💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 37By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
A haka Maryam ta tashi da soyayyar Aliyu, wanda yana gama service ya samu aikin dan haka bai wata wata ba ya siyi filaye ya dankara gini, lokacin da ta shiga SS1 ne Haidar ya fara nunawa Maryam zallar soyayyar da yake mata, wanda a gaban kowa yake kiran ta da *MATAR HAIDAR* babu wanda a lokacin bai san soyayya Maryam da Aliyu ba, makaranta kuwa a sati sai yaje sau biyu sau uku, dan haka ita ji take tamkar ma a gida take, Haidar ya gama koya mata yadda zata so shi da yadda zatai rayuwa dashi, soyayya suke mai tsafta wanda kowa yake sha'awar su.
Tana SS2 tazo hutun second term yana cikin mota yana jiran ta ta fito zasuje shopping, wanda ta fito sanye da doguwar riga, da hijab din ta zuwa gwiwa tai kyau ta karaso tana yamutsa fuska fitowa yai yana fadin
"Menene yake damun *Matar Haidar* ?"Kofa motar ta kama ya bude mata ta shiga ta zauna ya juyo yana kallon ta yace
" *Matar Haidar* "
Dagowa tai tana cije baki yace
"Fada min me yake damun ki?"Hannun sa ta kamo tace
"Yaya tin jiya gefen ciki na yake min ciwo sai naji yana soka min."
"Dai dai ina?"Hannun sa ta kamo ta daura a kan marar ta, tana lumshe ido, murmushi ya dan saki yace
"Baki ga komai ba kuma?"
Baki ta dan turo tace
"Me kenan?"Wajen kunne ta yai da baki sa yace
"Blood."
"Which kind of blood?""Haila."
Ya fada a hankali. Ido ta zaro tace
"Yaya nifa ban fara ba har yanzu kuma ma ni wallahi bana so na fara yanzu.""Why?"
"Ni kawai bana so nafi jin dadi yanzu ba ruwana da wani kazanta."Murmushi yayi yace
"Dole kuma kiyi ba, yarinya ki fara shirya masa daga yanzu zuwa ko da yaushe dan kin girma."
Dagowa tayi ta aika masa da wani kallo, ido ya lumshe yace
"Zaki zautani da wannan idanun naki."Kai ta dauke sai kuma ta dan cije bakin ta tace
"Wallahi Yaya yana damuna ka bani magani."
"Muje daga nan ma biya clinic ko?"Ya tayar da motar suka bar wajen yana fadin
"In kuma abin yazo yanzu ya zaki ji?"
"Yaya Allah bana so ni nafi so after i graduate naga fa yadda wasu ke wahala a school yana bani tsoro ni da ace ba zan nayi ba."Tai maganar cike da damuwa, yace
"Ki rufa mana asiri mana, in bakya yi akwai probability ba zaki haihu ba fa."
"Kai kuma kana son kids ko?""Yes now."
"Shiyasa nake tsoron kar na haifa maka yara ka maida son da kake min kan su.""See dis girl ke har kina da bakin magana, ni dake wa yafi son yara, ni ne ma na fi jin wannan tsoro kar daga kin haihu a daina ji da ni kuma."
Kallon sa tayi tace
"Ba mai kwace maka fada ta a wajen na.""Bare ni, zance musu wannan ita ce duniya ta."
Tai murmushi sai kuma ta jingina da kujera tana fadin
"Yaya ciki na"
"Ko mu fara zuwa clinic din dai?""No muje in mun dawo ma biya."
Haka suka karasa wajen, a ciki ma shi ya dinga dibar mata kayan da zata bukata amman ita ta rasa me yake damun ta, da aka je biya ma fita tayi dan ji tayi wajen gaba daya yai mata zafi, dakyar ta samu take daga kafar ta wajen motoci ta nufa, tana dafe da cikinta cikin tsananin azaba a take jikinta ya hau rawa kaman mejin sanyi sakamakon iskan gurin dake busowa kasancewar ta hada zufa a jikinta, cigaba tayi da tafiya a daddafe, ta kusa da karasawa wajen motar maranta tai wani irin murdawa wanda ya haddasa mata tsala wani kara mai karfi nan tayi baya ji kake tim ta fadi a kasa, a daidai lokacin ya fito ya hangota cikin wani irin masifar firgita Haidar ya kwalla mata kira daga inda yake at once ya nufi gurin da wani mugun gudu, amma koda ya isa gurin sam bata numfashi.
YOU ARE READING
MATAR HAIDAR
Fantasy*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi ra...