Page 24

357 15 1
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 24

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Ya ja masa abu ya rufe fuskar sa. Yaa Alkasim ne ya shigo yana ganin haka yace
"Abbi me ya faru?"
Kai Abbi ya girgiza, Yace
"Sai dai muyi hakuri!"

Dai dai shigowar Abbah da Yaa Muhammad kenan. Abbah yace
"Ya rasu ko?"
Kai Abbi ya gyada masa kawai yai shiru. Abbah yace
"Allah ya jikan ka Aliyu Allah yasa can tafi nan Allah ya yafe maka. Ni bakai min komai ba inma kayi a rashin sani ne kuma na yafe maka. Allah ya jikan ka Aliyu...."

Ya kasa karasawa saboda muryar sa dake rawa. Abbi ya karaso ya dafa shi yace
"Kayi Hakuri Allah masa rahma."
"Amin!"

Yaa Alkasin kuwa gaban gadon ya karasa cikin shock yake kallon Aliyu dake rufe bude shi yayi ya zuba masa ido yana fadin
"Anya kuwa Abbi, kalli fa!"

Ya nuna sa yace "Yana numfashi Abbi bai mutu ba, ba yanzu zai mutum ba Abbi kazo ka duba kaga."
Abbi ya girgiza kai ya dawo ya kara duba Aliyu ya dago yace
"Sai hakuri fa Alkasim!"

Dagowa Alkasim yayi yace
"Abbi kalli fa yana numfashi."
Tausayi ya bawa Abbah, Abbi da Yaa Muhammad dan ba numfashin da yake yi. Abbi yace
"Muhammad kira likitocin suzo su kara duba shin."

Ya juya tare suka dawo da wasu nurse da Doctors su Abbi suka basu waje duk suka fita, aka barsu suna kokarin su dawo da nunfashin sa. Amman ina Allah ya amshi abinsa, babu yadda suka iya babu yadda zasuyi saboda wanda ya hallice sa ya dauke wanda ya fisu son shi ya dauke, wanda kowa na can ne, kowa ita yake jira can ne gidan gaskiya ba nan ba Allah ya bamu ikon cikawa da kyau da imani. Allah jikan musulmai yasa sun huta ya kyautata namu zuwan, Amin.
Bayan minti kusan ashirin suka fito gaba dayan su. Da sauri Alkasim ya karaso yace
"Bai mutu ba ko?"

Kai ya girgiza sannan ya dafa shi yace
"Am sorry to say...."
Baya Alkasim yayi da sauri Doctor ya taro shi ya shiga dakin da Aliyu yake. Ruwa ya shafa masa ya farfado yana ganin gadon Aliyu ya mike ya nufi wajen yana fadin
"Dan Allah kuce min karya ne bai mutu ba. Ku kalli fa yana numfashi wallahi yana numfashi kalli cikin sa yana dagawa da komawa."

Kalla sukai sukaga sam ba abinda ke motsi a jikin sa dan haka suka kama Alkasim suka fita dashi suka samu Abbi da Abbah sukai masa bayani. Alkasim kuwa yaki yadda Aliyu ya mutu sai cewa yake su kara dubashi. A haka suka cike komai sannan suka dauki gawar Aliyu aka tafi gida da ita.

*
*
*
Tin da suka fita daga asibitin take kuka ta rasa na menene tasan dai tana tsoron kar abinda Aliyu ya fada ya tabbata kuma tana tsoron kada ya tashi cikin sa yai ta ciwo. Gaba daya ta gama rudewa da fita a hankalin ta domin kuwa bata gane komai da kowa sai zuciyarta dake ta dukan tara-tara kamar zata ballo kirjinta ta fito. A haka suka karasa gida Ammi ta kamata ta sukai ciki. A falo suka samu Inna,  Yaya Zainab, Yaya Rabi, Yaya Ummulkurusm, Yaya Hauwa da wasu kannen su Ammi da Abbi. Suna shiga suka hau tambayar ya jikin nasa. Ammi ce tai karfin halin cewa da sauki sannan ta wuce da ita ta kai ta dakinta anan ta samu su Aisha da Rukayya da Zarah da Yaya Fadima duk idon su biyu suna jiran dawowar su.

Jikin Yaya Fadima ta fada tana sakin wani kuka mai ban tausayi da sauri Ammi ta juya ta fita Aisha da Rukkayya da Zarah duk suka karaso suka rufe Maryam suna lallashin ta. Kuka take kamar ranta zai fita dan har numfashin ta yana daukewa yana dawowa.

Mamah ma na komawa aka hau tambayar ya jikin sa. Kanwar ta Hajara ita ta basu amsa Mamah ta shiga daki ta zauna. Yaya Hauwa ce ta shigo ta zauna tace
"Yaya dan Allah kada kisa damuwa ki masa addu'a!"
"To Hauwa."
Ta fada ta zuba tagumi kawai.

Karfe sha biyu da rabi su Abbi suka karaso gida bangaren Aliyu aka wuce da gawar Aliyu. Abbi da Abbah ne sukai masa wanka. Abbi ya aika Yaa Muhammad ya debo kayan da za a bukata a dakin sa. Ta kofar baya ya shiga ya dauko duk abinda za'a bukata suka dawo akai masa wanka aka shirya shi cikin shigar sa. Suka ajiye shi anan falon sa. Aliyu ya kara tsayi da haske da ka kalli face din sa ta kara kyau sai murmushi dake dauke akan fuskar sai ka zata zai yi motsi.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now