Page 12

327 21 2
                                    


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 11

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

*
"Shikenan na gane matsalar da aka samu tin daga wajen su Abba ne ya kamata su farai masa bayani in yasan wacece ke shikenan, naji anan anyi ba dai dai ba, amman ki daina fadar ba zaki aure ba, menene aibun ki, ina da yakinin duk daga inda kike kina da asali da tsatso mai kyau, a halaiyar ki menene marar kyau, kina da hakuri tarbiyya ilimi ga hankali me za kuma a nema a wajen ki, ki bar damuwa da izinin Allah zaki tuna da kowa naki zaki ga iyayen ki kuma zaki aure ki kara haihafa dan Allah ki daina kuka da saka damuwa, ko Muhammad yaki ki wani zai zo ki duk aibun ki bare ke baki da wani aibu dan haka kiyi hakuri ki cire damuwa kinsan kina da ciwon zuciya ko so kike in rasa ki, kina zaton in na rasa ki wane hali zan shiga, ban taba haihuwa ba sai gashi Allah ya hada ni da yara biyu a lokaci daya ni me zanyi to nagodewa Allah na amshe ku to kema ki godewa Allah kuma mu kara tashi da addu'a zamu kara komawa asibiti a duba ki muga ko za a samu wani cigaba da yaddar Allah zakiga iyayen ki da yan uwan ki, ki daina kuka kinji?"

Rumgume Ummi tayi kawai tana sauke ajiyar zuciya. Ummi ta shafa bayan ta tace
"Sorry kinji Daughter."
A haka bacci ya dauke ta,  Ummi ta dade a dakin sannan ta mike ta rufe mata dakin.

Daki ta shiga ta zauna tare da zuba tagumi, wayar ta ce tai kara tana dauka taji muryar Aliyu, ta sauke ajiyar zuciya tace
"Son ka sauka lafiya?"

"Lafiya lou Ummi ya gidan? Ina Maryam"
"Tana nan kalau."

"Masha Allah. Ummi kin tambaye ta?"
"Aliyu ba yanzu ka sauka bane kaje ka kwanta ka huta ko?"

"Ummi kar ki damu ki fada min me tace miki? Maryam na cikin damuwa Ummi bana son ya taba mata lafiyar ta please Ummi ki fada min."
"Shikenan yanzu kaci abinci?"

"A'ah Ummi bana jin yunwar Ummi."
"To shikenan akan batun wanda yazo neman auren ta ne."

"Cewa tayi bata son sa?"
Ya fada da sauri, Ummi tace
"Ba haka bane, bansan me ya mantar da Abba ba bai masa bayani akan wacece Maryam ba......"

Da sauri ya katse ta da fada yace
"Cewa yai baya son ta dan bata san iyayen ta ba?"
"Haba Haidar cool down mana, ba haka bane, yaso yaji wani abu akan ta ne."

"Bashi da hankali yaje yai bincike mana a wajen ta zai ji lallai...."
"Aliyu ba haka bane ya tambaya ne kawai."

"To me yace akan haka?"
"Ba haka bane Aliyu, i think ma ita bata bashi amsa ba, shine abinda yake damun ta dai."

"Shine take kuka dan kada yace baya son ta, ce mata akai ba zata samu wanda yake son ta ba haka? Menene da ita da za a 'ki tan?"
"Aliyu dole ta damu ai."

"Akan me? Akan me zata damu? Dan kada ya guje ta? Wai yaushe ta san shi ma da zata saka shi a zuciyar ta haka? In ba zai iya ba ya kyale ta mana me zatai da shi itama, ai tafi karfin sa, Ummi in ta tawa ce a hanata kula sa in har zai na saka mata damuwa bana so sam"

"To menene na daukar zafi ne haka, ai laifin mune da bamuyi masa bayani ba zanwa Abban ku magana sai ai masa magana ya sanar dashi in yaga yana so to in baya so ni nasan wani zai zo mata insha Allahu."
"Is better dai."

"To kaje ka huta."
"Sai da safe."
Ya fada ya kashe wayar sa dan ransa ba karamin baci yai ba, kwanciyya yai akan gadon yana dafe kansa da yaji ya dau zafi, kila fa yanzu tana can tana kuka akan wani can yazo ya tada mata da hankali yasa mata damuwa. Mikewa yai ya dauki wayar sa, layin Maryam ya fara nema amman sai aka ce masa a kashe take kira ya kara yi same a kashe take wayar yai cilli da ita, ya mike ya shige ban daki. Yana shiga ya sakarwa kan sa ruwan ya jima a karkashin shower ruwa na zubo masa amman bai bar wajen ba, sai daga baya ya fito daure da towel, jallabiyya ya dauka ya  saka, ya hau kan sallaya dan yayi sallah yana idarwa yaji ana knocking budewa yayi yaga Yasmeen yar yar Ummi ya saki murmushi yace
"Baby Yasmeen."

"Big bro Momy ce tace wai kazo kaci abinci."
Hannun ta ya kamo yace
"Am not hungry dear."

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now