_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 101*
Jama'a kowa yayi kokari yayi register mu Samu team ya cika zuwa karshen wata mu fara kwasar romon demoradiya,Kunga dai irin salary din da muke rabawa sunata yi mana Addu'a da sam barka suna fatan Alkairi akan wannan team work kowa yayi receiving alert Yana kwance cikin aminci, bugu da ka'ri kana a gefe da'ya account dinka Yana budewa ka ringa kwasar naira 100k a hakan ma Idan baka kawo kowa bane zaka Samu 100k Amma idan kayi kokari ka kawo jama'a zaka ringa samun Sama da haka duk da haka fa akwai arias na 600k bayan budewar account dinku da company ta baku Alhamdulillah 🙏💃💃💃 maraba da 52u,godiya ta tabbata ga Allah 52U Alkairi ne💸💸💸💸 🥰🥰🥰💃💃💃💃💃
Contact us via
07034464517
08160508316"Yau zan samar maku waye UMAR Fatah UMAR sannan miyasa na dauke Jamila miye dalilin dayasa na ajeta wajena duk da ban nema kudin fansa ba."d'an numfasawa Umar Diga yayi yana sake fesar da iskan cikin bakin shi mai zafin gaske yayin da idanunsa suka rine kamar barkono cikin kankanin lokaci, ga jikinsa yayi masa sanyi matukar gaske sake gyara zamansa yayi yana facing din Baba yaci gaba da cewa.
_LABARI_
Sunana Umar Abdulfatah Umar Ni haifaffan d'an rugar Fa'di sanka ne daga cikin karamar hukumar Kankia ta Jihar Katsina, tun da ALLAH yasa na taso a rugar mu nakasance yaro ne ni mai hazaka da kwazo Hakan yasa mahaifina ya dauki son duniya ya dauraman kasancewar ni kadai mahaifiyata ta haifa banfi shekara bakwai a duniya ba ALLAH yai mata cikawa mahaifina ya shiga cikin tashin hankali Wanda bai taba tsintar kanshi a cikin shi ba, Ni kaina da bani da wani cikakken wayo na rasa Mahaifiyabta saida maraicin ta yai tasiri a gareni,Gidan mu gida ne da yake cike da Yan ubanci 'yan uwana basu kaunata saboda sun ga kulawa da mahaifina ke bani wannan dalilin yasa suka dauki Karan tsana suka dauramin duk da kasancewar Ni ne karami a cikin su.Mahaifina Malamin ne na addinin musulunci yana da almajirai a gidan sa yana basu karatun addini wannan dalilin yasa muka tashi Muna karatu a gidan mu...matan malan ukku Mahaifiya ta Aishatu itace babbar matar sa sai Aminatu itace matarsa ta biyu Kuma kusan itace uwar Ya'yan sa sai matarsa ta ukku Khadijatu, Ya'yan mahaifina Ashrin a duniya Kuma nine cikon na ashrin din, malan ya auri mahaifiyata tun auren Saurayi da budurwa yake tare da ita zama suke na amana ta mutunta juna saidai tun da aure ta Bata taba ko da 'batan wata a gidan sa ba saidai suka dauki sama da shekara goma da aure amma ALLAH bai nufesa da samun haihuwa ba saidai Hakan baisa malan ya nuna rashin Jin dadin sa ba, saidai danginsa suka tiso mahaifiyata a gaba suna mata gorin rashin haihuwa suna kiranta da juya musamman yayar sa Baba Hinde tafi daukar lamarin da zafi kasancewar ita ce matsayin Mahaifiya ga malan saboda iyayen su sunjima da rasuwa tun kan malan yasan zaiyi aure ALLAH yaima iyayensa rasuwa,tun da dangin malan suka tsiro da maganar rashin haihuwa hankalin iyayena bai Kara kwanciya ba duk da a lokacin ba wani cigaba oe akwai ba bare suje asibiti domin su san inda matsalar take duk da mahaifina ba ma'abocin son zuwa asibiti bane yafi ganewa idan mutun bai lafiya yayi masa rubutu ya basa yasha Hakan ya kasance kullin cigaba da ne ma masu taimako yakeyi shida mahaifiyata fatan sa yaga ya samu magaji kamar yanda Yan uwansa ke fata haka dai rayuwa taci gaba da tafiya haihuwa Shiru ALLAH bai nufesa da samun karuwa wasa wasa saida suka kai shekaru goma sha ukku da aure amma basu haihu ba,Baba Hinde ta hurowa malan wuta a dole saiya kara aure ba duk yanda yaso ya nunawa Baba Hinde lafiyan su lokaci ne baiba ta gaza fahimta dan dole Saida tasa yayi sabon aure ta hadasa da Yar uwarsa Baba Aminatu Ya'ya maza suke da ita,tunda ALLAH yasa Baba Amina ta auri mahaifina ba'a Kara samun kwanciyar hankali ba a gidan mu kullun cikin fitina ake, Kuma ba mai ruro wutar sai Baba Hinde haka akaita rayuwa, har ALLAH ya albarkaci Baba Amina da samun ciki, bakaramin farin ciki suka shiga ba dukkan y'an uwan malan suka dauki son duniya suka daurama cikin Amina kullin cikin gargadin Umma suke akan ta kulla da Amina Kada ta cutar da ita,Hakan da sukeyi mata kuwa yana Sosa mata rai saidai bata taba nunawa ba,itace take komai a gidan daidai da ruwa idan Baba Amina ta nema ita ke bata shi koman dare kuwa ko bacci isashshe Bata samun damar yi duk ranar da ta bukaci wani abu batayi mata a ranar saita hadu da fushin Baba Hinde, ba karamin wulakanci zatayi mata ba, akwai wata rana da ta zama rana mafi Muni a wajen Umma ta ranar da aka tashi ciwon ciki ya kama Baba Amina duk da Umma na tare da ita tana bata magani duk ta shiga tashin hankali ganin mawuyacin halin da take ciki Batasan sadda ta ruga gidan Ba'ba Hinde ba ta gaya mata halin da Amina ke ciki kusan a tare suka iso wajen Baba Amina"mi kika bata taci? Anya ba so kike ki kashe mana ita ba saboda kina bakin ciki ta samu ciki ke ko baki da wani ciki saina Kashi idan wani abu ya samu cikin nan sai nayi ajalin ki Aisha."kuka Umma keyi tana."kiyarda dani Ba'ba wlh ba abun da nayima Amina kema kinsan ba zan iya cutar da ita ba Kada ki manta jinin malan jinina ne,wlh tashi tayi da ciwon cikin nan."Yi mani shiru nakira wai ina Fatahun ya tafi ne yabar mace Mai juna biyu sakaka hannun makiyan ta saura a halaka mana ita."sadda kanta Umma tayi taci gaba da kuka a hankali tace."yaje Kasuwa yayo mata siyayya tace tana son cin tsarabar kasuwa shine yace bari yaje ya kawo mata."Wani irin kallon tsana Hinde ta auna ma Aisha tace."shine yana fita cikin nata ya fara ciwo kenan?kedai anyi mayyar yarinya kika kuskura wani abu ya sameta sai kinyi danasani mayyya Kawai."ba karamin bakin ciki bane ya turnike zuciyar Aishatu ba ita dai ta gaji da abun da dangin mijinta keyi mata,su kira mayya ita dai tasan kaf danginta ba maye amma Babban gorin da suke yawan yi mata kenan....ihun da Aminatu ya buga ne ya dawo dasu hankalin su sukayi kanta saidai bata numfashi sai jinin dake faman fita daga jikinta a gigice Hinde ta kurma ihu tayi waje tana Azo a taimaka mata Aishatu zata cinye Amina,da sauri kanin malan Baba Jafaru ya shigo cikin gidan saidai zuwa yanzun Batasan inda hankalin ta yake ba,da gudu Umma ta tafi Kiran unguwar zoma Koda suka iso ta iske halin da take ciki tasan cewar ta rasa cikin jikinta,ruwa ta yayyafa mata ta farfado sannan ta taimaka mata ta gyarata,tace."ta rasa cikin jikinta Amma idan tayi wanka na kwana ukku zuwa sati zataji saukin jikinta, ku daina da'ga hankalin ku ba Wani abu bane ALLAH zai sake bata Wani rabon."mikewa Hinde tayi ta faurawa Aisha mari tahau jibgarta tana."Taya wannan mayyar zata bari Fatahu ya samu karuwar Ya'ya ita bata haihun ba yanzun kuma ta fara cinye jinjirin da baiji bai gani ba har saida akayi barin shi,ba karamin dukane sukayima Aisha ba dakyal unguwar zomar ta anshi Aisha hannun Hinde tace."Haba Hindatu kefa uwace akan mi zaki dauki alhakin baiwar Allah nidai nasan Aisha bata maita Kuma barin nan fa ba akan Amina aka fara ba,kuyi hakuri mana." Yanzun nagane dalilin dayasa taje ta kiraka domin ku karasa d'an ko? Shiyasa kike goya mata baya Ashe."? mamaki da tsoron lamarin Baba Hinde ya gama kama unguwar zomar mikewa tayi taci gaba da cewa." Kada ki jefeni da sharri Hinde Amma ina so kisa tsoron ALLAH a ranki,irin cin kashin da kike ma Aisha yai yawa itama fa 'ya ce kamar kowa, ALLAH ba madakata." Da haka ta fita tana Jin tausayin Aisha a ranta,itako Amina daki aka maidata ta kwanta inda Aisha ta fara gyara wajen da jinin ya 'bata ta dauki tabarmar tafara wankewa tana wanke jinin Baba Hinde na bala'i tana dukan Umma"wlh yau sai kinbar gidan nan Indo bake ba zaka da kanina Ina dalilin bala'i an auro mana irin mayu,dama can bana son auren nan yaron nan ne ya nace sai ke,Ashe ba hali ,kyawunki bai maki rana keda d'an maciji abaku da banbanci."ban da kuka ba abun da Aisha keyi tana wanke kayan jinin da abokiyar zaman nata ta ba'ta tunda Hinde ta fara magana malan Fatah ke tsaye tsakar gidan yana kallanta tana wulakanta mashi Aisha duk da yaji ance Amina tayi b'ari saidai Hakan bai taba masa Rai ba akan ynda ya iske yayar sa tana tozarta masa mata a hankali ya karaso inda suke hannunsa rike da Leda ya aje gaban yayar tasa yaja munfashi mai zafi yace."Duk abun da ALLAH ya hukuntama bawa a rayuwar sa shine daidai,yarda da qaddara shine Imani, Baba kiyi hakuri Aishatu ba zata iya cutar da Aminatu ba,nayi Imani da ALLAH ko ni nan bankai Aisha son cikin dake jikin Amina ba,Dan ALLAH ki daina muzan tata, kodan Ni."tafa hannu Hinde ta fara taba rike haba cike da takaicin kanin bata tace." Lallai kam Fatahu ka cika mijin tace ikon Allah ba rabon Babar mu taga kayan takaici ashe,toh bari kaji bani kaunar Indo Kuma dolene ta auna ta gidan su yanda tayi silar cikin Amina dole tayi silar auren ta"rufe idonsa malan yayi yanajin ransa na Kuna ya Kuma kallan yayar tasa yace."yanzun ina ita Aminar take."? Tabe baki tayi tana cewa" sai yanzun kake tambayarta tunda ka gama tarema Yar do fa'da ai da dukana kayi da yafi mani sauki akan wannan lusarancin da kakeyi akan mace." Shidai baice da ita komai ba saima dukawa da yayi ya dauki Leda biyu ya mikama Aishatu daya yace."ungo Aisha kidaina wannan kukan da kikeyi,jeki daki ki sauya kayan jikin ki Kinga duk sun jike Kuma jini ya Bata maki su." Girgiza kanta tayi tace." Bakomai malan, Nagode."juyawa tayi zata wuce daki ya Kuma cewa."karbi ledar mana takice fa."ya isa gabanta yana mika mata,tun kafin ta amsa har Hinde ta yi saurin fisge ledan dake hannun malan ta wankawa Indo gigitaccen mari tana cewa."makira ashema ansa zakiyi da yake Baki da Kunya ga duka ga tsinka jikka."da gudu Indo ta fada dakinta tana sakin marayan kuka,Banda malan da yayi mutuwar tsaye ranshi ya gama baci yace." A gaskia na gaji da wulakancin da kike yima matata Ba'ba akan mi zaki dinga dukar man matata bayan dukan Kansa haramun ne inatayi maki biyayya saboda kece nikema kallan uwa amma kaf kannen ki nine bakiyiwa adalci kinsa na auri Amina Baki bari na huta Banda tozarta min mata ba abun da kikeyi keda sauran yan uwana,kaf dinsu ba Wanda kikewa haka saini nagaji gaskia Kuma maganar Amina tunda haka kukace Aisha ce ta kashe mata d'a duk sainayi karar ku,komai zakuyi kuje kuyi, Ni dai Ina tare da matata hakurina yazo karshe.....Wani irin gigitaccen mari Ba'ba Hinde ta sauke saman kuncin malan dan dole sauran kalamansa suka tsaya cike da masifa taci gaba da cewa."yau ka tabbatar min da cewa bana ka haihu Fatahu tabbas kai din haifaffe ne yanzun akan mace kake da'ga min murya ina yayarka dama can ba kallan uwa kake min ba,tun da yau harka iya maidomin amsa abun takaicin ma akan Indo Kuma kara Kada kafasa Ina sauraron ka lokacin zaka tabbatar min da cewa kaidin haifaffe ne." Shidai malan Fatah dafe yake da kuncin sa ya rasa mi yakeji a cikin ransa wulakancin da akewa matarsa Indo ke damunsa ko dai masifar da magajiyar sa keyi masa ne ya dame shi...."ka zuba man idanu ko dai zaka dake Ni ne iyeeh da irin shu'umin kallo da kake jifana dashi kayi iya abun da zaka iyayi Fatahu dolen ka ka ramu da waccan makirar matar taka nadai nagaya maka." A hankali ya juya zai bar gidan zuciyar shi na masa zafi sosai har yakai bakin soro sai kuma ta fasa fita ya dawo har gaban Hinde yace."bazan Daina yi maki kallan mahaifiyata ta ba har gobe saidai kisani Hakan ba zaisa in rabu d matata wlh Ba'ba Ina son Indo Kuma itace farin cikina uwar Ya'ya na,duk wacce zan aura bayan ita Neman suna ne kawai amma ba za'a taba canzawa tuwo suna ba,ita dai ce macen da take tare da ni fil azal banajin zan rabu da ita,idan har ita tayi hakurin zama dani batare da haihuwa Ni kam bazan saketa ba akan wata can."kama Baki kawai Hinde tayi tana kallan yanda kanin nata ke rabtaho zance bazata iya tuna lokacin da ya taba musu da ita ba yau gashi takai yana fa'da mata magana son ranta a lokacin da yake gaban ta a matsayin uwar sa Wanda kowa ya shaida hakan."Yanzun Aminatu kake cewa wata can?? Iyehhh Fatahu?? Macen da ta dauki jinin ka a jikinta kake wulakantawa akan Juya?? Lallai Abdulfatah kazama shanyayye tabbas shakka Babu akan zancena ka kyauta tohh bari kaji ko Ni ko waccan algungumar billahi bazata kwana a gidan nan ba dole zata tafi gidan su yau din nan." Bata jira cewar shi ba ta afka dakin Aishatu ta na zauna saman darduma tana kaiwa ALLAH kukanta duk abun da sirikar tata ke fa'da ba Wanda bataji ba kuka kawai takeyi "fito waje dan uban ki." Ta tsinkayi maganar Hinde ta yaye mata labulan daki tana auna mata banzan kallo jiki mace Aisha ta fito daga dakin nata,rankwashi Baba Hinde ta sakar mata akai tana"yau sai kin koma gidan ubanki na dai fada maki."kuka tasoma yi ta kalman kafarta kawai ta zira ta nufi hanyar fita,malan dake tsaye kamar andasa shi ya gaza furta komai banda sanyi da jikinsa yai bala'in yi mashi ta gefen sa Indo ta wuce zata tafi gidan su."Aishatu."ya samu Kansa ta Kiran sunanta,cak ta tsaya daidai soro ta gaza ko motsin kwarai."ban lamunce da ki fita ko kofar gidan nan ba matukar kin yarda ni din mijin ki ne."ita dai Indo ta Kasa kwakkwaran motsi sai aikin kuka da takeyi,yayin da Baba Hinde ke rike da hannun Aminatu wanda tashin ta kenan daga dogon baccin da tayi duk da ba Wani kwarin kirki jikin ta takeji ba."kayi hakuri malan ba zan kwana gidan ka ba tabbas Kaine mijina bazan zauna ba."Bata jira cewarsa ba tayi gaba Banda kuka ba abun da takeyi, bakin cikin da Hinde ta dasawa malan bana wasa bane ba kadan zuciyar sa ke Kuna ba,ji yake kamar zuciyar sa Zata kubto daga kirjin shi tsabar takaicin da yakeji yau din nan,kallo da'ya yaima Hinde ya dauke Kai yasa Kai yai waje abun sa duk irin Kiran da Hinde ke ma kanin nata baisa ya ko kalleta ba." Inalillahi wa'inna ilahirraji'un wannan wace irin lukutar musifa ce kinga harya bita ohni Hinde,ace kana da marar Lafiya Amman bazata dubata ba kabi Juya marar haihuwa naga takaina Ni Hindatu."kukan takaici Amina tahau yi tana cewa."haka fa yake min Baba ba shafaffa da Mai sai Indo ya maisheni banza a cikin gidan nan,jiba kiga ciwon da b
Nake fama da shi ko sannu Banda arzikin ta yabi mace ALLAH na gaji da rayuwar kuncin da nikeyi a gidan nan, Nima gidan mu zan tafi bazan zauna ba."girgiza kanta Hinde tayi alamun aa tace "ba inda zakije tashi zakiyi muje gida na zaizo ya sameni ne, bashi ba waccan makirar matar tashi muje."mikewa Amina tayi tana kuka da haka suka nufi gidan Ba'ba Hinde sai korafi takeyi tana surfa masifa kamar wata zararra marar hankali.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.