💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 9By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ya fita, baki ta murguda ta shige daki, alwala tayi tai sallah tana zaune akan sallaya wayar Najwa tai kara Najwa na gani ta mika mata amsa tayi ta dauka ta kai kunnen ta yace
"Kinyi sallah?"
"Eh.""Ina fatan kin mana addu'a."
"Eh.""Me kika rokar min?"
"Allah biya maka bukatun ka na alheri."
Wani murmushi mai sauti yayi yace
"Nagode sosai, sai anjima.""Nagode."
Sukai sallama ta ajiye wayar, bayan isha'i Aliyu ya dawo yana falo suna hira da Sitti har tara, sai da ya mike zai fita yace
"Ina Maryam ne?""Tana ciki."
Sitti ta fada, Najwa ce ta fito daga daki, Aliyu na ganin ta yace
"Turo min Maryam."Ya juya ya fita, cikin mota ya shiga, bai jima ba ta fito sanye da hijab har kasa ta karasa tace
"Gani."
"Waye Muhammad?"Kai tayi kasa dashi yace
"Ba magana nake miki ba?"
Nan ma tayi shiru yace
"Ok sai da safe."Kan tai magana tini yaja motar ta dago tana kallon sa har ya kai gate mai gadi ya bude ya fice aguje kai ta dafe tace
"Wai meyasa haka ne?"
Baki ta murguda tace
"Kayi ka gama."
Ta juya tai ciki tai kwanciyyar ta.Gaba daya Aliyu bai bar Maryam ta sake ba dan kullum yana gidan da yamma kuma bai tafiya sai dare duk yadda Muhammad ke son yazo taki ta bashi dama dan tana tsoron haduwar su da Yaa Aliyu, a daddafe da kyar ta kwana bakwai tace zata tafi Najwa taso ta kara amman taki, Aliyu ne yazo da yamma ya maida ita gida.
A compound din su ta samu Haidar na buga ball yana hango ta ya karaso a guje yace
"I miss you Adda."
Ta daga sa tana fadin
"I miss you too."Ta sumbaci kumatun sa tana fadin
"Ya makaranta?"
"Alhmadulillah."Ta shafa sumar kansa tace
"Masha Allah."
Ya rumgume ta. Duk abinda suke Aliyu na tsaye yana kallon su sai murmushi yake mikewa tai ta dauke shi tana fadin
"Ummi fa?""Tana kitchen."
Dire shi tayi tace
"Bari naje naji dumin ta."
Tayi ciki tana fadin
"Ummi na kina ina na dawo."Ummi dake kitchen na aiki ta leko tace
"Ah Daughter u re welcome."
Maryam ta karasa ta rumgume ta tana fadin
"I miss you.""Miss u more yasu Sitti?"
Ta fada tana shafa bayan ta. Aliyu ne ya shigo Haidar a hannun sa sukai daki. Maryam ta shiga tace
"Me kike?""Girki."
"Yau zanci girkin Ummi.""Sai kace wacce ta shekara."
"Wallahi ni ji nake kamar na shekara."Tai murnushi tace
"Yasu Inna da Mami."
"Suna lafiya kullum Inna sai ta tambaye ki?""Ayyah bari naje na gaishe ta."
Ta juya ta shiga dakin Inna, tana bandaki dan haka ta dawo falo wayar Inna ta gani ta dauka ta fara rubuta number Muhammad kira ta tafi bai jima ba ya dauka tai sallama yace
"Kece?"Kai ta gyada yace
"Ina wayar ki?"
"Ban ganta ba.""Ah haba ko dai kin yar?"
"Kila since bata motar Yaya."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...