001

129 4 1
                                    

*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*

*NA*
*JAMEEY* 

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*Alhamdulilah godiya ta,tabbata ga Allah daya sake bamu aron lokaci inda zamu kasance a cikin littafin Nahiyata Arewa fatan Allah* *yasadamu da alkhairan dake cikin shi,ya rabamu da kowane sharri ameen.*

_Salati da daukaka su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi_ _Muhammad (SAW) da lyalan gidan sa,da sahabbansa masu daraja ameen._

_*The Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.*_

Kasar NIGERIA kasace mai faɗa aji a Nahiyar Africa wadda akema lakabi da *Mother of Afrika* kasace data tara albarkatu kala daban daban kasace wadda takeda bangarori biyu Kudu da Arewa,kowane yanki na wannan Kasa Allah ya azurtasu da arziki kamar noma da kiwo inda Arewacin Kasar ke noman Gyaɗa da Audiga da sauran kayan masarufi na rayuwar yau da kullim kacokam Kasar sun raja'a kan noma dashi suke samun kudin da suke hudda ta yau da gobe.

Bayan samuwar men fetir arzikin kasa ya ru6enya da albarkatu iri iri da ake samu a cikin men fetir,wannan dalilin yasa akayi watsi da halin ko in kula da noma al'umma suka maida akalasar su akan wannan Mai dake cikin Kudancin Kasar

Nigeria tana da Kabilu daban daban manya da kanana manazarta sun hakaito akalla yarukan Kasar sun kai adadin 400 koma sama da haka...Tana dauke da addinai daban daban saidai mafi rinjayen addinin musulunci da chiristian sune addinan da akafiyi bayan yarukan da Kasar ta tara,akwai manyan yaruka dake cin karen su ba babbaka sune manya yaren dake faɗa aji a cikin Kasar ta Nigeria.

*HAUSA,FULANI,IGBO da YORUBA* sune yarinka da sukafi kowane yare rinjaye a cikin wannan Kasa musamman Hausa data kwashe kaso saba'in cikin ɗari da akeji a kasar dama Nahiyar Afrika baki ɗaya banda sasssan duniya da wannan yaren ya karaɗe.

*Kano,Katsina,Gombe,Bauchi,Sokoto,Jigawa sune Jihohin da suke dauke da HAUSA FULANI.*

*Abia,Enugu,Beni,Imo waɗannan Jihohi su kuma duk kabilar IGBO* ne a cikin su,shima babban yare ne dake bugun gaba da wannan Kasa ta Nigeria.
*Lagos,Osun,Oyo,Ondo,Ogun da Ekiti Jihohine na Yoruba* babban yare ne dake a Kudancin Kasar ta Nigeria Kamar yanda tarihi ya nuna Kasar Nigeria ta samo suna daga Flora Louisa Show taga yadace asama Kasar suna  *Niger and Area* saboda babban kogin Neja da ya shiga ta Kasar daga wannan Nigeria ta samu suna a 1897...Kasar Nigeria tana makwaftaka da Kasar Chadi,Benin,Cameron da kuma Nijar.

*BAKASI* kogi ne dake tsakanin Nigeria da Cameron mafi akasarin ruwan yana a cikin yankin Kasar Nigeria,kowa yasa yanda ruwa ke dauke da albarkatu iri daban daban hakan yasa gamayyar kasashen guda biyu kowa ke ganin wannan ruwa mallakin shine,hakan ya kawo sabani iri daban daban har Allah ya kawo mulkin Shugaban Kasa *Olusegun Obasanjo* yasa hannu Bakasi tana kalkashin kulawar Kasar Cameron inda *Kofi Anan* ya zama immediator a tsakanin Kasashen.

Hausa Fulani Kabilune dake zaune a Arewacin Kasar,ta yammacin Kasar Yoruba inda Igbo take a gabashin Kasar.
Tun ana mulkin mallaka na turawan kasar Burtaniya har Allah yasa akaba Nigeria Yancin kanta a shekarata 1 ga watan October 1960...Allah ya azurtamu da shuwagabanni tunda ga prime minister har zuwa yau da muke a mulkin shugaban kasa Bola Ahamd Tinubu..Tarihin Nigeria yanada tsawo nima nadan kawo kadan a takaice,muje zuwa.

_________

*PAGE 1*

Dago fararen idanunshi yayi wanda suke lumshe a koda yaushe kamar mai jin bacci haka idanun suke gasu dara-dara wanda babu alamar wasa ko imani acikinsu kallo daya zai maka ka shiga a hankalinka ko kodan tsara da lafiyarka da rayuwarka wani kallo yayi  mashi yana bude bakin cikin kakkaursar muryarshi ta cikakken namiji wanda karfin samartaka take yawo a cikin jikinshi yace."Jigida fasaman kanshi."Wanda aka kira da Jigida ya ɗago a firgice yana zare idanu alamun razane murya na rabewa yace.
"Ranka shidade Oga wannan aikin na manya ne." Kallon da yayi wanda ya kira da jigida yasa hantar cikin jigida kadawa yana kasa da kanshi ba abunda jikinshi yake sai karma dan tunda yake bai taba kisa ba a nashi iskancin,gashi yau ana sakashi fasa kan wani gani yake ba zai taba iyawa ba maganar Oga ce ta dawo da jigida a cikin natsuwarshi inda yaji Oga yana cewa."Idan nakara yimaka magana zan fasa ƙoƙon kanka Jigida."Ya ida maganar a matukar fusace.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now