💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 28By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Dai dai farkawar Maryam wanda taji abinda Nurse din ta fada. Dummmmmm haka dakin ya koma babu wani abu da yake motsi na wani dan lokaci. Kallon kallo suka fara yiwa juna. Maryam kuwa zuciyar ta kamar ta fito daga kirjin ta dan yadda take bugawa da tsalle. A wannan lokacin da za'a sake auna jinin ta ba karamin hawa ya sake yi ba saboda tsananin firgicin da ta tsinci kanta a ciki.
Takardar hannun nurse din Yaya Zainab ta fizga tana karantawa jikinta ya hau rawa. Yaya Ummulkursum ta karbi takardar suka hada kai ita da Yaya Fadima da Yaa Abdullah suka karanta. Gaba dayansu takadar suka saki ta fadi kasa fuskar su cike da tsoro da fargaba.
Ammi dake gefe ta zaro ido tana tambayarsu me suka gani a takardar. Kasa magana sukai. Yaa Alkasim kuwa ko kallon takardar baiyi ba ya fita wurin likitan ya nufa ya samu Yaa Muhammad suna tattaunawa akan ciwon Maryam da rashin maganar har yanzu. Kamar wanda aka jeho haka ya shiga office din ransa ya gama baci. Yaa Muhammad ya mike da sauri yana fadin
"Menene ko jikin Maryam din ne?"
"Ina fa ba gwara jikin ta ba da abinda suka ce tana dashi. Wata mahaukaciyar nurse ce take fadin wai ciki ne da ita!"Ya maida kan sa kan Doctor yace
"Ka taso muje ka duba ta da kan ka, dan ni ban yadda da aikin ta ba ko canjen result akai."
"Is ok ka kwantar da hankalin ka kaji zan kara duba ta, na gani kaji!""Is better!"
Ya biyo bayan sa, suka nufi dakin gaba dayan su. A tare suka koma dakin wanda yayi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa. Karar fanka kawai ake ji sai jefi jefi wannan ya kalli wannan. Suna shigowa likitan ya dauki result din ya karanta.Kallon Yaa Alkasim yayi yace
"Ba an daura mata aure ba, mijin ya rasu?"
"Yes!""So shine me?"
"Kaga ka kara gwada min ita kawai."Sirinji ya dauko a cikin aljihun lab coat din sa sannan ya karasa wajen gado inda Maryam ke kwance komai ya tsaya mata cak. Jinin ta ya dauka sannan ya fita da kansa ya shiga lab ya kara yin gwajin. Sai da yayi sau uku yana bashi result iri daya dan haka ya dawo dakin. Kowa yasa ya fita sannan ya karasa wajen gadon inda Maryam dake jin duk abinda ke faruwa take.
Ido ta bude wanda ya rine yai jajir, Paper ya bata yace
"Zan miki tambayoyi kinji kanwata?"
Kai ta gyada!"Wata nawa da auren ku?"
Shiru tayi tana nazari kan ta ya kulle wanne zata fada to wannen ne dai dai in ta fadi wancan me iyayen su zasu ce."Kanwata!"
Ta dago ta kalli shi.
"Fada min kinji?"A paper ta rubuta sannan ta mika masa. Amsa yayi ya gani yace
"Are you sure?"
Kai ta gyada yace
"When last did you saw your period?"Abinda tin dazu kwakwalwarta ta kulle babu wani tunani da take iya yi sai yanzu ta dawo hayyacinta da taji wannan tambayar. Hankali a tashi dan zata ce tin kan su fara exam da tayi wani period marar ta tai ciwo har ta dawo gida bata karayin wani ba. Shin me hakan ke nufi kenan?
Taiwa kan ta tambayar
"Fada min kinji!"
Rubuta masa tayi ya amsa sannan yace
"Kin tabbata?"Kai ta gyada masa ya jin jina kai yace
"Good"
Fita yayi ya kira Ammi da Abbi sannan ya kalle su yace
"A bisa binciken da nayi da kuma amsar da tambayoyi da nai mata, ya nuna tana da *CIKI* na kusan wata uku.""Lahaula walaquwwata illabillah........ La'ilaha illalahu Muhammad Rasulillahi Sallalahu alaihi wasalam!"
Ammi ta fada. Mika musu result yayi sannan ya fita.Amsa Abbi yayi da zuwan sa kenan bai san me yake faruwa ba. Takardar ya karanta sannan ya juya ya fita kawai. Ammi ta bishi da kallo sannan ta kalli Maryam dake fidda numfashi kadan kadan. Hawaye na zubowa a idon ta.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...