💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 11By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir rahmanir rahim*
*
Ji tayi gaban ta ya fadi abu da ta jima da mantawa ya dawo mata kwakwalwar ta ta shiga kai koma, yadda ta fada duniyar tunani, yace
"My wife."Da sauri ta dago wanda idon ta tini yai ja, ga hawaye da ya taru a ciki, shima take ya shiga damuwa yanayin ta ya sauya idon ta har ya kada yai jawur kallon ta yayi yA yace
"Subhanallah meya faru?"
Kai ta girgiza ta mike tana fadin
"Kayi hakuri."Sai tayi cikin gida da sauri, dakin ta ta shiga ta fada saman gado rayuwar ta take son ta tuno so take ko ta halin yaya ta tuno wani abu amman ina ta manta tasan dai ta kasance a wannan gidan wanda yake shine gatan ta a duniya kawai su suka rufa mata asiri suka zame mata iyaye da family, shin su waye iyayen ta? Ina suke? A baya ne take shiga wannan halin na son lallai sai ta tino su waye iyayen ta wanda in tai wannan tunanin yake saukar mata matsanancin ciwon kai saboda damuwa in ba sa'a ba sai ta kwanta ciwo ma.
Bata san lokacin da bacci ya dauke taba, Ummi ta leko dakin ta ganta kwance ta rufe kofar kawai ta barta da dare Aliyu ya aika Haidar ya kira Maryam, lokacin har ta saka kayan bacci, kana ganin ta zaka gane tana cikin damuwa, hijab ta dauka har kasa ta daura sannan ta fita, ba kowa a falo dan lokacin tara ta gota, dakin ta nufa ta kwankwasa aka amsa ta bude a hankali, zaune ta same shi akan kujera da remote a hannu.
"Gani."Ta fada tana duban shi sai taga ya daure fuska, itama fuska daure dan daman bata cikin walwala tun dazu da aka famo mata inda yake mata ciwo. A ranta tace
"Miskilanci na shi ya tashi kenan."Bai kalle ta yace
"zauna"
Ta zauna, ya dago ya dube ta yace
"Waye Muhammad?""Nima ban san shi ba."
Wani murmushi yayi yace
"Bana son karya, ke kuma yanzu kina son ki koya ko?"Kai ta girgiza yace
"Nasan kin sanshi tinda ke kika bashi dama zuwa wajen Abba, buri na akan ki, ki tsaya kiyi karatu, kamar yadda kike fita da point mai kyau ya zama har karshen karatun ki haka amman ke kin nuna kin girma aure kike so ko? Ki sani in nace a'ah ba wanda zai ce eh dan haka ba zan bar yaron yana zuwa wajen ki bane dan ya hanaki karatu, ko da tafiya zanyi bana son yawan zance a wata sau biyu ya isa dan ina da buri akan ki, wani can ba zai zo ya lalatan buri ba dan haka ki kiyaye ke kina son sa ne?"Banza tai masa dan ya fara bata mata rai ina ruwan sa da tana son sa ko bata son sa ya bari ya gani ko yaji mana,
"Ba magana nake miki ba."
Ya fada wanda hakan ya sa ta dagowa da sauri duk da yadda yaga idon ta a kumbure sai ya kau da kai yace
"Uhmmm."Shiru tayi yace
"Shawara daya zan baki kada ki soma yin kokarin rusa min buri na, in har kikai haka daga ke har ni ba wanda zai ji dadi, ki daure ki cika min buri na akan ki."
Dagowa tayi tana son karin bayani gane haka yasa yace
"Eh akan karatun ki."Kai ta dauke yace
"Shine gatan mu, kuma ilimin shine madogarar mu, kina ji ko?"
Kai kawai ta gyada, yace
"Kar kice zaki bar karatun ki kiyi aure wannan duk bata lokaci ne da daurawa kai wahala.""Ni daman ba aure zan yi yanzu ba, karatu nake so na karasa kuma shima ya sani."
"Na fada miki dai dan kar yazo ya hure miki kunne gashi ni zan tafi amman duk da haka zan saka ido akan ku, na sani ba wai son sa kike ba ko kina son sa?"Kai ta gyada yace
"Karya kike Maryam, ki koma ga zuciyar ki ta fada miki wanda kike so amman ni nasan ba son Muhammad kike ba."
"Yaya....."Hannu ya dauran akan bakin sa yace
"Bana son naji wani abu, da kina son sa da dazu dana tambaye ki, kin sanar min amman kin kasa saboda har zuciyar ki ba son nasa kike ba, bana son kije inda za a wulakanta ki, ina son kije inda za a kula dake inda akasan darajar ki."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...