091

6 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 91*

Furzar da naunauyen numfashi Faruq yayi yana kallon Khalid yace."Saboda ko na gaya mata ni ba saurarata zatayi ba Khalid dan ko kallon fuskata Ramlat bata son yi Khalid dan baka ganin abinda take man shiyasa."cike da tausayinshi ganin yanda ya koma kamar ba Faruq ba Khalid yace."kaga ko?abinda nike guje maka tun farko kenan Faruq kaƙi tsayawa ka natsu balle har ka saurareni irin wannan lokacin nike guje maka gashi Allah ya jarabaika da masifar sonta ita kuma yanzun taki ta soka, shi yasa ba'a son ana zurfafa ƙiyaiya saboda gudun haka dan haka ni ba zan je nayi ma Ramlat wannan maganar ba Faruq."kallanshi Faruq yayi yana cewa.'Haba dan Allah Khalid Please ka taimake ni ka gane irin zazzafan son da nike ma Ramlat wallahi na tuba ba zan sake yi mata duk abinda nayi mata ba wallahi Khalid da gaske nike na tuba."dafashi Khalid yayi yana cewa."Da kanka zaka gyara zamanku Faruq ba sai wani ya shiga ba koda kuwa Momy ce."gyaɗa kai Faruq yayi yana cewa."Taya Khalid?nidai lamarin har tsoro yake bani dan tsanar da Ramlat take nuna man tayi yawa."murmushi Khalid yayi yana cewa."Duk karya ce tana sonka har yanzun dan nasan son da Ramlat take maka ba zai taɓa juyewa ya zama ƙiyaiya ba kawai gajiya tayi kuma da kanka zaka gyara kuskurenka a wajenta kuyi rayuwarku kamar komai bai taɓa faruwa ba."inason hakan ta kasance Khalid amman As How?tell me the way Khalid."gyara zamanshi Khalid yayi yana kamo kunnenshi ya rada mashi wasu maganganu ɗagowa Faruq yayi yana kallon shi ɗaga mashi kai Khalid yayi yana cewa."Try it Faruq I know you nasan zaka iya."dan shiru Faruq yayi yana nazarin maganar da Khalid ya rada mashi can kuma ya saki murmushi yana cewa."Thank you so much friend in shaa Allah I'll try my best."Good luck."sosai Khalid ya ƙara ɗaura Faruq a hanya akan shawarar da ya bashi sanann ya rakoshi har parking space ya shiga motarshi dan komawa gida with full confidence ya nufi gida dan ya shirya gwada shawarar da Khalid ya bashi akan Ramlat dan ya hangon hasken nasara a plan din.

★★★

Alhmdulillahi Jummala ta farfaɗo bayan wahalar da tasha dan ba ƙaramar wahala tasha ba ta jigata sosai dan kuwa har fidda rai da ita sai da su Hajjah sukayi sai kuma da yake Hausawa na cewa wuya bata kisa sai gashi Allah ya tashi kafadunta ta samu sauki sosai kamar ba ita ba,zaune take saman gadon rest room din da aka ajiye ta a asibitin tana kallon Babyn da Rumaisa ta riƙe kam tana kallon cike da zallar sonshi take tausayin yaron ya kamata har da ita kanta wai shi yanzun qaddararshi haka Allah ya rubuto ta a haifeshi ba ta hanyar aure ba,kuma gauwurtaicen dan kiddneping ne ubanshi innalillahi wa'innalaihirajiun abinda ta ambata kenan a cikin zuciyarta tana jin wasu hawaye masu tsananin zafi suna zubo mata a saman fuskar dan bata san da fitowarsu ba sai dai kawai taji saukarsu,zama gefenta Hajjah tayi tana kamo hannunta gami da share mata hawayen tana cewa."Haba Khadijah wai har yanzun kukan bai isa haka ba? karki manta da haka Allah ya qaddara maki a rayuwarki kuma sai kace ba musulma ba Khadija bayan kin san da cewa Allah maɗaukakin sarki yace ba zaku taɓa zama cikakkun musulmai ba har sai kunyi imani da qaddara mai kyau da kuma marar kyau shine cikon imani Khadija,tabbas da ciwo da kuma zafi gami da raɗaɗi sai ayi hakuri a rungumi qaddara sai Allah ya saka maki da kyawawan qaddara kuma wanann yaron har dake kanki in shaa Allah har abada ba zakuyi kukan maraici ba dan yanda nike kallon su Rumaisa a matsayin jikokina nike sonsu haka kema nike maki kallon da kuma sonki dan Allah ki saka ma zuciyarki hakuri da dangana kibar kukan haka nan karda kuma wata matsalar ta samaiki muna zamanmu lafiya." Kwantar da kanta a jikin Hajjah kawai tayi tana ambatar innalillahi wa'innalaihirajiun abinda take yi kenan ta kusa 10mn a haka sannan ta ɗago tana cewa."Nagode sosai Hajjah in shaa Allah ba zan sake kuka ba Hajjah Allah ya raya mana shi bisa tafarkin addinin musulunci."murmushi Hajjah tayi tana cewa."Amin ya Allah,tunda jikin yayi kwari bari Abida tazo ta bamu sallama mu koma gida sai dai wane sunan kake son a saka ma ɗan."numfasawa Jummala tayi tana cewa."Bani da zaɓi dan ban kai na zabar ma yaron nan suna ba da kaina Hajjah bayan gaku a matsayinku na iyayena duk sunan da kuka ga ya dace a saka mashi Hajjah."shigowar Umar Y kenan yaji maganar da suke samun waje yayi ya zauna yana cewa."A'a Khadija ke kike da hakkin da zaki saka mashi sunan dan haka ki fadi sunan da yayi maki sai ayi mashi huduba da shi."taɓe baki tayi tana girgiza kai tana cewa."Nidai kam gaskiya a'a dan kuwa bai da iyaye sama daku dan haka tunda kazo sai ka rada mashi duk sunan da ya dace."shiru kawai Umar yayi yana kallonta can kuma ya sauke kanshi daga kallanta yana kallon Hajjah yana cewa."To kinji Hajjah abinda tace."murmushi Hajjah tayi tana cewa."Naji Allah yayi albarka sai a sama yaro suna Umar hakan yayi maki ko Khadija.?" Murmushi Jummala tayi tana cewa."To Allah ya raya mana Umar."Da Amin suka ansa Umar Y yayi mashi hudduba da Umar take Rumaisa tace sai a ringa ce mashi Little nan aka gama Nurse tazo ta duba ta aka basu sallama.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now