Page 48

273 14 2
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 48

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Kano
A haka suka cigaba da neman Maryam ba dare ba rana, Alkasim kuwa saboda Maryam ya dinga tafiye tafiyen gari gari duk inda yaje yake bada cigiya ko zai samu wanda zai ga Maryam. Wani aiki da ya kai shi Bauchi ranar da ya gama zai dawo kamar da wasa duk inda ya tsaya sai ga nuna picture din Maryam ko akwai wanda Allah zai sa ya ganta, a lokacin ya tsaya a wajen wani mai siyar da lemo a hanya bayan sun gaisa ya nuna masa picture din Maryam, kallon hoton mutumin yai, sai ya shiga shago da sauri ya dauko wata jaka ya mika masa, a zabure Alkasim ya amsa dan ba zai manta ba tare suka siyo jakar, sunje shopping zata makaranta taga jakar tace lallai sai ya siya mata, dan haka yana amsa ya hau budewa yana fadin
"Ina Maryam din a ina take?"

Kai mutumin ya girgiza yace
"Yau kusan wata biyu kenan, da na tsinci jakar nan, anan saboda akwai wata rana wata yarinya tazo tsallaka titi wanda anan wasu suka zo suka kusan kade ta, to bamu sani ba dai tana da rai ko bata da rai suka tafi suka bar ta, sai bayan sun bar wajen naga jakar shine na dauka na ajiye, to kaji a inda na samu jakar."

Wata rumguma Alkasim yayiwa jakar hawaye na zubo fuskar sa yace
"Ina suka yi?"
Hanya ya nuna masa yace
"Amman kila asibiti suka kai ta."

Daga nan ya shiga bin asibitoci wanda a ranar bai koma gida ba sai da ya dada sati akan neman Maryam amman ba Maryam sama ko kasa. Hankalin sa ya tashi domin kuwa yaga samu yaga rashi, a haka ya koma gida cike da damuwa.

****
Zaune yake cike da damuwa a dakin sa, wayar sa ce tayi kara kamar ba zai duba ba, dan rabon sa da waya tin mutuwar Haidar, tin lokacin komai ya fita a ransa sannan ga rashin kanwar sa, mostly ma wayar a kashe take, in bai kashe ba kuwa tana flight mood, janyo wayar yayi yana kallon da sauri ya mike yana kai wayar kunnen sa, wani kuka yaji yana son ya taso masa yace
"Ahmad."

"Ba wani Ahmad ku me yake damun ku ne, daga aure duk kun kashe waya, kai sai kace kai ne kayi aure, na shiga damuwa na rashin samun ku a waya amman nasan wancan dadin aure yasa ya manta dani ya kashe waya....."
Sheshekar kukan da yaji ne yasa yai sauri dauke wayar a kunnen sa ganin wayar nayi yai sauri ya mayar kunnen sa yana fadin
"Alkasim meyake faruwa?"

"Ahmad mun rasa Haidar, Haidar ya tafi ya barmu."
Cike da razani Ahmad ya dago yana fadin
"What? Me kake nufi? Ina ya tafi ya barmu?"

Kai ya hau girgiza yana fadin
"Haidar has died for more than three month."

Wani duhu-duhu Ahmad ya fara gani da kyar ya iya cewa
"kai karya ne Wallahi. Haidar din? Haidar aminina fa, a'ah dan Allah kada kai min wannan wasan Alkasim."

Alkasim yasan za'a rina. Ahmad da Haidar abokai ne tin yarinta sannan suka kara karatu tare matsala daya ba a gari daya suke ba sai kuma da ya samu aiki ya bar kasar amman Ahmad shine aminin sa a ta dalilin haka ya zama abokin Alkasim, dan a da ma haka kawai zai zo yai kwanaki a Kano, a garin su Ahmad Aliyu yai service dan a gidan su ma ya zauna. Cikin nutsuwa ya labartawa Ahmad abinda ya faru.

Tamkar karamin yaro haka Ahmad ya rinka kuka. Har wani zazzabi yaji ya kama shi a lokacin. Ya dan gyara murya yace
"Innalillahi wainn illahir rajiun!"
Abinda ya fada kenan wayar hannun sa ta subuce ta fadi, komawa yayi ya zauna hawaye na bin fuskar sa, Alkasim ma na gefe yana kuka, dan kiran Ahmad ya dawo masa da komai baya. Shi kadai yai jinyar rashin abokin nasa, yana gamawa ya tashi ya fara shirye shiryen barin kasar dan ji yayi ba zai iya kara zama a garin ba.

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now