Page 27

342 29 1
                                    

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 27

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

"Muje office!"
Doctor ya fada ya fita. Abbi da Yaa Muhammad suka bi bayan sa. Yan dakin kuwa sai murna suke suna mata sannu Maryam kuwa ba magana sai hawaye dake zuba a idon ta kawai.

Abbi ne zaune shida Yaa Muhammad sai Doctor dake duba file din Maryam. Mikewa yayi yace
"Ina zuwa!"
Sannan ya koma dakin ta. Sallamar su yayi dan su basu waje aka barta ita dashi sai wasu nurses sawa sukai ta mike tayi tafiya sannan suka sa tayi motsi da wasu part din jikin ta, bayan ta gama yace
"Yi min magana Maryam!"

Idon ta ne ya kara cikowa da hawaye sai ta girgiza kai alamar ba zata iya ba. Duk yadda yaso tayi bata iya ba. Har suka gama suka kira Ammi akan abinda zasu iya bata taci wanda Nurse zasu kawo mata yanzun nan. Sannan ya koma office wajen su Abbi.

Zama yayi yai danyi rubuce rubuce sannan ya dago yace
"Kuyi hakuri dan Allah!"
"Ba komai!"

"A gaskiya Maryam ta shiga hatsari sai dai cikin hukuncin Allah, Allah ya kawar da hatsarin wanda halin da ta shiga wani daga shi yake mutuwa wani ya makance wani ya kurmance wani ya bebance wani kuma ya rasa wani bangare na jikin sa kamar rashin tafiya da sauran su. To yanzu daga can nake naje na duba ta Alhandulillah matsalar tata ba wata babba bace domin kuwa ciwon kadan ne dan naga magana ce ta dauke mata kuma insha Allahu zamu daura ta akan magani da yaddar ubangiji in da rabo sai ta warke amman gaskiya ba a fiya warkewa ba."

"Innalillahi wainna illaihir rajun! Alhamdulillah! Allah mungode maka da wannan jarabawar Allah ka bamu ikon cin wannan jarabawar wannan yarinya Allah bata ikon dauka da cinye ta. Amin!"
Abbi ya fada. Yaa Muhammad yace
"Toh Allah yasa a dace!"

Magunguna ya rubuta sannan ya mike yace
"Zan kawo mata maganin yanzu!"
Mikewa su Abbi sukai sukayi masa godiya suka koma daki inda Nurses suka shiga da ita bandaki Yaya Fadima ta taimaka ta gyara ta suka fito ta zauna akan kujera daya daga cikin nurse din tana hada mata abinci dayar kuma tana matsa mata kafafun ta. Maryam kuwa sai bin yan dakin take da kallo kamar bata san su ba.

Gama hadawa tayi ta karaso ta zauna zata bata abincin kai ta dauke, tace
"Haba My sister ki daure kici ko yaya ne?"

Kai ta girgiza. Yaya Fadima ta amsa tace
"Haba dai Kici kinji kanwata."
Dagowa tayi ta kalli Yaya Fadima sannan ta girgiza ka.

Aisha ce tace
"To me kike so?"
Hawayen dake makale a idon ta ne ya zubo ta daga hannu tai mata nuni da cewar Yaa Haidar shi take son ta gani.

Abbi da ya gane me take nufi ya karaso ya kama hannun ta yace
"Kiyi hakuri kinji Mama nah, Aliyu ya tafi inda ba zai dawo ba."
Kuka ta fashe dashi tana girgiza kanta,  Aisha ta rumgume ta tana jijjiga ta.

Ammi ce tace
"Wai Abbi rashin maganar nan fa?"
"Zatayi da yaddar Allah!"

"Toh! Allah ya yadda!"
Haka kememe taki taci abinci,  magani ma kin amsa tayi sai allura da akai mata har da ta bacci dan taki ta daina kuka tin da ta tashi kuka kawai take yi wannan yasa sukai mata allura. Kwana ta uku da farfadowa amman sam bata cin abinci sai karin ruwa kuka kuwa shi ya zaman mata abun yi ko da yaushe. Maryam ta rame sosai sai idanu da hanci da suka fito.

In suka zauna ita da Yaa Alkasim tai ta kuka shima sai kukan baya iya lallashin. Kullum cikin nasiha da lallashi su ake a haka ta kwana ashirin a asibiti wanda a lokacin aka sallame su. Lokacin da ta koma gida komai sai ya dawo mata sabo saboda tina yadda suke rayuwa da Yaa Haidar a lokacin baya wanda kullum suna tare.

Tana zaune a falo hannun ta rike da Kur'ani tana karantawa Ammi na kitchen tana hada mata kunu ko zataji dadin bakin ta. Yaa Alkasim da Yaa Abdullah suna zaune a gefen ta.
Da sauri ta dago sai kuma ta mike tana kallon kofa. Yaa Abdullah ne yace
"Menene?"

MATAR HAIDARWhere stories live. Discover now