💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 8By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Bayan isha'i ta idar da sallah, ta mike ta nufi kofar fita wayar ta dake can kan mudubi ta fara ringing kan ta karasa ta katse, tana dauka taga Muhammad ne ya kirata, komawa tayi ta zauna tayi dialing, katsewa yayi ya kira cikin cool voice din sa yai mata sallama ta amsa tare da gaishe shi. Yace
"Ba zan amsa ba bayan dazu nunawa kikai baki sanni ba.""Nima ai haka kai min."
Tai maganar a shagwabe, yai murmushi yace
"Nifa ba kuka nace ki min ba ko?""Uhmm to ina yini?"
"Lafiya lou ya gajiyar school?""Alhamdulillah."
"Masha Allah. Dazu kinyi kyau amman fa.""Hmmm kaji ka."
"Allah da gaske ban gaji da kallon ki ba.""Uhmm ina Abdul kwana biyu."
"Baku hadu ba?""Eh kwana biyu banje gidan Sitti ba."
"Yaushe zakije?""Ban dai sani ba."
"To ya shirye shiryen biki?""Alhamdulillah."
"Allah ya kaimu.""Amin."
"To sai da safe.""Allah tashe mu lafiya."
"Amin."
Ta kashe wayar ta mike ta fita.*
Yau watan ta biyu kenan rabon ta da gidan Sitti ba wai zuwan ne batayi ba tayaya zata tambayi Yaa Aliyu zata take tunani tasan halin sa, da sauri ta mike tace
"Shi Yaa Aliyun nan in yasan wata bai san wata ba Abba zan tambaya tinda yana gari."Ta mike ta nufi dakin Abba sallama tai yana zaune a falon sa ya amsa ta shiga ta zauna tare da marairaice fuska tace
"Abba zan je gidan Sitti nayi ko sati daya ne tinda mun samu hutu.""To Maryam ki shirya ki tafi mana kin fadawa Maman taki?"
"A'ah haka nace bari na fara fada maka.""Ok kije ki shirya to."
"Nagode Abba."Ta mike ta shiga dakin Ummi a zaune ta same ta tana danna wayarta, ta zauna tace
"Ummi gidan Sitti zani nayi mata sati daya.""To yaushe zaki tafi."
"Yanzu in na gama hada kaya na.""To shikenan. Je ki hada kayan."
Ta mike ta fita tana murna, dakin ta ta shiga sai ga kiran Muhammad nan dauka tayi tin daga muryar ta ya gane tana cike da farin ciki yace
"Ya dai yar gida na?"Tai murmushi tace
"Yau zani gidan Sitti."
"Da gaske ko na zo na kai ki?"
"A'ah.""Why?"
"Ba komai.""No ba dai ki yadda dani ba ko?"
"A'ah fa.""To in ba haka ba zan zo na kai ki."
"To shikenan.""Da karfe nawa."
"Yanzu."
Yai murmushi yace
"Gani nan."Ba ai minti ashirin ba sai ga Muhammad ya kira ta wai yazo, jakar ta ta rufe ta mike ta fita a dakin wajen Ummi ta shiga tai mata sallama sannan taje wajen Abba ta fita taje wajen Sitti tana fitowa daga wajen Sitti ta hangi Aliyu na tahowa sanye da wando nude colour sai milk riga mai dogon hannu, kafar sa da sandal baki, kamar ta koma ciki haka taji amman saboda ya ganta sai kawai ta maze ta fara takowa.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...