_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 86*
Zaune suke a babban parlon gidan Buba har da maigirma His Excellency Alhaji Ma'azu dan takarar gwamna ta jam'iyar PNP dukansu sunyi shiru dan abun duniya ya ishesu yayi masu yawa komai ya jagule masu yayi masu tsaye cak! numfasawa Alhaji Ma'azu yayi yana cewa."Haba Alhaji Buba wallahi kana da damuwa kana da saurin fushi idan har bakayi wasa ba da wannan fushin zaka kore mana yaran jami'ya suna komawa wancan sakarar jam'iyar ta su Alhaji Yusuf haba mana yanzun wa gari ya waya mun rasa mutun kamar Umar Diga a wannan jam'iyar ko wancan mune fa muka ci zabe aka hanamu aka basu nasan wannan karan kuwa su zasu ci da kansu ba tare da wata damuwa ba tunda Diga ya koma tafiyarsu."Firzar da naunauyen numfashi Buba yayi yana cewa."Ai Alhaji Diga bai isa yaci amanarmu irin haka ba wallahi bai isa ba kuma yayi kaɗan yanda ya fara siyasa a wannan jam'iyar tamu haka zai gama ta a ciki ko yaso ko yaƙi."Tashi tsaye Alhaji Ma'azu yayi yana nuna Buba da yatsa yana cewa."Taya hakan zata kasance?kasan waye Diga kuwa Buba?Na lura ganin Diga kawai kake amman baka san waye shi ba Buba,nine nan na ɗauko Diga da wa'annan hannayen nawa na kawo shi siyasa,tabbas yaro ne mai rike amana da alkwari kuma Diga mutane ne mai ra'ayin kanshi ba'a isa a saka shi abinda bai niya ba tun ada haka yake yana da taurin kai sosai to gaya man taya zaka iya tauƙwara Diga ya dawo jam'iyarmu bayan ya fita har ya sake wata.?"Murmushi Buba yayi yana cewa."His Excellency calmdawn relief ni nan Buba zan maido Diga a wanann tafiyar tamu dan haka zanje gidanshi zamuyi magana ta fahimta dole ya dawo gida yabar gidan yan hamaiya kuma laifin da yayi mana na saka shi aiki yaƙi yi dole a ɗauki hukunci shima yaron Diga din wato Dila sai ya dandani hukunci da yaƙi kawo mana maganar da Diga yayi dasu Hadi bayan yana da yanda zai yi yajiyo mana tsoro ya hanashi lusari."Komawa mazauninshi Alhaji Ma'azu yayi yana cewa."Okay Goodluck Buba tunda kace zaka iya i proud of you Buba dan nasan waye kai."Murmushi Buba ya saki dan yaji dadin yabon da His Excellency Alhaji Ma'azu yayi mashi, numfasawa Alhaji Ma'azu yayi yana cewa."Bani da damuwa a yanzun da kuma buri da ya wuce naga bayan Acp Sanda ina son naga yana kuka da idonshi yana yabani ya shiga uku dama ace ya mutu yabar duniyar ya huta,sannan kuma bani fatan Yusuf Umar ya koma kujerar nan yanda ina kan mulki sukayi yanda sukayi suka saukeni saboda suke da presidency suka nuna man fin karfi suka haye haka nike so nima a wannan karawar da za'ayi na kwalashi ƙasa na fito government house tunda ba gadon uwa da uba bane,amman taya zamu kai ga daci?sai Umar Diga ya dawo tafiyarmu dan kuwa dukanku nan kun sani shine karfin tafiyar nan dan matasan Katsina sun zaɓe mune saboda Diga shi yace su zaɓe mu shi yasa har suka zaɓe mu wancan karan,to mudun wannan ƙaren Diga ya daga hannun Yusuf a matsayin gwaninshi tabbas mun soye inba Wata hanyar muka bi ba,to mulkin katsina zai bar hannunmu kenan sai dai hange daga nesa kuma ai ba haka aka so ba ƙanin miji yafi miji kyau."Gyara zama Buba yayi yana cewa."Ai hakan ma bazata faru ba dan mulki ya gama zama namu Alhaji mu iya jiran lokaci ba saura wata biyu ba?zamu basu mamaki ne koda Diga ko ba Diga mune zamu hau mulki."To Buba ai nasan zaka iya yin komai akan mulkin nan shi yasa nike alfahari dake."Godiya nike gwanina."Tashi His Excellency Alhaji Ma'azu yayi dan komawa gida bayan sun gama tsara yanda zasuyi da Sanda dan ba yafewa yayi ba ace kamar ɗanshi wai yana prison idan ya tuna hakan ranshi yana ɓaci sosai shiyasa yake jin bai iya yafe ma Sanda shi kuwa Diga ya bar komai a hannun Buba kamar yanda ya bukata wannan kenan.
★★★
Duƙe Samira take a gaban Hajia Mero tana surfa mata ruwan bala'i da masifa ita dai kan Samira yana ƙasa bata motsa ba, balle har ta ɗago ta kalli Hajia Mero da take maganganu mararsa dadin ji da saurare ta inda Hajia Mero ta shiga ba tanan take fita ba, numfasawa Samira tayi tana sauke ajiyar zuciya cikin muryar kuka tana cewa."Dan Allah Hajia kiyi hakuri wallahi hakan ba zai faruwa ba duk da ban ma san mai nayi ba." Wani kallo Hajia Mero tayi mata tana cewa."Wato dai na lura Samira kin raina man wayau ko?har ni zaki kalli idona ki wani ce man baki mai kika yi ba har ni zaki ce ma haka.?"Dan Allah Hajia kiyi hakuri ba zan kuma ba."numfasawa Hajia Mero tayi tana cewa."Mudun kika sake yin magana da wasu a cikin gidan nan idan har ba yan apartment din nan ba sai kin bar gidan nan daga ranar,dan ni ban san munafinci kuma bani harka da munafiki maciyi amana dan ba yanda za'ayi in ɗauko ki aiki da kaina kuma kina cin dunduniya ta."Sai a lokacin Samira ta ɗago tana kallon Hajia Mero cike da zallar mamaki saman fuskarta wai mai ke a cikin zuciyar Hajia Mero gamai da kishiyoyinta?wani irin zamane suke yi haka ne?Yanzun daga ta gaida Hajia Bilkisu da taje baya kwaso ma su Haulah wankin da tayi masu shikenan har ya zama laifi har tayi laifin da za'a kirata da munafika?ko so take ta raɓa mata ita da gidan mijinta ta ganta bata gaisheta ba sai kace wata marar tarbiya numfasawa tayi tana cewa."Kiyi hakuri hakan ba zai kuma faruwa ba duk ba wata magana mukayi ba ina wuni kawai nace mata Hajia."Wa yace kice mata ina wunin?dawa kikayi?Ni nace na dauke ki aiki dan ki dinga gaida wasu a gidan nan Samira.?"Girgiza kai tayi tana cewa."A'a hakan ma ba zai sake faruwa ba."Ya ma sake kin ga yanda wasan zai kasance tashi kiyi iron din kayan su Haulah saiki tafi salon kuma ki kona masu kaya."Tashi tayi ta shiga ɗakin da ake gugar kaya ta zauna ta fara guga a hankali cike da natsuwa da rashin son hayaniya dan Samira bata da wata matsala a rayuwa komai yin shi take a cikin sanyin hali dan kuwa zuciyarta cike take da damuwar halin da suka tsinci kansu a ciki a gidansu hakan ke hanata yin ko wace walwala.. shigowa tayi da wani veil a hannunta tana jefa ma Samira saman jiki tana cewa."Ke yi maza ki goge man ki bani zan fita yanzun."inda Sholy take Samira bata kalla ba ta cigaba da gogar unifoam din da take, veil din ko kallarshi bata tsaya kalla ba balle har tayi tunanin goge shi,tsaki Sholy ta buga tana cewa."Wai ba dake nike ba.?"Again Samira bata dago ba kuma bata fasa abinda take ba,ida shigowa Sholy tayi tana fisge iron da ke hannun Samira ta ɗaura mata shi a hannu tana cewa."Ke har kin isa ina maki magana kiyi banza dani?ke din wacece damai kike takaima.?"yarfa hannu Samira tayi tana jin wata irin masifar zafi saboda iron da ta daura mata a hannu,bata sanda itama ta tashi ta daura ma Sholy wani wawan mari ba har sau biyu take Sholy ta fasa wani irin ihu tsabar azabar saukar marukan ta dataji a saman fuskarta,da gudu Hajiya Mero ta shigo dakin tana cewa."Auta lafiya mai ke faruwa.?"Cikin kuka Sholy tayi kan Samira da sunan kokowa aikuwa ta rike ta gam tana cewa."idan har kika sake kika taɓa man jiki da sunan buga wallahi wanda zan maki sai yafi na farko."kama baki Hajia Mero tayi tana cewa."Ehyeh mai zan gani haka?Samira kardai ace bugar man yarinya kikayi.?" Share hawayenta Samira tayi tana cewa."Hajia dutsen goga fa ta daura man a jiki sai kace baiwar ta dan kawai ina aiki a gidansu sai ƙaramar yarinya ta raina man wayau har haka ko kuma ni ba haihuwata tawa uwar tayi ba a duniyar ko?to na gaji da wanann cin kashin da ake man daga wannan sai wannan ba irin zagin da yaran nan basuyi man kuma a gabanki baki taɓa hanasu ba kuma dukansu ba wanda ban ba shekara biyar ba a cikinsu koma sama da haka,dan Allah yayi ne a tallaka nazo neman na kai a karkashinku sai na zama abar wulaƙantawa a gareku Hajiya? nima fa ba jahila bace sa ilimi na idan suna takama da suna secondary school to ni degree ne dani rashin gatane ya kawo ni aiki a gidanku,zuwana aiki ba shi yake nuna ayi man duk wulaƙancin da aka gadama ba."Cacimo Samira Hajia Mero tayi tana kai mata mari Samira ta riƙe hannun tana cewa."Wallahi ba zan tsaya ki dokeni ba haka kawai mai nayi maki taya yarinya zata konani kuma naki dukanta."sakar man hannu ko naci ubanki a gidan nan."Wallahi Hajia ba zan saki ba kuma ubana baya ciyuwa."Dambe aka fara a tsakanin Samira da Hajia Mero dan kuwa Samira riƙe hannun Hajia Mero tayi gam ta hana ta taɓa mata lafiyar jiki.. shigowa yayi dakin yana cewa."Innalillahi wa'innalaihirajiun Aunty mai zan gani haka.?"shiga Auwal yayi a tsakaninsu yana cewa."Haba Aunty wannan ba girmanki bane fada da yar aiki.?" Nunashi da yatsa Hajia Mero tayi tana cewa."To tsohon munafiki ina ruwanka wata gulmace ta shigo da kai bangare na."Taɓe baki Auwal yayi tak bai ce mata ba yana kallon Samira da take goge hawayen fuskarta yana cewa."Yi hakuri baiwar Allah taho muje." Tare kofa Hajia Mero tayi tana cewa."Kuje ina?ba inda zaka je da ita a gidan nan wallahi Auwal,dan sai naci uban yarinyar nan sai na nuna mata ita karamar yar iska ce ba zata dokar man yarinyar a banza ba."kamo hannun Samira Auwal yayi fuskarshi babu wasa ko ɗaya a saman ta ya kalli Hajia da ta tare kofa yana cewa."Maza mu wuce."Take kwarjinin Auwal ya cika ma Hajia Mero ido bata san lokacin da ta matsa daga bakin kofar ba tana bala'i ko inda take bai kuma kalla ba ya fita da Samira har compound din gidan yana dauko kudi har 100k yana bata yana cewa."Ga wannan karki sake dawowa gidan nan."Ansa Samira tayi tana mashi godiya daman da hijab dinta a jikinta ta fita tana sauke ajiyar zuciya,dan daman koda ace ba'a bata kudi ba,ba zata sake dawowa gidan Hajia Mero ba dan ita ɗaya tasan irin wulaƙancin da ta kunsa a gidan tun daga farkon zuwanta.
Kamo hannun Sholy Hajia Mero tayi tana cewa."Bari uban naku ya dawo sai na gaya mashi duk irin wulaƙancin da yar aiki tayi maki kuma Auwal ya goyi da bayanta."kuka kawai Sholy take tana cewa."Allah ya isa ban yafe marin da tayi man ba,daman ai shi Yaya Auwal ba kaunarmu yake ba da ace Kausar ce ta mara ai sai inda ya karfinshi ya ƙare da yake mu daman ba son ganinmu cikin gidan yake ba,bai ki ma ace mun mutu ba."Tsaki Hajia Mero tayi tana cewa."Aikuwa sai dai shi ya mutu ba dai ku ba nan gani nan bari yanda na gagari uwarshi a cikin gidan nan haka kuma zaku gagareshi yanda suke takama gidan ubansu ne kuma haka tunda ba daga sama kuka fado ba,bari Alhaji ya dawo yau dai ayi ta ta ƙare a gidan nan dan na gaji da yan'ubancin da ake nuna ma yarana a gidan nan,yara kwaya biyu sun hanasu kwanciyar hankali to bakin cikin ganinsu da ake cikin gidan nan zai zama ajalinsu kuwa."Haka sukai ta masifarsu su kaɗai tana lailashin Sholy tana duba fuskar da tasha mari a wajen Samira..zama yayi yana kallon Mahaifiyarshi yana cewa."Momy ina rasa gane maike damun Aunty a gidan nan,ace tunda take bata taɓa kulla wata da yar aiki a gidan nan ba?ita dai kullum cikin korar yar'aiki take a gidan nan sai kace ita ɗaya ce mai masu aiki."Murmushi Hajia Karima tayi tana cewa."Auwal kenan sha'anin Auntynku sai hakuri da kuma addu'a mai ya haɗa ta da yar'aikin tata?yarinya mai hankali da natsuwa."numfasa yayi yana cewa."hayaniya naji na tashi a apartment dinsu ina shiga dan ganin maike faruwa na tadda tana kokowa da yar'aiki."kama baki Hajia Karima tayi tana cewa."Dambe fa kace Auwal?kamar Hajia Mero zatayi dambe da yar'aiki.?"Daga kai yayi yana cewa."Aikuwa Momy nine nan na fiddo yarinyar daga ɓangaren sai dai idan na lura kamar marin Sholy yarinyar tayi."Jinjina kai Hajia karima tayi tana cewa."Ikon Allah marin Sholy kuma?to da walaki goro a miya idan aka bibiya ai ruwa baya tsami banza,Allah ya tsare gaba."Amin ya Allah ina su Kausar su fito su tafi islamiyya."shirin da suke kenan." Fitowa su Kausar sukayi ya tashi yana cewa."Mun tafi Momy."A dawo lafiya."Da Amin suka amsa baki ɗayansu suka fita.wannan kenan.
Share pls
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.