043

6 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 43*

Yana isa office din Khalid PA dinsa ta gaishe shi cikin girmamawa kai tsaye ciki ya wuce zaune ya tadda rike da phone yana waya sai sakin smile yakeyi a saman fuskar shi,tsaye yayi yana aikama Khalid wani irin kallo kafin ya isa wajen fridge ya dauki goron ruwa ya dawo ya zauna kan sofa,ya bude murfin yafara shan ruwan a nutse.Almost five minute Khalid nakan waya hakan ba karamin kular da Faruq yai ba kallon Khalid yayi cike da takaici yana cewa."what's kind of this nonses Khalid?ka shanya ni kamar wasu kaya."murmushi ya aika mashi kafin yayi sallama ya yanke kiran yace."ohh i think soyayya ba karya bace ko.?"tsaki Farouk yaja ya kara shan ruwan sa kafin yace."hmm common kaga muje karakani wajen yarinyar nan." Wani kallo Khalid yayi mashi yana girgiza kai yace."bazani ba."da mamaki Faruq ke kallan shi yace."saboda me.?"wani kallo ya watsa mashi kafin yace."bazan iya bata lokacina ba,look Faruq wai kai yaushe zaka zauna da mai son ka karabu da rubish din nan?yarinyar nan fa batasan kanayi ba at all."Jinjina kai Faruq yayi yana cewa."Yes i know yanzun idan na gabatar da kaina fa."dariyan kasan makoshi Khalid yakeyi yace."wama yasani kota fidda gwani."a hankali ya aje robar ruwan hannun sa yace."kada kamanta ba abinda kudi basu iya siye."with suprised in his face Khalid yace."really?"jinjina kai Faruq yayi yace "offcourse so kadaina tinanin akwai abinda zaifi karfin Faruq a duniyar nan." Jinjina kai Khalid yayi yana cewa."Ok best of luck but idan kagama gabatar da kan naka zaka rakani wajen tawa yarinyar."Murmushi Faruq yayi yace."For sure kana son Musriya?is it serious kodai wasa kakeyi."mikewa Khalid yayi yace."Idanun ka zasu baka wannan amsar."daukar key din motar Faruq yayi yai gaba shima tashi yayi yana sakin kayataccen murmushi akan fuskar shi suka fita mota suka shiga sannan sukabar company nin baki daya Khalid ke driving din.....Kamar yanda Ammun Umar Sanda ta fada mashi ta shaidawa magabantan sa batun auren da yakeso anema masa aikam hakan ta kasance zaune suke a sashen mahaifin Jamila su biyu kana ganin su kaga mutanen kirki,basu jima ba Abba ya fito cikeda kamala ya zauna suka gaisa fuska sake ya tarbi bakin nashi aka kawo masu ruwa da kayan motsa baki da fruit after some few minute kawun Umar yai gyaran murya yace."Alhaji nasan bazaka shaidamu ba,mune iyayen Umaru Sanda."cikin jin dadin daya bayyana a kan fuskar Abba yace."masha Allah sannun ku da hanya ya mutanen gida.?"Lafiya lau."suka ce kowa ya kuma yin shiru Bashir wanda yake yaya ga Ammin Umar yace."munzo ne neman alfarma a wajen ka."mamaki ya bayyana a fuskar Abba amman ya boye hakan a zahiri kuwa yace."Allah ya bani ikon yimaku."Ameen."yaci gaba da cewa."Munzo nemawa dan mu neman izinin auren Jamila idan ba damuwa."ɗan shiru Abban yayi kamar mai nazari sai kuma yace."Alhamdulillah saidai ince zai iya zuwa su gana da yarinya har su sansan ta kansu,saboda Umar mutumin kirki ne Allah ya tabbatar mana da alkhairi."Ameen."suka amsa kowa yaji dadin hakan matuka domin suma sun yaba da tarbiyar gidan kwarai da gaske shiru ya kuma gauraye falorn kafin ya kuma cewa."ina fatan duk alkhairin dake cikin wannan tarayyar Allah ya tabbatar ya kademu daga kowa sharri."ameen."basu wani jima ba,sukayi mashi sallama suka tafi.bayan yan mintoci mahaifin ta yasa Umman ta,takira ta zaune ta isketa saman gado tana rubutu gabanta aje da Journals tana dubawa tsaye Umma tayi baki kofa tana mamakin yar tata tace."Ke kam Jamila baki gajiya da aiki,keda Abban ki bai amince ba kike ba kanki wahala,ko baccin kwarai bakya samu ina dalili."sai lokacin Jamila ta ɗago kanta tana smiling a saman fuskarta tace."Umma kamawa tayi wlh ina bin cike ne akan wani case shiyasa kikaga bana samun bacci."Allah ya kyauta amman ki kula kada Abban ki ya gani kinsan dai yace bake ba komawa wannan aikin."marairacewa Jamila tayi kamar marar lafiya tace."insha Allah zai yarda Umma kiyimin addu'a dai."Okk Allah yatabbatar da alkhairi."ameen."cigaba da aikin tayi tace."Kinga aje wannan aikin naki da bai karewa kije Abban ki,na kiran ki."Hakanan Jamila taji faduwar gaba ya saukar mata ta dago ta kalli Umman tace."lafiya Umma.?"kije mana zakiji ai."rufe book din dake gaban ta tayi ta aje Jounarls kafin ta sauko saman gadon ta mike tsaye,Press dinta ta bude ta dauki gyale sannan ta fita da sallama abakinta,ta shigo Palorn,kallo ɗaya yai mata ya maida kanshi kan tv dake aiki a hankali kafin ya amsa mata sallamar ta kasa ta zauna tace."Barka da rana Abba."Yawwa Jamilatu."wasa tafara da yatsun ta da suke dogaye sun sha jan lalle,gyaran murya yayi yace."Nasa akira mani ke dan in sanar dake mihimmiyar magana mai amfani fatan zaki bani aron hankalin ki.?"to Abba."cigaba da cewa yayi."Dazun nan iyayen Umar sukazo neman izinin auren ki,kuma nai masu shine nace bari in sanar maki halin da ake ciki dan haka any time zaki iya ganin Umar yazo fatan zaki karbe shi hannu bibbiyu."wani irin razana da faduwar gaba ya samu mazauni a cikin zuciyar Jamila lokaci ɗaya taji komai ya kwance mata shin wane Umar din?amman ai ba haka tayi da shiba taya zai turo iyayen sa kai tsaye!akan mi zai dinga nuna mata karfin iko!why Umar ke bahaggon mutun....."baki ce komai ba Jamial."ajiyar zuciya ta fesar tace."Abba bansan taya zan fara karbar Umar a matsayin wanda zan...."ya isa Jamila zaki iya kallan idanun sa ki fada masa haka."Rabo da ita Rukayya tafadi ra'ayin ta karko tauyeta."Shiru Umma tayi tana  kallan Jamila ko keftawa batayi,Abba yace."Ki sani Umar mutumin kirki ne sannan shine ya cetoki hannun mugayen mutane,harya sadaki da iyayen ki shin wannan ma ba halacci bane.?"Kanta ya kara sara mata kamar zai bar gangar jikin ta,lokaci ɗaya tafara shavring jin abinda yace."Abba Sanda."Eh ya'ta bazaki dana sanin rayuwa da Umaru ba inada tabbacin hakan."wannan karon shiru kawai tayi tana ganin abinda kamar ba real ba,ya zatayi da Umar Diga taya hakan zata faru bayan tasan akwai kwantacciyar takon saka dake tsakanin Umar Diga da Umar Sanda how?why abubuwa ke zuwar mata a negative...Jin an dafa ta ya katse mata sakar zucin ta,ta kalli Umma dake gaban ta tace."baki ce komai ba ya'ta."wani kwalla taji sun cika mata ido ta rasa mike mata dadi bataji zata iya jayya da mahaifan ta muryar na breaking tace."zabin ku shine nawa."sunji dadin biyayyar ta har cikin ransu Abba yace."Allah yaimaki albarka."ameen."tace a sanyaye sallamar ta sukayi ta koma daki tanajin wani irin yanayi na damuwa a lokaci ɗaya wayar ta,ta dauko tayi dailing number kawar ta Dijja ta kara a kunnen ta saidai not reachable aje wayar tayi tana nazari hawaye na shida ta gefen idon ta....12 pm Privet Jet din su Faruq yai Landing cikin Katsina International Air port,basu jima da isowa ba Driver dinsa Kabir yazo daukar sa as usual any time idan yazo Katsina shike daukar shi,kai tsaye Hotel suka nufa suna isa reception sukayi duk abinda ya kamata suyi sannan suka isa room din da suka kama na yini ɗaya bcs of basu da plains din kwana,hutawa sukayi kafin su kimtsa Kabir ya nuna masu Unguwarsu Jamila basu  wani sha wahala ba aka numa manasa har kofar gidan tsayuwa sukayi baki gate din gidan inda Faruq ke karema gidan kallo yadan ya mutsa fuska kada kafin nan ya sako kafar sa kasa sannan Kabir ya rufe kofar ya koma cikin motar ya zauna sun dauki almost ten minute ba wanda yai yace komai,cikeda kosawa khalid yace."Kagani ko Faruq tun kan kaganta ka kasa cewa komai duk wannan uwar tafiyar da muka kwasa zai tasha a banza kenan.?"fesar da iskar bakin shi yayi yana dallama Khalid wawan kallo yace."kadaina complain Khalid so kake mu faɗa gidan mutane ko me?"Kauda kanshi yayi daga duban Faruq yana jin haushin shi,wani yaro yazo shiga gidan Faruq yakira sa,dawowa yayi ya gaishe su cikeda girmamawa yace."kace ana sallama da Jamila."toh."cewar yaron harya juya zai shiga ciki Khalid yace."Abokina ji mana."juyowa yayi ya dawo yace."Kace inji Umar."tafiya yayi,kallan sa kawai Faruq keyi yace."first time daka kirani da ainihin sunana wow gaskia tafiyan nan ta musamman ce akwai nasara a cikin ta."ya karasa maganar yana murmushi,shiko Khalid sai shan kunu yake yana tabe baki yana karema unguwar kallo like kai kyamar wani abu a cikin ta,duk da kasancewar unguwar bata da makusa mutanen cikin ta kuma sunada rufin asiri daidai gwalgwado ɗaga kafada yayi yace"the hole Faruq ya buge da auren villager gaskia bakayi ba."baice masa komai ba ya cigaba da danna phone din shi.Yaron ya fito yace."Ance ku shigo."gaba yayi yakaisu inda ake saukar da bakibin harabar gidan suka bi da kallo ba wani gidan masu kudi bane amman suna da rufin asiri ba laifi suna shiga wani makimancin falor suka zauna.Itako Jamila tinda aka ce Umar nakira ta hade girar sama data kasa ba alamun annuri a saman fuskar ta.flat shoe din ta ta sakala kasancewar jikin ta sanye take da Abaya milk and veil,a nutse take tafiya tana isa bakin kofar ta samu kanta da faduwar gaba kadan kadan,shiga ciki tayi bakin ta dauke da sallama kanta kasa saboda bata son kallan fuskar sa shiko Faruq tinda ta shogo yake aikin kallan ta,banda sauti ba abinda zuciyar shi keyi ko kiftawa baiyi haka yake aikin kallan ta.Khalid yadan yi murmushin karfin hali yadan bugo Faruq sai lokacin ya dawowa nutsuwar sa,zama tayi daga dan nesa dasu kadan duk ta takura,shiru ya gauraye illahirin dakin ba mai cewa komai miskillanci zakai min kenan?ta furta a kasan zuciyar ta tanajin haushin shi.Khalid yace."barka da gida ranki shidade."sai lokacin ta dago kanta ta kalli Khalid take yai mata wani irin kwarjini ta sauke kanta kasa tana tunanin inda tasan shi."Yawwa,ya hanya.?"ta tambaya cikin sanyin murya."Alhamdulillah."dan satar kallan Faruq yayi da har yanzun baice komai ba sai satar kallan ta da yakeyi beside yana rike da phone din shi kamar mai aiki,sign yai mashi da ido alamun yayi magana."Jamila."ya kira sunan ta kamar maijin tsoron magana."kallan sa tayi wanda yai daidai da haduwar idanin su cikin na juna kowa na kallan dan uwan sa,sun kuyar da kanta tayi tace."Na'am."fesar da iskar bakin sa yayi yace."da farko ina tayaki murnar kubuta da kikayi hannun bata gari."nagode."tace tana dan sakin murmushi."And ina son na...kasa ida maganar yayi saidai aikin kallan ta baki daya yarasa encourage da zaiyi magana tsabar kwarjinin da tai mashi."Am Faruq Umar Faruq."girgiza kanta tayi domin koda bai gabatar da kanshi ba,waye bai son Faruq ba a fadin Kasar baki ɗaya no need ya gabatar mata da kanshi duk da tana mamakin dalilin zuwan su wajen ta cewa tayi."nice to meet you Sir,i hope ba wani problem.?" Daga kai yayi yana cewa."Yeah."ya samu kanshi da furtawa unexpected ta gefen ido yake aikawa Khalid mugun kallo jin yaki magana."let me get you some thing to drink."No kada kiba kanki wahala."cewar Khalid bata jira cewar su ba ta fita zuwa cikin gidan."Amman baka da kirki Khalid even ka gabatar dani kasan dalilin zuwan mu akan mi zakayi shiru." Dariya Khalid yayi yana cewa."ni na aiko ka? I think ur heart is commanding you,so idan zaka sanar mata da kanka ka sanar mata idan bazaka iyaba saidai ka gane tunda kai kasa kanka."kwafa Faruq yayi yanajin bakin cikin kalaman sa a cikin zuciyar sa,shigowa tayi hannun ta dauke da tire ta aje masu drink tace."kusha ruwa."daukar lemon civita tayi ta zuba masu kafin ta koma gefe ta zauna tana mamakin dalilin zuwan Faruq wajen ta,fatan ta Allah yasa ba wani aiki zatai masu ba bcs of Election na matsawo,duk da tasan Abba bazai bari ta kuma aikin ba."hope ba abinda sukai maki.?"ya samu kansa da tambayar ta."Eh bakomai."tace tana cigaba da murza zoben yatsan ta."Can i get ur contact."yeah."mika mata phone din shi iphone 15pro yayi ta sama shi sannan ta mika mashi ya amsa yanajin wani irin dadi har ransa.yana amsa yace."i will give u a call thank you for ur entertaiment."jinjina kanta tayi tana sakin murmushi a saman fuskar ta mikewa sukayi sukai mata sallama sannan suka tafi ta koma ciki tana al'ajabi a ranta.

☆☆☆☆

Fitowar su kenan daga meeting kana ganin su kasan suna cikin farin ciki marar misaltuwa zugar mutanen ta ne zagaye da ita kowa na fadan albarkacin bakin shi."Ranki shidade duk abinda kika umurta angama fiddawa."cewar SA din First Lady.Hajia Aisha Umar Faruq tace"Alright but gobe kufito in time banda African time."angama ranki shidade."da haka suka tafi,da sauran matan governors da sanators dan komawa jihohin su.Hajia Aisha tana shiga side din ta,ita kawarta Hajia Zainab Y Umar matar governor of Katsina wato Her Excellency Hajia Kubrah Yusuf Umar falor suka zauna ta dubi kawar ta tace." inaji ajiki akwai nasara a wannan tafiyan." Jinjina kai Hajia Kubrah tayi tana cewa."kwarai kuwa First lady dagani wannan tafiyan ta musamman ce bakida matsala da Jihata."Thank you friend."cikin kankanin lokaci aka fara jere masu manyan warmers kala kala da kayan abinci da fruit iri iri kallon first lady Hajia Kubrah tayi tana cewa."Ya wajen Faruq.?" Murmushi First lady tayi tana cewa."He's fine,but duk yau ban gan shi ba i think yazo ina cikin meeting."ina ruwan Faruq."murmushi tayi suka fara having lunch.Hajia Hajia Kubrah ta duba agogon hannun ta tace.weather din yau sai a slow yanzun kinga dole sai 4 jet dinmu zai tashi ida  weather din ya daidai ta."Gaskia kam why not kibari sai gobe."ranki shidade i have something to do that's why."Ok hakan nada kyau."cigaba da tattaunawa sukayi ana la'asar driver yakaita Air port,wannan kenan.

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now