_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 42*
Sanda ne zaune saman tabarma shida mahaifiyar sa suna taba firar duniya cikin kwanciyar hankali Ammu ta kalli Sanda tana cewa."Umaru nifa wannan hukuncin da aka yankewa wannan yaro yana bani tsoro yanzun kana tunanin har Alhaji Ma'azu zai lamunce da wannan hukuncin.?"Dan sosa keyar shi yayi yana lankwasa kanshi a hankali yace."Haba Ammu dolensa ya yarda da hukuncin hukuma ba wanda ya garareta saidai idan ba aikin za'ayi ba."ajiyar zuciya ta fesar tace."kaga yanayin kasar tamu indai mutun nada rufin asiri zai iya taka doka kuma ba abinda za'ayi bare shi attajiri ne bugu da kari kuma yana cikin rigar siyasa."Wannan karan murmushin gefen baki yayi yace."wannan dalilin yasa na nuna masa karfin ikon hukuma natsaya tsayin daka har Kotu ta watsa shi gidan yari,Haba Ammu dame akeson talaka yaji a wannan rayuwar idan yarasa wanda zai bidar masa hakkin sa,jiba kiga yaron nan natafiya da kayan sana'arsa Hafiz ya bige shi da mota sannan ya fito yahau shi da duka hakan bai isaba ya kuma zuwa har gida ya ture masu gini shin waye Hafiz dan kawai yana ɗan gwamma mai neman kujera kuma ɗan Sanata shine zai dinga wulakan ta Jama'a,abin takaici dawowata Katsina na iske cases na yaron nan ba adadi kuma ba abinda aka iya yimasa shiyasa ni kuma kuduri aniyar hukunta shi duk da nasan hakan ba zaima mahaifin sa dadi ba." Numfasawa Ammu tayi tana cewa."Allah yasa hakan yai silar gyaruwar halayen sa."ameen."shiru kowa yayi inda Ammu ke murza gyada amaro tana zubawa cikin wani Vowl Umar yace."Yawwa Ammu inada muhimmiyar magana dake."ture kwanan gaban ta tayi ta maida kaf hankalin ta kanshi tace."inajina Umaru."Sake sosa keyar sa yayi yana maida kansa kasa yace."Ina son kisa su Kawu Ali suje nema mani izinin auren wata yarinya idan ba damuwa."wani irin farin ciki ya lullube Ammu tace."masha Allah,naji dadin wannan albishir naka Umaru tabbas burina zai cika kenan,yar ina ce kagani kana so.?" Sake soke kansa yayi alamun kunya yace"yar jarida ce Jamila."Dan shiru tayi alamun mai nazari sai kuma tace." Jamila yar gidan Alhaji Abubakar mai taki Dan kasuwan nan ko wanda aka ɗauke ."?Eh Ammu." Murmusawa tayi cike da jindadi take cewa."shikenan yau dinnan kuwa zan shidama iyayen naka suje suyi abinda ya dace Allah yasa hakan yafi zama alkhairi."ameen." Shiru kowa yayi a cikin su Ammu ta cigaba da aikin gyadar da takeyi."Sara fa?" Taje wajen Murjanatu." ta gidan Kawu Ali.?"Eh."bai kuma cewa komai ba,kiran sallah akayi ya mike."zanje masallaci."Allah yataimaka saika dawo."Fita yayi ya nufi side dinshi danyin alwalla.
☆☆☆☆
"Wai mi ake jira dashi har yanzun ba'a kauda mana shiba."cewar Alhaji Ma'azu."Mai gida ka kwantar da hankalin ka indai mune sai mun kwatar maka hakkin ka sannan Hafiz bazai kulla sati ba a Prison ba." Furzar da iskan bakinshi Alhaji Ma'azu yayi mai zafin gaske dan cike yake da bakin cikin Sanda yake cewa."Haba Buba taya hakan zatafaru ace da'na ɗaya kwal yana Yari,abinda baka sani ba wannan hatsabibin Dan sandan ya rufe duk hanyar da zanbada cin hancin dan murkushe wannan bahaguwar shari'ar abin takaici." Daga can bangaren Buba yake cewa."ka kwantar da hankalin ka wannan karan sai kudi sunyi amfani wannan shine takon farko da zamu nuna masa karfin mulki yafi na hukuma,ko Muhi?" Ya ida maganar yana kallan Muhi da baice uffan ba."Hakan ya dace sannan akwai hanyoyi da yawa da zamusa Sanda ya shiga tara,har sai ya gwammaci inama kashe shi akayi."Cikin jin dadi Alhaji Ma'azu yace."kamar wa'anne kenan.?" Girgiza kai Muhi yayi yana cewa."Aaa mai gida kaida kasa ido kayi kallo kowane aikina yana da tsari sannan yanada limit kudai ku saki hannu."ba damuwa Muhsin kome kake bukata ga Buba nan."Angama Mai gida."Fita yayi dan yagama fadar abinda yake tunanin zai fada saboda Muhi nada wani abu guda bai cika son yana shiga sabgar da bata dame shi ba koda a gaban shi akeyin komai yana fita mota kirar Roys ya shiga yana danna wayar sa,pcs din Jummala yake kallo yana sakin smile."Khadija na,kin dauka na manta da rayuwarki ko?aaa ina taredake kina cikin zuciya ta kuma soon zanzo ganin lafiyarki data da'na."kiss yasakarma screen din wayar daidai Buba ya fito daga cikin gidan shima shiga yayi driver yajasu suka tafi,wannan kenan.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.