in zakuyi duba irin wannan deep love din bai fiya kaiwa inda ake so ba, kuma ko a gaske muna son mutane Allah ke daukewa, masu cewa Maryam tayi wauta jarabawa ce Allah ya riga ya rubuta, mu bamu san irin wacce Allah zai jarabce mu da ita ba, fatan mu dai Allah ya bamu ikon cinye tamu kalar jarabawar, itama bamu san tukuwicin da Allah zai mata ba, kila Yaa Haidar ba alheri bane a gareta ba shiyasa ya dauke shi, kuma rabon wani a ko da yaushe yakan iya kisa dan haka kuyi shiru kawai ku dai...._
*Hakika naga kauna sosai Allahu ya bar zumunci, masu kuka kuyi hakuri mutuwa nasan ko ta wasa ce babu dadi nima nai kukan kuma duk lokacin da na karanta abun mutuwa yana kara kashen jiki da kara min imani wanda yake kara min kusanci ga Allah, abinda nake so daku kuma kenan. Allah jikan musulmai yasa muyi kyakyawa karshe yasa mu cika da kyau da imani*
*Maryam Suleiman*
*Antty*
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...