_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 4*
_NIGER STATE_
Kimamin mako biyu zuwa ukku yan sanda jihar suna aiki tuƙuru dan gano wa'anda suka kashe Comissionern yan sanda ta jihar Alhaji Adamu,inda aka wallafa ragamar aikin ga Jami'in tsaro kuma mai kishin kasar shi UMAR SANDA...UMAR SANDA ya kasance matashin saurayi wanda akalla zaiyi shekaru talatin da biyar da haihuwa kyakkyawane kana ganin shi kasan ɗan asalin Nahiyar Arewa ne aiki yakai shi Nahiyar ta kudancin su a Jihar ta Niger..Umar wanda akema laƙabi da Sanda ya kasance baban ɗan sanda ne wanda yake taka roll din ACP 2 daga CP Sai ACP sai shi matsayi na ukku kenan a cikin hukumar..Ya kasance saurayi domin bai taba aure ba amman hakan bai hanashi nutsuwa ba gami da kamewa,kamala, haiba,kwarjini da tarin farin jini ako ina badan komai ba sai dan shidin mai yawan kamanta gaskiane.
Sanda haifaffen dan asalin Jihar Katsina ne wanda aiki ya rabashi da tashi Jihar sannan ya zauna jahohi da dama domin aikin force ya gaji haka,Farine sannan yanada makimanta idanu wanda suka dace da halittarshi sai dai shidin matsakaicine mai cikar damtse,wannan kadan daga cikin tarin UMAR S UMAR wanda yake bearing da Umar S Umar inda jama'a ke kiran shi da Sanda..Tunda aka kashe shugaban yan sandar jahar hankalin Sanda bai kara kwanciya ba kullin aiki suke ba dare ba rana,hakan yasa suka kai case din zuwa ga ofishin sadarwa ta kasa domin ayi tracking wayar shugaban tasu kasancewar ta babbar waya kila ta wannan hanyar za'a kama masu laifin,da haka hankalin Umar ya dan kwanta ganin anci gaba da aikin gadan gadan.
☆☆☆☆
"Umar ina zamuje muketa ratsa uban jeji haka."?Cewar Jamila takema abokin aikinta tambayar cikin rauni da ɗan fargaba atareda ita, murmusawa Umar yayi yana cewa."Jamila rugar mutanen nan akwai tafiya sannan yazama dole muje domin muji halin da suke ciki kinga lamarin nan akwai firgitarwa."Ya ida maganar cikin tsantsar tausayi a saman fuskar shi zuwa ruhin shi..Umar Y Umar kenan kamilallan ɗan jarida wanda yasan makamar aikin shi,baya tsoron faɗar gaskia ako ina sannan kowane lokaci shirye yake dan kare martaba da darajar aikin shi saboda shidin ba makwadaici bane,Umar ɗan gwagwarmayane duk girman waje da hatsarin sa zai iya jure shigar shi dan kwatarwa talakawa hakkin su musamman idan yasan dauko rahota zai kawo masalaha a cikin halin da al'umma ta tsinci kanta a ciki..Umar ya kasance babbane a gidan Jarida na Hikima Trust sannan suna da Hikima Station Television wanda Jamila ke kula da mafi akasarin programs din inda take gabatar da shirin Tafaru takare,inda shi kuma ke Kula da fanni Radio Station yanayin shirin Karta kwana sai dai shine shugaban fannin shirye shirye da gabatarwa da masana'antar Hikima Journal and Station Channel kuma aikin su yana kalkashin Federal kowace Jiha ana turasi domin gudanar da nasu aikin.
tafiya mai nisan gaske sukayi sannan suka fara hangen bukkokin na ruga Hu6agge dake cikin Jigar Kano,Wani waje suka aje motar su sannan suka idasa ciki sanadiyar sahara data fara rike masu tayar motar su..Suna isa sukaga jama'ar rugar cikeda damuwa fuskokin su duk sun nuna hakan,banda tarin rakuma ba abindake yawo a cikin garkunan jama'ar kauyen ko baka tambaya ba kasan sudin Buzaye ne..Wajen mai gari suka sauka akai masu iso bayan sun gaisa da mai garin wanda suke kira Jabiru yasa aka karramasu a nutse yake nazartar, numfasawa Umar yayi yana cewa."Ranka shidade nidai sunana Umar Yusuf Umar ma'aikaci na Jarida tareda abokiyar aikina Jamila Abubakar,munzo ne domin mu jajanta maku halin da kuka tsinci kanku sannan muji halin da ake ciki a halin yanzun."Sauke ajiyar yayi domin yanayin shi kadai ya nuna farin cikin dayaji,jin abinda suke tafe dashi cewa yayi.
"Madalla Malan Umaru munji dadin wannan ziyarar domin tunda lamarin nan ya auku damu ba wanda ya waiwayemu ashe dai ansan damu a cikin wannan Nahiyar tamu harma da Kasar mu baki ɗaya sai dai muna cikin taraddadi musamman yanda ya'yan mu suka afka a cikin wannan musibar ta kamen mutane yaran wannan rugar tamu su biyar ke wajen su akwai Nura sai Lantana,Halima, Saude sai karamar su Jummala kaga dole muyi kuka domin bamuda kudin da suka bukata kuma sun shaida mana matukar muka saka Jami'an tsaro a ciki bako shakka zasu kashe mana iyalin mu."Kafe kayan aikin su sukayi a jikin su ba lallai ka gane ana fira dakai ba duk da sun shaidama mai garin aikin da sukeyi, amman basu nuna wata alama da zan gane daukar shi video suke ba,cikin jimami Jamila ta numfasa tana cewa."Baba har nawa suka bukata sannan kana ganin kin fadawa Jami'an tsaro ba,babban hatsari bane.?" Numfasawa yayi yana kallon Jamila da kyau kamar yasan video suke mashi yana cewa."Kayyah baiwar Allah million shabiyar ga kowane rai ina mukaga wadan nan makudan kudade har million saba'in da biyar.?"Ya ida maganar yana sakin kuka gwanin tausayi lamarin...share zufar da ta keto mashi a goshi Umar Y yayi yana kallon maigari yace."Yanzun Alhaji kadaina kuka addu'a itace mafita sannan insha Allah zamuyi iya kokarin mu dan ganin hukuma tasa hannu kuma ba tare da kun rasa ya'yan kuba,duk da a jihar Kaduna lamarin ya auku saidai za'ayi iyakar kokari ku daina damuwa sannan ayawaita addu'a." Share hawayen yayi yana cewa."Insha Allah munayi, addu'a kam ba dare ba rana." Jinjina kai yayi yana cewa."Ko zamu iya ganawa da sauran iyalan da wannan iftila'in ya afaka dasu?" Ɗaga kai yayi yana cewa."Kwarai kuwa."Haka yasa aka kirawo su ,sukai masu jaje sannan sukai fira dasu har ihisani sukayi masu,har sun tashi zasu tafi cikin wani gida aka rafka uban ihu da sauri jama'ar wajen sukayi cikin gidan musamman mata wata baiwar Allah ce keta faman nakuda shine ta saki ihu tsabar azabtuwa ga garin su ko abin hawa babu a rude Umar yace a daukota sukaita cikin gari.A gaggauce suka sata a amallanke har gaban motar su Jamila ganin idan sukace sai sun shiga cikin alƙarya zasu iya rasa ranta,shiyasa suka tsaya wani makimancin gari dandai yafi nasu alkarya rigi rigi aka kaita bayan ta farfado saidai abin takaicin ko nefa basu dashi a asibitin gashi ba likitoci hakama kayan aiki ran su Umar ya sosu ainun,ganin zasu bata lokacin su dan dole sukayi cikin gari da ita aka karbi haihuwar da kyal ta haihu cikin ya'ya biyu saidai guda ya koma,bayan an sallamesu Umar ya maidasu har gida sannan suka kama hanyar tafiya gida.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.