_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 74*
Lumshe ido Sanda yayi yana buɗewa gami da Furzar da naunauyen numfashi yace."Jamila." Daga can bangaren Jamila take ansawa cike da kamaiwa, numfasawa yayi yana cewa."Nagode da duk abinda kika yi man kuma kin kyauta." Dan shiru yayi yana mai cigaba da cewa."kuma komai kikayi man nine nan na sayar man kaina da shi, sai dai inason kin san wani abu Jamila Allah ne ya qaddararman masifar sonki ina sonki Jamila kuma ina Kaunarki maiyasa ba zaki yi man adalci ba a soyayya? Sonki shine qaddararta kaunarki da ita nike kauna a zuciyata Jamila idan kika ce zaki cigaba da yi man irin abinda kika yi man yau a wani irin hali kake tunanin zuciyata zata kasance Jamila?Dan Allah Jamila." Shiru yayi yana mai jin zuciyarshi tana mashi wani iri yana jin yanda sonta yake luguje a cikin birnin zuciyarshi maganar Jamila ce ta katse mashi shirun a inda take cewa."Sanda kenan baka sona duk wannan maganar da kake ba a cikin zuciyarka take fitowa ba iyakar ta saman bakinka." Girgiza mata kai Sanda yayi kamar tana gaban shi yana cewa."Ko ɗaya Jamila inason ki yarda da cewa da zuciya ɗaya nike sonki kuma nike Kaunarki amman maiye naki dalilin na cewa haka.?" Numfasawa tayi tana cewa."Saboda da ace kana sona ba zaka taɓa yi man gadara ba Sanda balle nuna man isa da karfin iko,kenan a haka kake son na aureka kana nuna man irin wanan halin?duk haka ake kira da soyayya kenan?idan har kuwa haka ake soyyaya ni Jamila ban shirya yin ba kam,dan ni zuciyata kula da tattali take bukata da kuma lafazi mai dadi Sanda." Jinjina kai Sanda yayi yana cewa." Da farko zan baki hakuri idan har gani kike ina maki gadara Jamila sai dai mai inason ki sani haka Allah ya hallaceni ban san ma ina maki wata gadara ba dan iyata ba Jamila balle har nayi ta,idan ma na iya taya zan iya yi maki gadara bayan ina fama da ciwon sonki Jamila.?" Numfashi kawai Jamila ta iya firzarwa ba tare da tace mashi komai ba,shima Sanda bai jira ta cewar ta ba yace." Dan Allah Jamila inason ki bani dama sannan kuma ki natsu ki gane waye Sanda Please Jamila." Daga kai tayi tana cewa." Zan baka dama kamar yanda ka bukata kuma zan natsu na gane waye kai Sanda sai dai inason kasan abu ɗaya."Maiye shi Jamila.?" Numfasawa tayi tana cewa."inason ka sani ba inda gadara da izzah zasu kai mutun a soyayya ba iyakar soyayya ba a komai ma." Murmusawa kawai Sanda yayi yana cewa."Naji kuma na gode Ranki ya daɗe." Dan shiru sukayi na yan mintina katse shirun Sanda yayi da cewa." Gashi gobe zan tafi Niger dan duba case din Cp Adam naso kin san har yanzun bincike kawai ake akan mutuwar tashi ba dare ba rana dan son samun gano wa'anda suka kashe shi idan na dawo zan sake shigowa dan ina kewarki ina bukatar ganinki Jamila." Gyaɗa kai tayi tana cewa."Okay ba damuwa Allah ya kaika lafiya ya kuma sa ayi nasara." Murmushi ya saki mai sauti har sai da sautin ya ratsa dodon kunnenta yana cewa."Amin ya Allah Soulmate take care of urself." In shaa Allah tace tana kashe wayar.
★★★
Tunda Hajia Kubrah ta gargadi Jummala akan shiga ɓangaren Sagir take wasan buya da Sagir dan baƙi ɗaya tabar fitowa daga BQ kulle tana zaune wajen inna zulai dan ko Umar Y bai sake ganinta daga ranar ba komai take bukata inna zulai ke gaya mashi yana aiko mata dasu...hakan da tayi ba ƙaramin tada hankalin Sagir yayi ba dan ya kwaɗaitama ranshi Jummala kuma ya gudurci aniyar samunta ko ta yane zaune yake a parlon Momy suna kallo shi da Hunaisa kallon Hunaisa yayi yana cewa." Wai Auta ina yarinyar nan take?two days ban ganta ba." Taɓe baki Hunaisa tayi tana cewa."Wace yarinya kenan Ya Sagir.?" Dan shiru Sagir yayi bai bata amsa ba sai kuma can ya numfasa yana cewa."am na manta sunanta,amman kamar Ya Umar ya kawota gidan i think." Wani kallo Hunaisa tayi mashi tana cewa."Wai wannan bush girl din kake nufi Ya Sagir.?" Ɗaga kai yayi yana cewa."Eh." Numfasawa Hunaisa tayi tana cewa."Amman Ya Sagir mai wannan bagidajiyar zatayi maka?baka ga yanda take ba ko ƙamarta ma baka ji sa...dakata haka Hunaisa." Sagir ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yana cewa."ina ruwanki da abinda zan mata?ba tambayar kawai nayi ba?ko ke kika haifeni da zaki saka ni gaba da silly questions.?" Girgiza kai Hunaisa tayi tana cewa."Sorry Ya Sagir but I don't know everything about her." Taɓe baki yayi yana cewa."Sure.?" Ɗaga kai kawai Hunaisa tayi ba tare da ta sake ce mashi komai ba,shima tashi yayi yana cewa."Fine bari naje na dubo ta da kaina nasan dai bata wuce BQ."karka kuskura ka soma wallahi Sagir." Momy ta dakatar dashi da tunda suka fara magana shida Hunaisa take tsaye tana jinsu karasowa tayi a parlon tana cewa."Maza koma ka zauna inda ka tashi." Kallanta yayi yana sunboro baki yana cewa."Wayyo Allah Momy bafa wani abu zan mata ba kawai gyaran apartment zatayi man shine fa kawai." Tsuke fuska Hajia Kubrah tayi tana cewa." Ka kiyaye wallahi Sagir zan ɓata maka rai a gidan nan,daman mata ke zuwa suna gyara maku apartment?a ina taɓa ganin anyi haka a gidan nan?tun wuri ka dawo cikin hankalinka idan kuma kace kai a dole sai Khadija taje tayi maka gyaran apartment zaka hadu da Dadynku ne dan ba zan tsaya naita kumfar baki a kanka ba tunda ni baka jin maganata sai ku hadu kasan dai waye Dadynku." Zama Sagir yayi yana cewa." Haba Momy mai ya kawo Dady a cikin maganar nan dan Allah?daga gyaran apartment sai kuma haka ya bijiro?naji tunda baki buƙata ba zata je ba ni daman kallo bata isheni ba amman dan Allah Momy kibar saka Dady a irin wanann maganar." Taɓe baki Hajia Kubrah tayi tana cewa." Kai dai ai ake ji Sagir kuma ba zanye maganata zanyi ba a kanka duk randa ka tura Khadija apartment dinka da sunan wai gyara wallahi sai na gaya mashi dan nasan halinka kuma kaima kasan nasan manufarka nayin hakan inason na gaya maka da babbar murya Sagir tun wuri ka ɗauke idonka akan Khadija dan Khadija amanata ce aka ba Umar idan har kuskura kayi mata wani abu ba ruwana tunda kai dai ba zaka taɓa barin wannan mugun halin naka ,Sagir karka bari baƙin cikinka yayi ajalina fa."maida kanshi ƙasa kawai Sagir yayi yana wasa da yatsan hannunshi cigaba da cewa Hajia Kubrah tayi."Ina gaya maka gaskiya baka jina Sagir kai dan Allah baka ga yanda yayanka yake rayuwa ba shin baya burgeka?komai nashi a cikin natsuwa yake yin shi ban da kai da anyi maka magana kace anfi sonshi a kanka,to inason na tuna maka ka dawo nigeria da zama baki ɗaya karka ga mahaifinka shine gwamna kace zaka dinga abinda ka gadama wallahi Alhaji da kanshi zai daureka ba ruwanshi da shine ya haifeka dan haka tun wuri ka natsu kayi rayuwarka a cikin salama kamar yanda Umar yake yi fatan kaji ni.!?" Jinjina kai yayi yana cewa."in shaa Allah Momy daman ni tuni na dai na duk abinda kike tunani kuma ki yarda dani ba da wata manufa nace Khadija ta gyaran apartment ba."Allah yasa haka Sagir." Da Ameen ya amsa yana cigaba da latsa wayarshi yana kuma auna yanda zai yi ya fita da Jummala a cikin gidan ba tare da kowa ya gani ba dan samun abinda yake so a taitare da ita wannan kenan.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.