💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 52By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*******
Wani waje ya kai su, ya fito ya bude mata mota ta fito tana bin wajen da kallo bata taba ganin waje mai kyau da tsari haka ba. Harabar wajen yalwace take da shuke shuke ga haske da ya kawata wajen. motoci ne manya a wajen yai gaba ta bi bayan sa. Wata Kofa suka nufa security dake wajen yai sauri ya bude musu hanya ya bata tai gaba yabi bayan ta, suka shiga. Wani sanyi da kamshi ne ya doke ta. Wajen take bi da kallo duk da hanyar wucewa ce amman an kawata ta. Sai da sukai tafiya mai tsayi sannan ta fara ganin wajen saida abubuwa kala kala. Wani waje ya shiga da ita suka nufi can karshe duk da wajen ba mutane suka zauna. Basu jima da zama ba aka kawo musu lemo da menu. Amsa yayi yai ticking sannan ya mika mata, rasa me zata zaba tayi ya amsa ya zabar mata sannan mutumin ya juya.Kallon wajen take dan wajen ya matukar burge ta, ga sanyi ga ni'ima suna zaune aka kawo musu abinda suka zaba. Maryam ta dauka ta fara ci Ido ta lumshe tana jin wani dandanno da dadi a bakin ta.
Sun dauki kusan awa a wajen sannan suka bar wajen dan ya riga yai musu transfer.
Cinema suka nufa, nan ma suna zama aka kawo musu pop corn da lemo aka ajiye a gaban su.
Aliyu ne ya fara ci amman ita ko kallon sa batai ba Idon ta na kan film din da ake nunawa. Dauka yai ya bata ta amsa batai niyyar ci ba yace
"Kici da dadi."Diba tayi tai Bismillah ta kai bakin ta, tana taunawa ta lumshe Ido dan ji tayi kamar Madara kadai take taunawa ga wani dadi da bazata iya misalta shi ba. Kadan Aliyu yaci ya ajiye amman sai ga Maryam ta tashi da nata gaba daya. sai da aka gama film din suka mike zasu tafi ta kalli Aliyu ta kalli ragowar 🍿 din yai murmushi yace
"Dauko mana muje ma mu siyarwa Ummi dan tana sonsa."Kan ya rufe baki har ta dauki abin ta suka fita ya siya da yawa zasu fita ta kalli shi ta nuna masa wajen da suka fara zuwa yace
"Wani abu kike so?"Kai ta gyara suka shiga ya amshi menu ya bata ta kara zabar abinda ya siya mata dazu aka bata ya biya suka fita tana gaba yana bin bayan ta.
Suna fita suka nufi wajen motar su zasu shiga wata mata da tin da suka shigo take kallon su dan ba karamin burge ta sukai ba bama da yazo ya bude mata ta shiga ya rufe ya zuba kayan a baya har ya zagaya ta karaso wajen inda Maryam ke zaune tace
"Sannu 'ya ta."Dagowa tai ta sakar mata murmushi. Dai dai shigar Aliyu ya kalle ta yace
"Sannu Hajiya.""Yauwah sannun ku. Allah raba lafiya Allah kara baku zaman lafiya."
Tana fada ta juya Aliyu ya bita da kallo Maryam kuwa ragowar popcorn din sa take ci a haka suka bar wajen suka nufi gida.*
Sha biyu saura suka karasa gida. Abba yana ta zaune a inda yake yaga shigowar su ya zuba musu Ido har Aliyu ya fito ya bude mata mota ta fito tai gaba yabi bayan ta da kallo ya bisu har suka shige bangaren Ummi. System din gaban sa ya rufe ya mike ya shiga dakin baccin su. Mami tai bacci shima kwanciyya yai yayi addu'a ya kwanta.Suna shiga tai sama shi kuma yai dakin sa. Kayan jikin ta cire ta shiga ta watsa ruwa ta fito ta saka kayan baccin ta ta hau kan gado tana addu'a Ummi ta bude kofar ta dago tana kallon ta.
"Sai yanzu kuka dawo cikin daren nan?"Kai tai kasa dashi dan itama sai yanzu taga dare yayi sosai har haka. Ummi ganin tayi kasa da kai tace
"Kinci abincin?"
Kai ta gyada mata. Shigowa tayi ta rufe kofar ta kwanta tace
"To kiyi addu'a kinji."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...