Page 58

318 18 4
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 58

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Wayar ta ce tai kara da kamar bazata dauka ba sai kuma ta janyo ta ganin sunan dake kan wayar yasa tai saurin goge idon ta tare da danna received ta kai kunnen ta
"Assalamu alaikum."

Taji yai sallama ido ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya ta, dan a duk lokacin da zataji muryar Aliyu ita kadai tasan me take ji, a hankali ta amsa da
"Wa'alaikum ssalam."
Ido ta runtse tai shiru, shima shiru yayi sai can yace
"Me ya samu muryar ki?"

Shiru tayi yace
"Kuka kikai ko?"
Kai ta girgiza kamar yana ganin ta. Yace
"Karya kike kinyi kuka."

Mikewa tai ta fita yace
"Ummi fa?"
"Tana gidan Sitti."

"Ke fa?"
"Ina gida."

"Ke da wa?"
"Ni da Najwa zamuje lalle ne."

"Haidar fa?"
"Yana wajen Inna."

"To sai anjima."
Sukai sallama ya kashe wayar dakin, Ummi ta shiga ta wanke fuskar ta sannan ta fito ta koma daki.

Jawahir da Najwa suna hira ta shiga tace
"Muje ko?"
Suka mike suka fita. Daga lalle saloon suka wuce sai dare suka koma gida.

Da sukaje gidan Sitti ba masaka tsinke saboda yan uwa da abokan arziki, yan garin su duk sun zo duk da washe gari za a fara biki, Maryam dai na daki duk ta takura, ita dama haka Allah yayi ta bata da sakewa cikin mutane. Suna zaune sukaji an shigo da sallama, dagowa sukai suna amsawa wata kyakyawar yarinya ce ta shigo sanye da wata doguwar riga maroon kala sai dan mayafi da ta yafa hannun ta rike da waya da jakar ta, Najwa ce ta mike a guje tana fadin
"Tasleem oyoyo."

Dagowa Maryam tayi tana kallon ta, Tasleem ta huging Najwa tana fadin
"Amarya ta sha kamshi."
Sai ta kalli yan dakin, hannu ta daga musu tace
"Sannun ku."

Maryam tace
"Yauwah sis ya hanya?"
A share ta amsa da
"Ahamdulillah."

Jawahir ta mike tace
"Ni tafiya zanyi."
"Waye zai kai ki gidan?"

"Yaa Muhammad."
"Nima gida zan tafi."

Najwa ta juyo tace
'Saboda me?"
"Gidan ya cika ni gwara na koma wajen Ummi kema kizo mu tafi."

"Amman nan yafi in na tafi can ma sai na dawo nan."
"Shikenan gobe nazo."
Ta mike tace
"Jawahir muje ku ajiye ni."

Babu yanda Najwa bata yi da ita kan ta zauna amma taki, lokacin da taje wajen Sitti sallama ta zauna Sitti ta kalle ta taga yadda take yamutsa fuska, Sitti tace "Ko dai za ki wuce gida ne?"

Kai ta gyada Sitti tace
"To waye zai kai ki?"
Kai tayi kasa dashi tace
"Muhammad ne zai kai Jawahir gida sai ya ajiye ni."

Sitti tace
"To tashi ki je, sai da safe."

Tunda Maryam ta fito Muhammad ke kallonta, ta sunkuyar da kai tace
"Ina yini"
yace
"Lafiya lau."

Jawahir ta shiga gaba ita kuma ta bude baya ta shiga ta zauna tare da jinginar da kanta tana sauke numfashi a hankali, lokaci lokaci Muhammad ke satar kallonta sai ya sakar mata lallausan murmushi, ita dai sai dai ta sauke idonta, dai dai gate din gidansu yayi parking, a hankali ta kallesa tace "Nagode"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now