💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 76By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ana gobe zasu tafi Malam ya kirata a parlorn sa, ta shiga kan ta a kasa zama tayi daga gefen, dagowar da zatai taga Aliyu zaune a kusa da ita, kai ya dauke ta gaishe da Malam ya amsa sannan ta gaishe da Aliyu ya amsa ba yabo ba fallasa, ita ta rasa saboda me yake mata haka kwanan nan ko dan yaga ta damu da shariyar da yake mata ne, kai ta dauke kawai. Malam ne ya fara magana wanda duk nasiha ce yake musu mai shiga jiki, daga nan kuma ya fara jan su da hira ita dai shiru tayi amman tana jin yadda suke ta hira da Aliyu sai kace wanda suka jima da sanin juna.
Suna zaune taji sallamar Haidar karami ta dago tana kallon kofa shima yana shigowa ita ya fara arba da ita dan yau kwata kwata bai ganta ba dan daga wannan ya dire wannan zai dauke shi kuma akwai sa da son mutane ganin sa cikin yan uwa yasa ya sake. A guje ya fada jikin ta yana murnar ganin ta, ta rungume shi tana mai jin wani iri, dan Yaa Haidar ne kadai ya fado mata da ace yana raye da komai bai faru ba da ta ina Yaa Aliyu zai na bata mata rai ta ina ma zata san shi bare har ya share ta taji haushi. Yana lura da yanayin ta duk sai yaji ba dadi, kai tayi kasa dashi tace
"Malam bari naje na kwana sai da safe.""Allah tashe mu lafiya, Allah muku albarka."
Ta mike ta fita dauke da Haidar da ya rumgume ta, da kallo ya bisu yana mai jin kamar yabisu ya lallashe ta sai dai kuma wata zuciyar tace ya barta. Tana shiga ta samu kakanin nata gaba daya dasu Inna da Sitti zama sukai Haidar ya lafe a jikin ta dan ya gaji bacci yake ji.Hankalin su suka dawo dashi kansu, ganin yanayin ta duk yasa sukaji ba dadi, nan su Inna suka hau lallashin ta da mata nasiha da jan kunne, kafin daga bisni suka 'buge da hira, wajen tara da rabi suka shige daki ita da Haidar suka kwanta.
*
Washe gari wajen karfe 10am suka kammala shirinsu gaba dayansu, Malam dasu Inna har bakin mota suka rako su Abbi, Maryam har da hawayen ta dan sati dayan da sukai taji dadin garin taga gata da kulawa Haidar karami ma da Abbin sa sunji dadin garin sosai ba wanda yaso ya bar garin a lokacin, haka Malam ya loda kayan abinci da amfanin gona dasu nono, kaji, zabi, kwai akan a bisu Ummi dashi wanda daga nan kayan aka sa su tafi can Abuja su Ummi saje su tadda shi dan sai sunje Kano kafin su wuce Abujan.Ranar da suka iso a ranar Yaa Ahmad ya sauka a garin Kano shima, da dare suna zaune a falo ita da Ammi ya aika cewa ace Ahmad ne yazo. Ammi tace "Allah Sarki Ahmad gaskiya ya rike alkawari kinsan baya wata bai zo ba duk da kina ganin ba a garin nan yake ba kullum yana cigiyar ki yau kun dawo ma ya kasa zaune bare tsaye, shi ya fara warware mana komai akan alamari nan. Allah ya saka masa da alheri dai."
Maryam ta amsa da amin tana daukar hijab din ta, ta saka, sallamar Ahmad suka jiyo suka amsa ya shigo cike da ladabi ya gaishe da Ammi ta amsa fuska a sake.
Daga nan ta tashi ta bar falon ta koma daki, Maryam ta durkusa ta gaishe shi ya amsa yai mata ya hakurin Aliyu, wanda har hawaye ya kawo a cikin idon ta, cikin lallashi yace
"Kiyi hakuri haka rayuwa tayi damu ban tashi sanin rasuwar Aliyu ba sai bayan wata kusan uku, a lokacin naji mutuwar na shiga damuwa da tashin hankali wanda na rasa yaya zanyi dana zo shine Alkasim yake fada min bakya ma gida ga abinda ya faru, ni na fara sanar dasu cewa da aure tsakanin ki da Aliyu na wata uku, ni na dauki Abbi na kai shi wajen malamin da ya daura auren anan aka kara bazama neman ki sai dai Allah bai nufa za a same ki ba sai yanzu, naji dadi da farin ciki da aka ce an ganki."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...