085

8 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 85*

Kwance take saman tafkeken gadonta na alfarma kana ganin yanda Azira take kwance zakasan kwanciya ce takeyi ta kasala irin ka farka a baccin nan,amma ta gaza tashi daga kwancen da take a hankali ta sake juyawa saman bed din tana sake rungume jibgegiyar teddy baby dinta akan kirjinta tanajin wani irin yanayi a tattare da ita, tarasa a situation din da take jin kanta a ciki yanayin farin ciki ne ko kuma akasin haka? batasan ya zata musulta yanayin ba...wayarta kirar Samsung ultra ta fara neman agaji da ido kawai ta raka wayar batayi ko yunkurin dauka ba akan idonta tagama ringing harta yanke,wani kiran aka sake yo mata tashi tayi a hankali ta zauna a matukar gajiye haka take jinta kamar wadda akayima dukan kawo wuka ita dai gata nan dai, yunkurawa tayi a hankali ta sauko da kafarta kasan tiles din dakin tana zura room shoes dinta dake gefen gadonta, a matukar kasalance ta mike tsaye tana yin doguwar mika tare da sallami a bakin ta sannan ta nufi hanyar bathroom dinta tsaye tayi tana bin bandakin nata da ido kafin ta Kuma sa bathroom shoe sannan ta shiga bathroom din wanda za'a iya kiran shi da aljannar duniya ya gaji dajin kayan ado na iri iri na decor din toilet ba irin wanda ba'a zuba aban dakin ba, direct wajen da aka danada domin danyin wanka ta shiga already hadimarta Latifa ta gama hada mata duk abun da tasan tana bukata domin yin wankan, a hankali tafara zubawa jikinta ruwa mai tsananin zafi har siracinsa ke tashi a saman fatar jikinta ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana watsa ruwan gami da shide ajiyar zuciya ba kadan takejin dadin su ba duk sanda zata zuba ruwan ajikin ta tajima tana abu da'ya kafin ta wanke jikinta tas ta fito Banda kamshi shower gel na abun dake tashi a bathroom din  Kamar wacce tayi wanka da ruwan turare tayi, tana fitowa wajen bath din ta Isa gaban mirror domin yin toothpaste tana gamawa tafito daga ban dakin baki daya, fitowar keda wuya ko gama tsane ruwan jikinta bata gama yi ba,hadimarta Latifa ta shigo room din bakinta dauke da sallama a cikin dressing mirror din take kare mata kallo har ta iso dukawa tayi Kasa tana maida kanta Kasa tace cikin tarin girmamawa tace."Ekaro olori."jinjina kai kawai gimbiya Azira tayi tanaci gaba da shafa lotion a jikinta cikin sanyin rai." sake kallanta Latifa tayi tace."Ranki shidade kamar wani abu na damunki,Allah yasa dai ba wani abu ne nayi maki ba."?girgiza Kai Azira tayi tana mai cewa." No Latifa bakiyimin komai ba, banajin dadin yay San wlh I'm out of my mode Latifa,bansan miye matsalan ba, inajin jikina very weak."Ajiyar zuciya Latifa ta sauke tace."Ranki shidade ki kwantar da hankali ki ba wani matsala bane da kinyi break fast zaki koma normal."jinjina kanta kawai Azira tayi tana shafa man baki a saman lip dinta ta mike tsaye ta koma gaban gadonta already Latifa ta gama fiddo mata kayan da zatasa, cikin nutsuwar ta tafara kimtsawa tareda taimakon Latifa harta gama shiryawa komawa tayi ta zauna saman bed tana mai sauke numfashi tace."miye labari Latifa."?zaunawa Kasa Latifa tayi tafara dannawa uwargijiyar tata kafafuwanta tace."Yarima Jabbar ya bukaci ganawa dake Allah yataimakeki."bayan wannan fa."? ta tanbayeta tana zura bangus din gold a hannunta,maida kanta Latifa tayi kasa tace."Yarima Gaffar yanayin birthday a yau din nan ranki shidade."cikeda zallar mamaki gimbiya Azira take kallan Latifa can kuma tace." A ina kika samu wannan labarin."Sake maida kanta tayi kasa tace."tuba nike ranki shidade jiya ya aiko amintacciyar baiwar sa Falmata domin ta shaida maki,harda takarda ta kawo min naso in sanar maki a lokacin naga kina cikin uzurika masu yawa,kimin aikin gafara."sake jinjina kai tayi tace."tabbas nayi busy dayawa, amma duk da haka da kinyi duk da yanda zakiyi domin ki sadani da sa'kon Yarima Gaffar, inaga indan naji daga wajen da sa'kon yake kila dana saurareki Latifa"d'an shiru tayi tana numfasawa sannan ta kuma cewa."Well zaki wakilceni ne a taron."arazane Latifa ta kalli Gimbiya Azira tace."Nagode da karamci ranki shidade, saidai zuwanki wannan waje yana da mahimmancin gaske a wajen Oba Gaffar domin kece babbar bakuwar sa a wannan rana mai dinbin tarihi a wajen sa,ko na komai inason uwar gijiyata data tuna da alkawalin da tayima Oba gaffar, nasan yana mai daukin ganin a ranar murnar haihuwarsa a matsayin shi na Oba mai jiran gadon wannan masarauta mai dibin tarihi ranki shidade."nunfasawa gimbiya Azira tayi tace."hakane Latifa saidai a schedules dina na yau bana tunanin an tsaramin zuwa birthday din nan,abinda nasani zan ga Oba Jabbar ne shima bayan la'asar ne ."Shiru kawai Latifa din tayi tarasa ta ina zata fara conviencing Azira taje wannan taroa da kowa yake daukin da kaf masarautar, ita dai ALLAH ne shaidarta tafi son gimbiya Azira da yarima Gaffar saboda sunfi dacewa,yafi yarima Jabbar komai,duk da tasan su dukan su din suna wahalar da kansu ne kamar iskane da mai kayan Kara....tasan kaf dinsu ba wanda yasamu karbuwa wajen gimbiya Azira, saboda kaf cikin zuri'ar Oba Ahmad Okeke,ba wacce keji da isa kamar ta, bakaramin dace bane a wajen mutun ace gimbiya kamar Azira ta aminta da mutun,muddun mutun ya shiga cikin sahun masoyan ta tabbas kayi dace, dacen ma na gaske saika isa kuna ka tumbatsa sannan zata kulaka,yarinyar da ko y'an matan masarautar ba da ko wacce take kulawa ba, saboda tana takama ita olari ce Kuma diyar Oba Ahmad Okeke tana gani tafi karfin kowa da komai a duniya, hatta Ya'yan sarakunan duniyama wa'anda sukafi ubanta Mulki ta nuna tafi karfin ya'yan su, bare tasu masarautar wanda ta bude idonta ta ganta a ciki....kawo burinsa kenan ya kasance da ita ba irin kokon barar su da basu kawoma Sarki Ahmad akan auren gimbiya Azira, amma kash takisu bare harta anshi kokon barar tasu, Suma Gaffar da Jabbar abin da yasa take kulasu saboda anasa ran a cikin sune zasu iya gadar sarautar Okeken,matukar sukayi sanadin budewar taskar Okeke duk da hakan ya gagaresu...babban mafarki da cikar muradin gimbiya Azira bai wuce taga tayi ido hudu da Yariman da zaiyi silar budewar taskar Okeken kamar yanda tarihi ya nuna cewa duk wanda ya bude wannan taska shine  zai zama Sarki na Hamsin cif a karagar mulkin ta Okeke,kowa yasan da wannan tarihin idan har ba'a samu wannan Omo Oba din ba,saidai ya tabbata itace zata gaji mahaifinta zata zama Sarauniya ta farko a cikin tarihin masarautar,wannan kuma shine cikar burin Azira da kuma burin mahaifin ta a rayuwa,Mai irn wannan buri ta ina gimbiya irin wannan Kamar Azira zata iya kula wani a rayuwarta? Da kamar wuya kam ko su din dake tadajijiyoyin wuya akan,tana basu lokacinta ne shima ba kowa ba daga yarima Gaffar sai kuma yarima Jabbar sune take kulawa,Kuma suma sunfi kowa izzar mulki da nuna su sukafi cacanta fiye da kowa na masarautar,shiyasa take kulasu shima ba sosai ba duk da kuwa tarin masoyan dake neman aurenta tun daga kan Ya'yan governor's, Senator's da sauran ya'yan sarakunan dake neman aurenta amma duk da haka gimbiya Azira tayi fatali dasu,daban komai saboda tana gadara da tsantsar kyawun da ALLAH ya wadata ta dashi, shine babban abun da yake Kara sa Azira keyin gadara da girman kai, duk da a wani bangaren dole ne Azira tayi irin wannan gadarar   saboda a iya hasashen da akayi  ana kyautata zaton cewa kaf yankin Niger dama Okeke place babu budurwa mai kyaunta duk da kasancewar Yaroba,amma da yake half case ce mamanta shuwa Arab ce babantane Yaroba,saidai Allah ya wadata gimbiya Azira da kyau, tabbas kyau mai ban mamakima kuwa....sake Maida kanta Latifa tayi tana mai miko mata wayarta tace "Ranki shidade, Omo Oba gaffar ne ke kiranki."sake duban Latifa tayi batare da tayi yunkurin amsar wayar ba, tace."dauka kice masa ina da uzuri ne yanzun."batayi kokarin yimata musuba ta daga wayar ta gaisheshi cikin girmamawa sannan ta sanar dashi  duk abun da Olori tace batare da ta rage komai ba, Ajiyar zuciya gaffar yayi yace."ki shaida mata alfarmar dana jima ina nema a wajen ta ina kara neman wata alfarmar ta taimaka ta halacci zuwa wajen birthday dina idan tayi maki haka zanji dadi sosai."jinjina kai Latifa tayi kamar yana gabanta tace."Angama ranka shidade zan isar da sa'kon ka kamar yanda ka bukata."murmushin Jin dadi yayi mata yace."idan har Olori ta amshi gayyatar da nayi mata kina da kyauta mai tsokar gaske."washe baki Latifa tayi taji kudi tace."baka da matsala, Allah ya taimaki Omo Oba magajin gobe."da haka ya yanke kiran na tareda ya sake cewa komai itama cire wayar tayi a kunnenta tana sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta ga gimbiya Azira dake aikin kallanta tun dazun ganin doguwar wayar da takeyi da yarima kamar Oba gaffar baccin sila ina Latifa ina yin waya da gaffar sukutum, murmushi kawai tayi tana mai da'gawa Latifa hannu dake shirin sanar da ita abun da Gaffar din yafada mata tace."ba sai kince min komai ba Latifa."Shiru tayi tana sauke kanta Kasa gabanta na faduwa kadan kadan."Latifa."gimbiya Azira ta sake Kiran sunanta adan kausashe,cikin kidima ta dago kai tana kallan jikinta harya dauki mazari ta amsa a matukar tsorace, ahankali Azira ta mike tsaye tana folding hannayen ta tace."kardai ace deal zakiyi da gimbiyar ki? bayan duk yarda da nayi maki a rayuwata."?da sauri ta girgiza kanta tace "bana fatan na kasance cikin Wanda zai ha'ince ki ranki shidade kawai dai ina son ki duba al'amarin yarima Gaffar ne."jinjina kai kawai gimbiya Azira tayi bata sake cewa komai ba ta dauki wayarta data fara ringing d'an shiru kawai tayi kafin tace."okay daddy"da haka tayi gaba, da sauri Latifa ta maye mata baya,wannan kenan.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now