094

5 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 94*

Jama'a kowa yayi kokari yayi register mu Samu team ya cika zuwa karshen wata mu fara kwasar romon demoradiya,Kunga dai irin salary din da muke rabawa sunata yi mana Addu'a da sam barka suna fatan Alkairi akan wannan team work kowa yayi receiving alert Yana kwance cikin aminci, bugu da ka'ri kana a gefe da'ya account dinka Yana budewa ka ringa kwasar naira 100k  a hakan ma Idan baka kawo kowa bane zaka Samu 100k Amma idan kayi kokari ka kawo jama'a zaka ringa samun Sama da haka duk da haka fa akwai arias na 600k bayan budewar account dinku da company ta baku Alhamdulillah 🙏💃💃💃 maraba da 52u,godiya ta tabbata ga Allah 52U Alkairi ne💸💸💸💸 🥰🥰🥰💃💃💃💃💃

Contact us via
07034464517
08160508316

Kallonsu Hajja tayi tana cewa." Waye Muhi kuma.?"dan jim Umar yayi sai kuma ya furzar da naunauyen numfashi yana cewa."Wanda yayi kidinafin din Khadija ne Hajjah."wanda yayi kidinafin idan na fahimta shine yayi mata ciki ko.?"kwarai kuwa Hajja kinga ya dawo amman ku barni da shi zanyi maganin shi ne sai na nuna mashi ruwa ba sa'in kwando bane naso ace ina nan ya kawo wannan sakon da yau ba zai kwana a gidan shi ba."girgiza kai Jummala tayi tana cewa."A'a Yaya Umar ban san ka saka kanka a cikin hatsari saboda dani daman ni yawa tazo karshe Muhsin ya gama yi man ila a rayuwa dan Allah karka ce zaka saka kanka a wannan fadan."Wani irin kallon Umar Y yayi mata yana cewa."keko kike da amfani Khadija kuma inason ki sani a kanki ba abinda ba zan yi ba Khadija dan kece rayuwata ke nike so ke nike mafarki da fatan ki zamo matata uwar ƴaƴana ba zan taɓa zabo ido ina kallon wani jahili marar ilimi ya cutar dake ban ɗauki mataki ba a shirye ne nayi fito na fito nida Muhi mudun yace zai dawo a cikin rayuwarki, ko yanzun ba kyaleshi zanyi ba tunda har ya baiyana kanshi sai na nemo shi duk inda yake dan hukunta shi akan cin zarafin da yayi maki."tunda Umar ya furta kalmar uwar yayanshi Jummala bata sake ganin mai ma yake cewa ba sai girgiza mashi kai da take tana ja da baya baya hawaye na zubowa fal a saman fuskarta tana tura hannayen ta cikin bakinta dan kuka yake neman kubce mata tana cewa."Dan Allah Yaya Umar ka rufaman asiri ka dubi maraicina ka tuna bani da uwa bani da uba banda kowa sai Allah sai kuma ku idan kana sona ba tabbata ƙarshen zamana daku yazo dan Momy ba zata taɓa barina ba dan Allah na tuba har ga Allah a bar wannan maganar dan kafi karfina ka fini komai kyau mulki kuma kudi ina kai ina tallaka kamata."Kallon Jummala Umar y yayi yana cewa."Wallahi Khadija inasonki kuma ba zan bar fadin wannan kalma a gareki ba a gaban kowa ma zan faɗa ina sonki ina aurenki Khadija a shirye nike da na ɗauki ko wane kalubale akan soyayyarki,ita soyayya ba ruwanta da nasaba ko kyau balle kudi ni dan Allah nike sonki Khadija, karda kice ba zaki aureni ba saboda wani dalili na daban Khadija idan har kika ce ba zaki aureni ba wallahi zan iya rasa raina."

Kuka kawai Jummala ta fashe dashi tana gurkushewa kasa numfasawa Hajja tayi tana cewa."Duk wanann koke-koken bashi bane Khadija tunda har shi Umaru yace yana sonki da bakinshi ai ba wani abu bane,kuma ta Kubrah duk ba damuwa bace dan ba zata taɓa hana abinda Allah ya ƙaddara ba Khadija kuma mu muna sonki a duk yanda kike Khadija daina kuka kiyi shawara da zuciyarki dan ba zamu so kanmu muyi maki dole ba,idan har kina son Umar to ni zan tsaya maku har aurenku ya tabbata kuma batun wannan yaro Muhi zanyi magana da Yusuf za'a dauki mataki akan shi ban san wannan kukan kinji.?" Taso da ita Rumaisa tayi tana cewa."Haba Khadija dan Allah ki daina kukan nan haka karda kanki yayi ciwo mana,kamar yanda Hajja tace ba za'ayi maki dole ba sai dai nima kaina inasonki da Yayana dan kun dace sosai sai da hukunci yana hannunki Khadija kuma ina maki fatan Allah ya zaba maki alkhari damu baki ɗaya."share hawayenta kawai Jummala tayi dan ita jinsu kawai take tana auna hatsarin da Umar yake kokarin jefa kanshi a kanta ba tare da ya sani ba,tasan waye Muhi ta kuma san irin son da Muhi yake mata daman yace mata komin daren dadewa zai dawo gareta gashi kuma tun ba'a yi nisa ba ya dawo din kamar yanda yace,ita haka tata ƙaddara take haka Allah ya qaddara mata rayuwa da dan fashi dan ta tabbata akanta ba abinda Muhi ba zai ma Umar ba kuma ita bata son wani abu ya samaishi akan ta, numfasawa kawai tana kallonsu tace."Naji duk maganganunku Hajja zanyi tunani kamar yanda kuka buƙata."Murmushi Hajja tayi tana cewa."Yauwa yarinyar kirki ki kwantar da hankalinki da kyau ki natsu kiyi tunani dan nema ma kanki rayuwa mai inganci karda dawowar wanann yaron Muhi ya daga maki hankali karki saka hakan a ranki Khadija kinga dai jego kike karda damuwar ta haifa maki wata matsalar kuma."To in shaa Allah Hajja."Daga haka ta shige room dinta shi kuma Umar magana yayi da su Hajja sosai yasa aka dauke kayan da Muhi ya kawo aka raba ma yan aikin gidan Hajja sannan ya wuce gida.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now