💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 57By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
~Cigaban labari~
Da dare, Ummi, Abba da Maryam suna zaune a falo, Maryam na kwance akan three sitter an saka mata karin ruwa, bacci take sama-sama, sai Abba da Ummi dake magana akan zuwan Muhammad, wayar Abba ce tai kara Ummi ta mika masa ya amsa, wanda karar wayar yasa Maryam ta bude idon ta a hankali, sai kuma ta mai dasu ta rufe.
Abba ya dauki wayar yace
"Muhammad ka karaso to ka shigo mana."
Da sauri Maryam ta bude ido tana kallon Abba to wanne Muhammad din? Ido ta mayar ta rufe dan wani bacci ke son dibar ta dan har da allurar bacci akai mata saboda ta samu hutu da nutsuwa dan jinin ta har ya hau.Ummi tace
"Ai bangaren Abbi zaku ko?"
"Eh bari na kira naji ya dawo?"Sallama Muhammad yayi ya shigo, su Ummi suka amsa masa ya karaso ya durkusa ya gaishe da Ummi da Abba suka amsa Ummi tace
"Zauna mana."Kan sa a kasa yace
"Ummi nan ma yayi."
Ya zauna a gefen carpet, Maryam ya saci kallo yaga yadda idon ta ke motsi alamar ba baccin take ba bude idon ne bata so, Ummi ya kalla saboda Abba na waya yace
"Ummi bata da lafiya ne?""Eh bata jin dadi."
"Allah sauwake.""Amin mungode."
Abba ya gama waya yace
"Tashi muje."Muhammad ya mike yabi bayan Abba, har cikin babban falon sa suka karasa, ya zauna akan carpet, Abbi yace
"Ah Muhammad yi zaman ka akan kujera.""Nan ma ya isa."
Ya fada yana gaishe shi. Abbi ya amsa sannan yai gyaran murya, zai magana kenan Farouk ya shigo, ya gaishe da su Abbi sannan ya mikawa Muhammad hannu ba yabo ba fallasa suka gaisa, gyara zama yai shima akan carpet, Abbi yace
"Muhammad mun kira ka ne akan Maryam, hakika wani lokacin ina manta alakar mu da ita domin mun dauke ta tamkar yar cikin mu, zan iya ce maka tafi wasu ya'yan namu a wajen mu, yarinya ce mai ladabi da biyayya wacce take da addini da ilimi, mai son kyautatawa kowa bata da hayaniya bare fada tin zaman mu da ita a gidan nan na sama da shekara hudu ban taba jin wani yace tai masa abu na batanci ba sam, kullum cikin kyautatawa mutanen gidan nan take, duk wanda ya samu Maryam ya dace kuma ya samu babba rabo. Ba ina fada maka haka bane dan na yabeta ko in kara maka son ta ta yadda zaka kara kwadaituwa da ita ba, sai dan naga kai ma kana da hankali in har haka zata faru zamufi kowa jin dadi dan fatana kenan Maryam ta samu me rike ta tamkar tana hannun mu bana son tai maraicin komai da kowa."Abbi ya dakata Muhammad kan sa na 'kasa sai yanzu ya gane cewa Maryam ba yar gidan nan ba kila yar kanin su ko wansu ce, kila iyayen ta ne suka mutu. Maganar Abba ce ta dawo da shi daga tunanin da yake,
"Mun tsinci Maryam shakara hudu da wani abu da suka wuce a garin Bauchi lokacin munje wani aiki da mai daki na akan hanyar mu ta dawowa muka bige ta wannan dalilin yasa muka kai ta asibiti, dole mu tsaya akan ta muga yanayin jikin ta wanda a dalilin haka muka kwana a asibitin duk da cikin dare ne amman da mai daki na ta bukaci ta kira gida sai muka gane bata da kowa, ko kuma nace tamkar ta rasa komai na tunanin ta, dan bata tuna kowa sai mutane biyu a rayuwar ta da muka tambaya ina suke kuma bata sani ba, gashi kuma bata magana, a wannan halin da muka same ta muka sa likita ya bincika mana lafiyar ta wanda anan muka gane matsalar ta na da yawa tana da ciwon zuciya, ga damuwa, kuma rashin magana ma razana ita ta dauke mata ita sai abu na karshe shine tana da cikin watanni wajen uku."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...