Page 69

384 23 6
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 69

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Ya amshe ta yai dakin sa da ita akan gado ya kwantar da ita yana fadin
"Meya faru?"
Kuka kawai Najwa da Aisha suke sun kasai masa bayani, duk kokarin sa na ya samu nunfashin ta ya dawo ya kasa wannan yasa ya kira Farouk ya fito da mota, shi kuma ya fita da ita a hannun sa, asibiti suka nufa Ummi da su Najwa uka mara musu baya, office din sa ya shiga da ita ya kwantar akan gadon marar lafiya, tin kan ya karaso yaga kira likita da nurses dan haka a bakin office din ya same su, yana ajiye ta suka rufa akan ta suna kokarin taimaka mata sai da numfashin ta ya dawo sannan sukai mata allurai, take ta fara bacci.

Aliyu dake tsaye a gefe yana kallon yadda suka taimaka mata take numfashi har tai bacci tana maganganu kasa kasa wanda ba ajin me take fada ya kalli Dr Yasmeen yace
"Me kika gano matsalar ta?"
"BP ta ya hau Dr and zuciyar ta tana kara rauni in tana cigaba da saka damuwa zata iya rasa rayuwar ta dan jijiyoyin sunyi rauni sosai kuma saka damuwar ya haifar mata, bama wannan ba a gaskiya yarinyar nan tai kankanta da wadan nan matsalolin ga hawan jini, ga ciwon zuciya, Dr tana bukatar kulawa da lallashi please a bata kulawar da ta dace."

Yana jingine da bango hannun sa harde a kirjin sa yake sauraron ta, har ta gama yai mata godiya ta juya ta fita ido ya lumshe a hankali ya sauke akan Maryam dake bacci, abinda ya fara guje mata kenan heart broke domin yasan ba ko wanne ahali ne zasu amshe ta ba yasan da haka amman a time din ta kasa fahimta su Ummi ma haka, in ta shine Maryam ba zata taba soyayya da wani a waje da zai cutar da ita ba su suka fi sanin matsalar ta dan haka su zasu iya zama da ita da kula da ita.  Gashi nan yanzu tana neman halaka kan ta kenan tana son Muhammad har haka ta kasa hakura dashi yau in ya mutu wa gari ya waya, su dan shi gashi can an daura masa aure nan da wani lokaci zai manta da ita su kuwa da Haidar har abada ba zasu manta da ita ba.

Ido ya kara lumshewa yana mai fadin
"In har aure nane bakya so Maryam zan sauwake miki ba zan taba takura miki zama da wanda bakya so ba har hakan ya kara jefa rayuwar ki cikin hatsari."

Fita yai dakin Ummi ta karaso tana fadin
"Ya dai Aliyu?"
Dakin ya nuna musu yace
"Bacci take me ta gani yasata a  wannan halin?"

Najwa ta saki kuka tace
"Ni na rasa menene dan mune dai a dakin daga Aisha ta kira sunan ta ta dago shikenan ta kura mata ido ta zube a wajen."

"Ina Aishan?"
Aliyu ya fada yana kallon ta waige waige ta fara sai ga Aisha nan ta taho daga wata hanya bayan ta wani namiji na biye da ita da kallo suka bisu har suka karaso, namijin shi yai karfin halin mikawa Aliyu hannu suka gaisa, Aisha tace
"Nan aka shiga da ita."

Da mamaki Ummi da Aliyu ke kallon ta dan so suke suji wa aka shiga da ita. Alkasim ya dago ya kalli Aliyu a karo na biyu yace
"Sunana Alkasim Jabeer ni dan garin kano ne aiki ya kawo ni garin Abuja ga mai daki na sunan ta Aisha, mu makwabtan Najwa ne wanda bamu jima da dawowa daga Canada ba muka tadda anyi auren ta, matata tazo bikin yar uwar Najwa inda yanzu ta kirani take shaidamin taga Maryam dan Allah da gaske Maryam ce a dakin nan dan ina mamakin ta ina ta ganta ban sani ba ko gezo ta farai mata dan kwanaki tazo tana fada min tana mafarkin Maryam tana fada mata tana kusa da ita dan Allah da gaske Maryam ce a dakin nan?"

Ummi da Haidar kallon sa suka tsaya sama da shekara biyar basu taba ganin wanda yace yasan Maryam ba sai a yau kenan da gaske wadan nan sun san ta ko kuwa? Aliyu ne yai karfin halin fadin
"Tabbas sunan ta Maryam amman bamu sani ba ko wacce kuke nema ce, amman kafin nan a ina kuka san ta ko ince menene alakar ku?"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now