💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 51By
*MARYAM S INDABAWA**HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Sam bata sauko ba dan a hankali dai nakuda take ita kuma sam bata sani ba za dai taji marar ta ko bayan ta sun rike sai kuma taji ya saki wanda yana sakin ta take bingirewa da bacci da ya tashi kuma zai tsayar da ita daga baccin da take. Ummi na hawa wani ta ganta na bacci wani idon ta biyu haka dai kuma duk tambayar da zatai mata sai ta girgiza kai kawai. Aliyu ma ya kira yafi sau nawa yana tambaya ya jikin ta dan ya kasa samun sukuni har yamma da ya dawo ma a kitchen ya samu Ummi yace
"Ya jikin nata?"
"Da sauki fa ka kwantar da hankalin ka.""Ummi bata ce komai na damun ta ba."
"Bata fada ba meyasa ka tada hankalin ka ne?""Yau ne EDD ta shiyasa nake tunanin ko zata sauka a yau."
"To ai kasan zata iya karawa ko ragewa ko daga yanzu dai zuwa ko da yaushe zamuna tsammani ne."Saman ya kalla sai ya juya ya nufi sama da dan saurin sa. Knocking yai wanda in taji knocking tasan shi ne dan haka ta dauki hijab ta zura tare da mikewa a hankali ta bude masa kofar taja baya a hankali ta koma bakin gado ta zauna, tin da ya shigo yake kallon ta har ta karasa ta zauna. A jikin bango ya jingina yana binta da kallo. Dagowa tayi jin shirun ita yake kalla idon ta, tana gaishe shi da hannu amsawa yayi yana fadin
"Me yake damun ki?"Kai ta girgiza ya karaso ya durkusa a gaban ta yana kallon fuskar ta, kan ta ta rasa kasa dashi dan idon Yaa Haidar ba karamin kwarjini yake mata ba, dan murmushi ya saki yace
"Kin tabbata?"
Kai ta gyada yace
"Good ki sauko muje ki motsa jikin ki."Dagowa tayi da sauri idon ta cike da kwalla yace
"Menene?"
Kai ta girgiza yace
"Ki fada min abinda yake damun ki."Ka ta girgiza yace
"To tashi mu tafi."
A hankal da kyar ta mike ya bude mata kofa ta fita yabi bayan ta. Kitchen suka karasa wajen Ummi tana ganin su tace
"Ah ta sauko?""Gata nan zamuje ta dan tattaka."
"To a dawo lafiya."Suka fita yana fadin
"Kinyi azhkar dai ko?"
Kai ta gyada yace
"Good girl."Dan murmushi ta saki suka fita a gida suna tafe in ta gaji ta tsaya ta huta su cigaba sun yi tafiya mai tsayi ta tsaya ta marairaice idon ta dan yadda taji kafar ta da bayan ta sun rike kallon ta yai yace
"Ya dai?"Hannu ta yafe ta nuna masa bayan ta, yace
"Ko haihuwar ce?"
Ya tambaye ta dan ya manta Maryam bata san wata haihuwa. Kai ta girgiza ta masa alamar ba zata iya tafiya ba. Napep ya tsayar ta shiga ya shiga suka koma gida kan suje gida har kafar ta saki da kan ta ta shige gida ya biya mai napep yai alwala ya wuce masallaci.Tana shiga ta wuce sama da Ummi ma bata kasa alwala ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta tada sallah a zaune tayi tana idarwa wani bacci ya dauke ta. Cikin baccin taji wani a zababen ciwo ta farka tana ciccije baki tare da addu'a a cikin zuciyar ta. A hankali taji ciwon na sauka zuwa can koma taji komai ya lafa.
Ummi ce ta shigo tace
"Maryam sauko kici abinci."
Kai ta girgiza, Ummi ta durkusa tace
"Dan Allah meyake damun ki? Ki fada min ki dauken a matsayin uwa na fada miki."Kai ta kuma girgizawa. Ummi ta kalle ta tace
"To sauko kici abinci."
Nan ma kai ta girgiza. Ummi tace
"Yau fa baki ci komai ba ki fada min ko akwai abinda kike so sai nai miki."
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...