021

10 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 21*

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un tana magance masiba,aikata alkhairi yafi komai riba arayuwa,karatun alkur'ani yana sanyaya zuciya a lokacin data kuntata."Maida kallan sa yayi a kanta jin abinda take yana cewa."Ita fa cin amana.?" Numfasawa tayi tana girgiza mashi kai tana cewa."Zato zunubi ne koda ya kasance gaskia."Kallan ta kawai yayi baice komai ba can ya ajiye system din dake gabanshi numfasawa tayi tana cewa."Masu imani su kadai ke cika alkawali."numfasawa yayi yana cewa."Mikike nufi.?" Firzar da naunauyen numfashi tayi tana cewa."Ka taimaka ka maidani wajen iyayena."girgiza kai yayi yana cewa."Kin saba yarjejeniya bazan iyaba Sanda yazo ya maidaki." Kuka ta fashe dashi tana cewa."Wlh bantaba waya da Umar ba asalima ba wata alaka a tsakanin mu." Dan Ɗagowa yayi yana kallonta can ya taɓe baki yana cewa."Kiran waya a boye kina ganin za'a iya kamani dan kawai na daukeki?Ko kina tunanin hakan halina ne daukar mutune.?" Share hawayenta tayi da bayan hannunta tana cewa."Ban san kaba asalima bantaba ganin ka ba,amman zaman da nayi da kai nagano kyawawan dabi'unka anso ka keta haddina amman kaki saboda darajar da Allah yaimani kake dubawa harka kimantani,zaman da nayi dakai naga kalan taimakon da kakeyi a inda ba'ayi zato ba,a zahiri dayawan mutane sunayi maka kallan mutumin banza...."Har ke.?" Katseta yayi yana jafa mata tambayar gami da kafeta da manyan dara-daran idanunshi,sauke numfashi tayi yana yin ƙasa da kanta dan bata iya jurar irin kallon da yake mata,wasa ta fara da yatsun hannunta tana cewa."Kwarai kuwa har ni." Murmushi ya saki yana cewa."Yanzun fa.?"

Girgiza mashi kai tayi tana cewa."Am so confused."Why."slowly yayi tambayar,a hankali ta fara cewa."Some times kana dabi'un mutan nan kwarai wani lokacin sai a hankali amma....ɗaga mata hannu mata yayi ba tare da ya batar ta karasa maganar ba yana cewa."Wane bangare nafi rinjaya.?" Ware mashi idanu tayi tana yarfa hannayenta tana cewa."I don't know." Numfasawa yayi yana cewa."Okay you can analyse about my behaviour i think zaki sakani a inda na dace." Marairaice mashi fuska tayi tana cewa."Dan Allah..."Kada kice komai matsalata ɗaya bansan maci amana."A razane take kallansa numfasawa tayi tana cewa."Hakan ma cin amana ne.?" Gyaɗa mata kai yayi yana cewa."Kullin saina gwadaki,kina cikin jarabawa ta kala kala,kisani duk abinda zakiyi nasani Jamila bakisan matsayinki agareni ba inaga shiyasa kikeso kici amanata."Karufamin asiri ka...daura hannunshi saman lips dinshi yayi yana cewa."Sheet you can go."Kukan zuci tahau yi har ta koma inda ake tsaron ta tagumi ta buga kamar marainiya."Nashiga ukkuna,wace irin rayuwa ce wannan,minayi maku zaku dinga tsareni,kubarni inkoma wajen iyayena,miyasa haka ke faruwa dani."Kuka ta saki mai sauti sai kuma tayi shiru kamar zararra."Sanda ka zama kaddarata akanka anki sakina miyasa ko yaushe kaike kawomin cikas,aikina ananma duk kaine why Sanda i hate you.!"Wannan karan kukan marar sauti takeyi zuciyar ta na kuna..Ashe haka mutane keji idan akayi garkuwa dasu,yanzun inajin kaina cikin bala'i inaga wa'anda ake zalinta,baci basha basu da wani yanci,kwarani ban rasa komi ba takurewa tayi ta hada kai da guiwa da haka baccin wahala ya kwashe ta.

☆☆☆☆

"Zaki tashi ko sai ranki yai mugun baci."Ba inda zanje."Harara ta wurgama Ba'ba Ladidi tana murguɗa baki kama baki Ba'ba Ladidi tayi cikin masifa ta fara cewa."Allah ya wadaran naka ya lalace wallahi Hannatu kifita idona in rufe tun muna shaidar juna." Turo baki gaba hannu tayi tana cewa."Wai Baba minayi maki daga ina wakata saiki kama dukana wlh nagaji da wulakancin da kike mani a gidan ubana dan kawai kinga Yayana bai nan."Dan ubanki sai na koya maki zama,kuma Ubaidu ba zai taba dawowa ba ai shike daure maki kike iskanci son ranki."Cigaba da dukan Hanne tayi tana tsinarta,tashi Hannatu tayi tana kama kuhu tana cewa Ba'ba."Kada ki kuma dukana zan rama wlh jiya ba yau ba." Sake kai mata wata bulalar tayi tana cewa."Saiki rama marar kunya mai hali irin na uwar ta."Kada ki kuma dukan ta,kyawun ɗa ya gaji iyayen shi." Shigowar Ubaidu Kenan ya tadda Ba'ba Ladidi tana bugar mashi kanwa,kuka Hannatu ta fashe dashi tana yin wajen Ubaidu cikin kukan take cewa."Yayana nayi kewar ka."Rungume ta yayi yana lallashin ta,kukan ta na kona mashi zuciya,cikin takaici yake cewa."Daina kuka kanwata nadawo gareki bazan taba bari rayuwar ki ta tagayyara ba."Kukan ta cigaba dayi tana cewa."jibi yanda jikina ya koma yaya dan Allah ka zauna dani banson kana nisa." Firzar da naunauyen numfashi yayi yana cewa."Shikenan bazan kuma fita ba kinji.?"gyaɗa mashi kai tayi alamun to kamai baki Ba'ba Ladidi tayi tana cewa."Eyeh Ubaidu ni zaka gayama magana wato halin shaye shayen za'a nuna mani da dabanci kome." Cike da rashin kunya Hannatu take cewa."Dan uwana ba dan shaye shaye bane kuma ba dan daba bane." Cikin ihu Ubaidu yake nuna Ba'ba da yatsa yana cewa."Baba ni kike cewa haka?bayan kece silar gurbacewar tarbiya ta,shine kike faɗa mani haka?kisa aranki bakiga komi ba a harkar dabanci,ko kin manta Uban Daba ake kirana.?"Jan hannun Hannatu yayi suka shige daki ranshi na kuna."Yaya kwanakin da kayi baka tare dani na zama marainiya." Girgiza mata kai yayi yana cewa."Kidaina faɗan haka,ke jaruma ce kanwata bazata zama marainiya ba,kedin mai karfin zuciya ce"Ya jima yana karfafama Hannatu kwarin guiwa kafin ya fita sakamakon kiran da akai mashi a waya,shima da kyal tabari ya tafi a waje ya iske aminin nashi."Kure ya ake ciki.?"Uban daba rasaka tamkar rasa jigone a gareni,sunyi amfani damu sun yardamu cikin kwandon shara,bazamu lamunta ba." Wani kallo Ubaidu yake ma Kure can ya numfasa yana cewa."Kamarya ban fahimceka ba." Cikin takaici Kure yake cigaba da cewa."Sun barku cikin cell basuyi tunanin fitar daku ba." Cike da mamaki Ubaidu yake cema Kure."Waye ya fitar damu idan basu ba?kaga ba lallai kasan sanda zasusa a sakemu ba suna da alfarma." Girgiza kai Kure yayi yana cewa."Basu bane kayarda dani asalima korar karr sukai mana musamman Tahir."Sake kallanshi yayi cike da son jin waye ya fiddosu yake cewa."wa ya fitar damu.?" Ƙasa da kanshi Kure yayi yana cewa."Umar Diga." Dan shiru Ubaidu yayi yana mamakin yanda Diga ya fiddosu bayan ba irin nasihar da Diga bai masu ba akan sun bar bangar siyasa daga karshe ya taitarasu ya watsar wanda suka yarda dasu suke ma banga sune suka kasa yi masu rana sai wanda suka juya ma baya? Numfasawa kawai yayi yana cewa."Ya dace mugode masa."Gaskia kam amman kasan ganin sa aikine amman yace idan muna neman alfarma zai taimaka mana."Saka hannun sa yayi cikin aljihu yace."kira mani shi inason in gode mashi."Kiran shi yayi saidai bai dauka ba har kusan kira hudu no answer, murmusawa Ubaidu yayi yana cewa."Nasani bazai dauka ba,saboda bai bukatar sake magana dani sannan bai bukatar godiya." Jinjina kai Kure yayi yana cewa."Shikenan,ya zama dole mu sake sabon taku akan wannan tafiyar." Jinjina kai Kure yayi yana cewa."Wannan shine tanan zamu kwatar ma kanmu yanci amman wlh sai mun dauki fansa akan Jigiri da mutanen sa."Aje yake dole su ɗanɗanu kudar su."Haiyyah Oga Uban daba nawa ina alfahari dakai nawa."Rungume juna sukayi suna shekewa da mahaukaciyar dariya kamar mararsa hankali.

☆☆☆☆

"Wata sabon gani Faruq Umar Faruq."Murmushi dauke a fuskar Faruq,ya cire glass din idon shi ya maida kallan shi kan Sanda yace."Ina gefe my man ya aiki.?" Firzar da naunauyen numfashi Sanda yayi yana cewa."Alhamdulillah,yaushe ka sauka kasar.?"Najima gaskia i think kana Niger?." Ɗaga kai Sanda yayi yana cewa."yeah but aiki ya juyo dani nan  kasan yanayin aikin mu." Murmushi Faruq ya saki yana cewa."Sanda problem kai dai kana son aikin nan gashi Allah ya cika maka burinka."Hmmm Faruq kenan,kaifa ya aikin.?" Girgiza kai Faruq yayi yana cewa."Ba yanzun ba aiki sai masu iyali."Wannan karan dariya Sanda yayi."kai ko a class komai naka saikasa wasa har yanzun baka sauyaba." Dan taɓe baki Faruq yayi yana cewa."Manta kawai, ya labari.?"Cofee cup ta aje masu daketa faman tiriri da kamshi a saman table din dake gaban su."Yallabai barka da hutawa."yawwa."cewar Faruq ba."Kamar kullin ba abinda ya sauya saidai soon zanyi suprise dinka."Cewar Sanda yakai hannu ya dauki coffee ya dan kurba kadan.Murmushi Faruq yayi yana cewa."kamar da gaske in gani a kasa kadauka yanda kaitayi mana game dinka last time yanzun ma hakane,impossible."Okay you will see."Like serious." Ɗaga mashi kai Sanda yayi yana gyara zamanshi yana kallon Faruq da kyau yana cewa."Nayi waya da Mummy ashe aurenka da Ramlat ya kusa."Da mamaki Faruq ke kallan Umar Sanda jin abinda yace,duk da yasan yanada kyakkyawar alaka da kowa nashi kamar yanda shima baida shamaki da komai na Sanda."Faruq are you ok.?" Numfasawa Faruq yayi yana girgiza kai yana cewa."Am ok am kasan wani abu wai ya maganar issue din Kiddinapers din nan.?"Aje cup din hannun shi Sanda yayi."Alhamdulillah komai na sauki." Allah yataimaka lamarin nan sai addu'a Allah ya shige maku a gaba."Ameen."Shiru ya gauraye wajen kowa da abinda yake sakawa a ran shi."Ansa bikin kenan.?"My Man."Faruq ya kira Sanda cike da kosawa da yake haka suke cema junan su."Yes." Dan tsaki karami Faruq yayi yana cewa."Pls we talk later about this issue but an saki yar jaridar nan kuwa.?" Firzar da naunauyen ajiyar zuciya Sanda yayi yana cewa."Aaa ana fafatawa dai,dagani bawai actual kiddinerp bane kawai akwai dalilin kama ta shiyasa."

Kamarya mi zasuyi mata da suka tsareta idan ba kudi suke bukata ba,mike faruwa har haka!Azuci Faruq keta tufka da warwara."mike damunka naga ka sauya at ones any problem.?" Girgiza kai Faruq yayi yana cewa."No ina mamakin yanda za'a kama mutun badan kudiba."numfasawa Sanda yayi yana cewa."Gaskia kam lamarin nan na damuna." Cike da damuwa Faruq yace."Am scared."Come on anything will be ok insha Allah haba my man tsoro ba naka bane."Nauyayyiyar ajiyar zuciya ya shide."okay am try by the gracs of God."You know her.?" Sanda ya jefoma Faruq tambayar yana  kafe shi da ido,shiru Faruq yayi yarasa mi zaicema Umar bcs sunsan sirrin junan su,duk da sukan jima basu haduba saidai hakan bai hana suyi amincin suba,saidai tunda har Mummy ta sanarma Sanda za'ayi baikon Faruq da Ramlat bazai taba goyon bayan sa akan zabin sa ba,zai goyi bayan su Fulani,Wannan dalilin zaisa yaima Sanda hiding komai..."Faruq." Sanda yace yana dafa kafadar sa."Nothing" cewar Faruq yana numfasawa."Okay shine kadamu da ita har haka i think she's your friend.?"No kawai abin ke damuna bcs she's Journerlist suna iya halakata that's why." Murmusawa Sanda yayi yana cewa."Kaidaina wannan tunanin hakan bazai taba faruwa ba,Jamila zata dawo cikin aminci insha Allah promise."Wannan karan mikewa sukayi baki ɗayan su,suka fito tare cikin aminci da kamala fuskokin su dauke da annuri har bakin mota Sanda ya rako Faruq, guard din shi ya bude mashi back seat ya shiga sannan ya kuma kallan Sanda."My Man gobe zan koma gida,komi kenan let me know kasan halin mutumin naka am so busy.""Okay my regard to Fulani."jinjina kai yayi alamun amsa."What about Uncle I?"He's came back last week."Special regard to him,zan shigo idan nasamu time."Zasuji."Musabaha suka sake a hankali Kabir yafara jan mota in slow motion."And Jamilas issue pls kasanar dani idan ansake ta."Okay."Da haka suka fita Head Quater din sukafara tafiya a tsanake,shi ko Sanda komawa yayi office yana mamakin Faruq da yake masa hiding issue din Ramlat yarasa mi yasa bai sonta almost 10yrs tana son shi amman komai yaki tafiya daidai,cikeda da tausayinta ya cigaba da aikin shi wannan kenan.

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now