💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 16By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Murmushi tayi tai gaba zata shiga da sauri ya karaso ya bude mata mota ta shiga ya rufe sannan ya zagaya. Motar ya tayar mai gadi ya bude musu suka fita. Sai da suka hau titi yace
"Ya zancen kudin kwalliya da gyaran amarya banji ance na bayar ba.""Oh amsa ake yi daman?"
"Baki sani ba. Nasan da Fadima na nan da yanzu ta damen da zancen.""Ni ai nasan Abbi zai bayar ba sai ka wahala ba."
"Wacce irin wahala kuma ai hakki nane nifa za a gyarawa ke."
Ya fada yana kashe mata ido daya.Kai tai saurin daukewa tace
"Kai Yaya ni ka bari."
Dai dai karasowar su shagon da zai amshi sakon waya kawai yayi ya fito ya bashi sakon suka dauki hanya. Sai da suka hau hanya sosai yace
"Me zan bari *Matar Haiydar* ni dake fa mun riga mun zama daya wannan kunyar please a ajiye ta gefe kar ta hanani sakewa da Matata."Murmushi tayi tace
"Uhmm naga katin?"
Mika mata bag din yayi ta bude kati ne kala biyu daya na kamu da yini ne dayan kuma na dinner ne duk sunyi kyau sosai ko wannen yana cikin envelope din sa na Dinner har da sit number.Bag din ta rufe tace
"Amman sunyi kyau!"
"Basu kai Matata kyau ba."Murmushi tayi tace
"Yaushe Yaa Ahmad zai dawo."
"Wannan dan iskan sai ja min rai yake yaki ya fada min yaushe zai taho amman ya kamata ace dai dis week end ya taso since wenesday za a fara biki."Murmushi tayi ya kalle ta yace
"Monday in naje zan dauki hutu, wata nawa kike so na dauka?""Wata kuma Yaya?"
Ta tambaya tana zaro ido, murmushi ya saki yace
"Eh wata nawa?""Haba My Hayyat wata ai yayi yawa sati daya fa ake dauka zuwa biyu!"
"Inji wa?""Mutane!"
"Baby nah ke daban ce wallahi sati daya ya min kadan zan ce su bamu three month dan daga nan zamu wuce honeymoon ko ya kika ce?"Hannu ta saka ta rufe fuskar ta tace
"Kai Yaya aikin fa, kaga sati biyu ya isa honeymoon ai kullum muna cikin sa dan kaje ka dawo dai kawai."
Motar ya tsayar ya juyo yana kallon ta wanda yasa tai saurin yin 'kasa da kan ta tana wasa da yatsun hannun ta.Hannun ta ya kamo yace
"Ma'ul Ayn kinsan yadda nake jin ki kuwa a zuciya ta, ina yawan fada miki amman kamar kina mantawa daga lokacin da na sanki daga lokacin so, kauna, shakuwa, tausayin ki suka dadu a zuciya ta, wallahi ko awa daya bana so naji na nisanta dake, hakika Allah shi ya dauran son ki, tin baki da abinda za a kalla a soki, sonki shine rayuwa ta duk lokacin da na rasa ki mutuwa zanyi, ba da wasa nake ba duk fitar numfashi na ko bugawar zuciya ta da sunan ki suke bugawa, ki gane yadda nake kaunar ki, bana son na nesan ta dake ko na minti daya, kina gani dan haka nai 'kaura na dawo gidan ku, dan numfashi na da naki suna gauraya a cikin waje daya, hakika duk lokacin da muke tare zan nuna miki so da kaunar da bazaki taba mantawa da ita ba, Ina sonki da kaunar ki, fatana mu rayu dake har tsufan mu ki haifa min ya'ya shine kadai burina na gaba....."Hawaye ne ya fara zubo mata a idon ta ya dago kan ta yace
"Kuka kuma Baby menene?"
Ya fada yana lashe hawayen idon nata jikin sa ta fada ta rumgume shi sosai tana fadin
"Na yadda da kai Yaa Haiydar shiyasa na baka duk rayuwa ta, Yaa Haiydar nasan bazan taba samun makamanciyyar soyayyar ka ba, da kai na rayu, na tashi nayi wayo son ka na budi ido na ganni a cikin sa dan Allah kada ka tafi ka barni, kada kayi nesa dani ko yaya ne Yaya na, zan kasance maka yadda kake so na kasance zan maka biyayya iya kar iyawa ta zan baka farin ciki Yaya nah ina son ka da kaunar ka, kaine hasken rayuwa ta."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...