💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 23By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Aisha ta amsa ta mike ta fita tace
"Ya jikin nasa?"
"Da sauki yanzu Abbah zai zo ya dauko Maryam din yana son ganin ta.""Yah Alkasim mufa muna gidan ta ma har an kawo ta gidan ta."
"Au yau ne fa za a kawo ta ko wallahi na manta ma kwata kwata.""Allah ya kara sauki sai anjima."
Ya kashe wayar. Kira ne ya shigo daga abokan sa ya dauka
"Wai kuna ina ne?""Muna asibiti fa. Aliyu ne ba lafiya."
"What? Wanne asibitin?"
Nan ya fada musu sannan ya kashe wayar.Abbah gidan su Maryam ya nufa kai tsaye yasa ai masa magana da Abbi. Har sitting room aka kai shi Abbi ya fito yana ganin sa suka kara musabaha yace
"Daman kai ne?""Wallahi nine."
Suka gaisa sannan Abbah yace
"Dan naka ne fa ba lafiya, ""Aliyu! me yake damun sa?"
"To yana asibiti ma dai yanzu nima Alkasim yake fada min likita ne yace nazo na dauko masa Maryam da sai kiran sunan ta yake yi.""Ikon Allah! Ai yanzun nan aka kai ta sai muje mukai ta naga jikin nasa ko?"
"To ba matsala."
Suka mike suka fita tare. A kofar gida suka tsaya Abbi yace
"Bari naga ko su waye a ciki!"Ya dauki waya ya fara neman layin Ammi, dauka tayi yace
"Su waye a gidan Mama nah?"
"Fadima suna can.""Shikenan!"
Ya kashe wayar ya fita a motar Abbah ma ya fita suka nufi gidan knocking sukai Mai gadi ya bude su Abbah ya gani ya bude da sauri yana fadin
"Barkan ku da zuwa!""Yauwah!"
Suka gaisa sannan suka nufi cikin gidan a bakin kofa Abbi yai knocking, Fadima ce ta fito tana ganin Abbi ta matsa yace
"A'ah ba shiga zamuyi ba ina Mama nah?""Tana ciki!"
"Je ki taho min da ita kuma kuzo ku tafi gida kawai.""Lafiya Abbi?"
"Lafiya lou."
Ta juya tai shiga. Maryam na zaune akan sallaya ta shiga ta nufi wajenta ta kamo ta tana fadin
"Taso!"Mikewa tayi tace
"Su Yaa Haidar ne?"
"A'ah Abbi da Abbah ne!""Ina Yaa Haidar me ya faru me ya faru?"
"Ke ki nutsu ba komai Abbi yace dai kizo."
Ta kamata ta fita da ita. Bakin kofa suka hadu dasu Abbi ta nufi Abbi da sauri tana fadin
"Abbi ina Yaa Haidar dan Allah yana ina?"Hannunta ya kama yace
"Ki nutsu yana nan kinji ko?"
Hawaye take kawai dan hankalinta ya dada tashi, ya kalli Fadima yace
"Zan turo Abdullahi ya dauke ku, ku rufe gidan kunji!""To Abbi!"
suka fita Maryam rike da hannun Abbi jikin ta sai rawa yake a baya ya saka ta ya kalle ta yace
"Kina ambaton Allah kinji?"
Kai ta gyada ya juya ya koma gidan driver ya tada motar ya kalli Abbah dake kallon Maryam cike da tausayi yace
"Wane asibitin zamu?"Fada masa yayi ya tada motar suka nufi asibitin sam Maryam bata cikin hankalin ta da zata san ina ma suke tafiya sunan Allah kawai take kira tana hawaye har suka isa Abbi yai parking ya fito ya rufe ya budewa Maryam kofa amman sai ta tsaya kallon sa hannunta ya kamo yace
"Taho Mama nah!"Ta kama hannun sa suka fito harabar asibitin ta kalla ta kalli Abbi tace
"Abbi me ya faru? Me yasamu Yaa Haidar?"
Tayi maganar murya na rawa saboda kukan da yazo mata mai karfi. Kama hannun ta yayi yace
"Ki daina kukan nan dan Allah!""Na daina Abbi!"
Tai maganar da kana kallon ta kasan bata cikin haiyacin ta. Abbah yai gaba Abbi na bin sa rike da hannun Maryam har suka shiga reception din suka nufi corridor da dakin da aka kwantar da Aliyu. Alkasim ta gani da sauri ta sakin hannun Abbi ta karasa wajen sa tace
"Ina Yaa Haidar din?"
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...