_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 54*
_OKEKE COMLORT_
Tunda aka wayi gari aka tashi da tashin hankali a cikin Masarautar ta Okeke inda Sarki Ahmad ya shiga cikin tarin alhini da bakin ciki akan tashi zaunen da ya'yan Masarautar suka tada duk akan mulki kowa na ganin shine ya dace daya zama Sarki saboda gazawar da sukayi na bude dakin da kowa yagama saka mashi ido a kaf fadin Masarautar wanda har yanzun angaza samun wanda yayi nasarar bude dakin a cikin Yarima sha biyu da suke tutiya suna buga kirji akan sune magadan Masarautar yayin da kowa ke ganin shine Sarki na Hamsin cif da tarihi ya bayyana zaiyi nasarar bude wannan daki kuma shine Sarkin daya dace a saman karagar mulkin ta Okeke.Rigimar data janyo yanke yanke a cikin Masarautar musamman bangaren Yarima Gafar da Yarima Jabbar wa'anda suke tutiyar su sukafi kowa cancanta da mulkin Masarautar sannan su suka fi kowa dacewa da kyakkyawar 'yar Sarkin dake ci yanzun wato Sarauniya Azira 'ya ɗaya tilo wajen Oba Ahmad Okeke na II.Koda hatsaniyar ta faru da safiyar yau bakaramin asarar dukiya akayima Masarautar ba wadda kusan ita ke taka rawa wajen tattalin arzikin na Okeke na daga gwala gwalai zuwa ɗanyen mai da yankin yake tunkaho dashi rigimar tayi silar kone kone da sukayima Junan su banda wa'anda aka kwantar da dama a asibiti a ciki kuwa harda Ola Gaffar.Rundunar 'yan sandan yanki tayi dirar mikiya domin kwantar da tarzomar dake faruwa a cikin yanki kai tsaye cikin kamilallar Fa'dar Masarautar sukayima tsinke har gaban Oba Okeke Ahmad.koda suka isa sun iske shi cikin tarin alhini da tashin hankali ya gaza tsaye ya gaza zaune bayan sun kai gaisuwa wajen Oba Okeke Ahmad suka shaida mashi dalilin zuwan su sannan suka bukaci ji daga bakin shi akan abinda ke faruwa,Inspector Machel Godwins yace."Ekasan Oba (ina yini."lafiya lau Inspector bawoni(ya kake).?"Alhamdulillahi,am ranka shidade munzo bin cike ne akan abubuwan da suka faru a cikin Masarautar nan muna bukatar muji abinda ke faruwa daga bakin ka amatsayin ka na Sarkin wannan Masarauta mai tarin albarka."numfasawa yayi yace."Alhamdulillah ala kulli halin a gaskia na tashi cikin tarin fargabar abinda yafaru duk da ba wani issue bane na waje wannan rigima ce ta cikin gida bakaramar rigingimun da suka saba faruwa bane."ranka shidade minene musabbabin wannan dauki ba dadin."Mulki."dama ana gadar mulkine bayan Sarki maici yanzun na raye."Eh kasan ainahin wannan Masarautar tamu ta gaji haka saboda akwai Sarkin da zai bayyana a cikin zuriyar mu wanda shine zai amshi wannan mulki sannan shine cikamakin sarakunan mu na Hamsin idan har wannan Yarima ya bayyana ya zama dole Sarkin da yake mulki a zamanin yayi murabus akan mulkinsa."Allah yataimaki Oba taya za'ayi a cikin omo oba din Masarautar nan agane magajin daya cancanta."?murmushin manya yayi yace."wannan shine dalilin daya jawo wannan dauki ba dadin saboda kowa yana nuna shine ya cancanci hawa wannan karagar mulkin Okeke."taya akai suka gane sudin ne suka cancanta."? "Eh to actually har yanzun babu wanda ya cancanta saboda har gobe ba asamu wanda yayi nasarar bude dakin taskar Okeke ba wannan dalilin shiya kawo fitinar da yayi silar jefa kowa cikin fitina har rigimar takawo haka."Mungode ranka shidade saidai muna neman hadin kanka idan wani bin ciken ya tashi zamuzo gareka kafin mutafi zamuso muji daga bakin ka tsakanin Abdulgafar da Abduljabbar wanene kake ganin ya canci da zama Sarkin Okeke."Himm sai ranar da ɗaya daga cikin su yayi silar budewar waccen dakin na Okeke daga lokacin kowa zai san wanda ya canci hawa wannan kujera mai dinbin tarihi."gaskia ne amma ranka shidade mi zai hana bazaka nada wani daga cikin su Sarki bayan kayi marabus."daga ranar duk wanda yahau bisa wannan mulkin matukar ba shi bane Sarki na hamsin ba tabbas zai mutu,amma bayan Sarki na hamsin ya bayyana idan yayi wafati zai a iya cigaba da aiwatar da mulki na kama karya."ranka shidade kayi hakuri da wannan tambayoyin da nike yawan yi maka duk cikin aiki nane kada kaga na koma maka kamar wani ɗan jarida."Hmm ɗan sharri kenan,amma inajin ka."kace mulkin kama karya kana nufin harda ya'yan ku mata."sosaima zamu samu Olori bayan wannan Sarki ya bayyana."Allah ya bayyanar dashi ka huta lafiya."nagode."fita Machel sukayi suka nufi babban asibitin dake cikin Masarautar ta Okeke kai tsaye wajen Omo Oba Gaffar suka isa saidai basu samu damar zantawa dashi ba saboda yanayin da suka sameshi na rashin lafiya."yallabai bazaku samu damar ganawa dashi ba."cewar likatan dake kula da Yarima Gaffar."ok ba damuwa Doctor zamu bukaci ganawa dashi bayan ya samu sauki saidai kasani sammacin mu na hannun ka bamu lamunci bayan ya warke ba yabar hospital din nan ba tareda mun samu damar ganawa dashi ba."ba matsala indai wannan ne."good Allah ya bashi lafiya."da haka suka fita suka nufi inda zasu gana da Yarima Jabbar shima din basu samu damar ganawa dashi ba.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.